GIDAN UNCLE 37
*GIDAN UNCLE*
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:
*PAGE THIRTY-SEVEN*
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kamota Hajiya tayi da sauri na hadata da jikinta tace “subhanallahi haihuwar tazo Umah bari mu tafi Asibiti” riqota tayi a jikinta suka fito parlourn inda Kaka take zaune tana duba jarida miqewa tayi da sauri daidai lkcn da Hameed din ya shigo parlourn ganin yanda Umaiman take yatsina ana rirriqeta ai baisan sanda yayi watsi da ledar shop din dake hanunsa ba ya nufi Umaiman da gudu ya ruqota Hajiya tace “yawwa maza sata a mota haihuwa ce…”
Ai bata I rufe bakinta ba ya sunkuceta yayi waje har yana tuntube yanakiran sunanta, sata yayi a sit din baya yashiga ya tada motar bai jira fitowar su Hajiyan ba saboda gani yake zata bata masa lkcn yaja motar a mugun guje ya fice daga gdan.
Suna fitowa sukaga tashin qurar motarsa suka shiga wata driver yaja suka rufa masa baya bai iya hqrn kaita asibitin nassarawan ba saboda nisansa yake gani daga unguwar tasu wani asibitin kudi ya nufa aka karbeta aka shiga da ita larbour room sai bayan an shiga da ita sannan su Hajiya suka qaraso Hajiya ce tabada katinta tare da fada musu matsalarta shikam gogan sai safa da marwa yake yana hada gumi kamar shine yake naqudar duk sanda ya juyo nishinta shima sai yayi kamar shine me haihuwar lamarin ba duk da halin tararrabin dasu Hajiya suke ciki basu kasa yimasa dariya ba amma shi ko a jikinsa bin likitocin kawai yakeyi da suketa kaiwa da komowa idan kuwa yajisu shiru ya rinqa leqe kenan ta window.
Cikin ikon Allah baa bata wani dogon lkc ba Allah ya sauki Umaimah lfy ta haifo kyakkyawar yarta mace me kama da ubanta da uwarta dake dama kamar tasu dayace kowanne ka kalla sai kace yarinyar tana kama dashi tsakanin Hameed din da Umaimah.
Kukan jaririyar ne ya ankarar dashi aikuwa tun kafin a bashi izinin shiga ya danna kai dakin ya hango Babyn tanata wutsil² a hanun wata nurse ko takan Babyn baibi ba ya nufi inda Umaiman take ya tsugunna yace “wayyohhh Allah Babyn Uncle sannu kinsha wahala ko da wahala haihuwa ko? Ni nama yafe kawai wannan kadai ta ishemu”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wani kallo da takeyi masa ne yasashi miqewa a sanyaye ya matsa inda nurse din take riqe da Babyn take shiryata ya tsaya ya zubawa yarinyar ido kawai sai yaji wasu hawaye sun zubo masa Allah kenan duk cikin yayansa babu wacce take tsananin kama dashi kamar jaririyar ajiyar zuciya yayi ya miqa hanu ya karbeta daidai lkcn dasu Hajiya suka shigo dakin.
Da sauri Hajiya ta nufi Umaimah ta dagota ta nufi toilet din da taga wata nurse ta fito tace “akwai ruwan da zata gyara jikinta?”
Amsawa tayi da “eh nama hada mata gashi can a ciki” shiga sukayi Hajiyan ta gasa mata jikinta sannan suka fito ta zaunar da ita a gefen gadon dagyar saboda ta dunku kamar qwarya sai a lkcn Hajiya ta samu damar daukar jikar tata da taketa wawuran abinci ta zuba mata ido kamarta da ubanta lkcn yana jariri har tayi yawa.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Hakanan suka yini a asibitin Hameed yana liqe dasu suna zuwa Hajiya dakinta takai Umaimah tana mata sannu har yanzu tana maqale da jikarta saida ta bawa Umaimah abinci da tea tasha sannan ta dora mata babyn a cinyarta tayi murmushi tace “yarinya kyakkyawa amma kun bata mata nasaba saboda son zuciyarku”
Hameed ne ya dago ya kalleta ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace “muma ba muso hakan ba Hajiya komai yana faruwa ne bisa buwaya da ikon ubangiji ku daina zargina wlh ba haka nakeba rabon wannan yarinyar zatazo a hakane yasa kika takura saina saki matata a halin inasonta tanasona kuma mun riga mun zama abu daya bazata iya rayuwa babu niba nima bazan iya rayuwa babu ita ba Hajiya ku taimaka ku dawomin da matata tunda ta haifemin abinda ke cikinta”
*UMMUH HAIRAN CE…✍????*