INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

INAYAH 41-50

41
Arewabooks@Mamuhgee
Ahankali Haj umma ta qaraso tana kallon babyn hannunsa a Rikice tace”

MAJEED babyn waye wannan?

Da sauri ya dago Yana kallonta dasu anty juwairiyyah.

Miqawa nurse babyn yayi yana kallon hajiyan yace”

Umma muje gida Zan Miki bayani.

Kasa motsawa tayi sbd fargaba da tsoro tace”

Majeed bazan koma gidaba wlh saikamun bayanin Inda kasamo wannan babyn.

Mezan gani majeed?
Mezan ji?
Ta tabbata kenan fasiki ka Zama har kayi nisa haka¿

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun” zuciyarsa dake rawa tafara karantowa.

Cikin dacin kalaman mahaifiyar tasa ya dago ya kalleta Jin sunan fasiqi data kirasa dashi.

Zuciyarsa na daci ya bude Baki zaiyi magana anty juwairiyyah ta taresa da munanan kalamai tareda kiransa da sunayen mazinatai kala kala.

Kasa dago kansa yayi cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki ya dakatar da Anty juwairiyyah da cewa”

Anty juwairiyyah me kika fada?
Sunayen mazinata fasikai kike kirana,
Idanma nine mahaifin babyn akwai yanda zakuyi ne da qaddarar Allah?…

Ba zato sukaji qarar saukan Marin da hajiya tayi sakar Masa tana kallonsa ciki tsananin bacin Rai da baqin ciki tace”

Wallahi wannan ‘yar bazamu taba karbantaba idanma Kaine ubanta,
Idan Kuma wani gurin kasamota kayi gaggawar maida ita..

Kai koma Kaine ka haifeta bazaka karbetaba wuce muje gida.

Jajir idanuwansa sukayi sbd baqin ciki da damuwa,

Su Anty safiyyah kuwa ta Inda suke shiga bayanan suke fitaba take hankalin hajiya yaqarasa tashi hawan jinin datake fama dashi yayi sama take
Ba Shiri suka Jata zuwa gida har ABDULMAJEED din Wanda jikinsa yayi dukkanin sanyi.

Isarsu gida Bai qarar da komaiba sai sabon tashin hankali Dan kuwa bayanai ne daga Yan sanda sukazo anga Hadiza Kuma ta tabbatar musu da ‘ya ‘yarsace.

Kasa yarda da zancensu yayi saida aka kawo Hadiza wadda gabaki dayanta batada bambamci da mahaukaciya sbd yanayin shigarta da rashin lafiyarta.

Saida aka fara tambayarsa ya tabbatar musu da itace mahaifiyar babyn kafin aka sake tambayarta itama tace babynsa ce.

Ganin yanayinta na tabin hankali yasa aka sallameta ta tafiyarta dayake yan sandan sunga gurin samun kudi sai suka Kama MAJEED din akan yayiwa mahaukaciya fyade ta Haihu.

Take Yan sanda suka sauya zancen Kuma suka tabbatarda Hadiza ta tafiyarta sbd karma aci gaba da tambayarta tadawo daidai tafada wani zancen Bayan wannan.

Babban tashin hankali yashiga Yana son mahaifiyarsa kadai ta yarda dashi ta fahimcesa Amma tuni taji tana danasanin fifita sonsa akan sauran ‘yayanta.

Kasa danne abinda takeji tayi zuciyarta take tafara Neman bugawa aka kwasheta zuwa asibiti.

Acan station kuwa ba Imani yan sandan suka rufesa tareda cike Masa laifin dabai aikataba.

Zafi zuciyarsa da kansa sukeyi kaman zasu fashe,
Wace irin masifaffiyar qaddara ce wannan?
Tayaya mahaifiyarsa da ‘yan uwansa zasu yarda da zai iya Koda kallon wannan matar so ukuma bare iya wani abun da ita sbd tsananin qyanqyamin dayake dashi.

Bai taba kukaba tun girmansa Amma ayau baisan lokacinda wasu hawayen baqin ciki da qunci suka gangaro masaba.

A rufe ya kwana Saida yakuma wuni a rufen kafin alhj jamilu qanin Haj umma yazo yayi belinsa shima ransa amatuqar bace da abinda MAJEED din yayi.

Ko sauraronsa baiyiba yayi Masa diban albarka da maganganun dasuke kaman Yana Masa Baki.

A gidan ma saida ya zubda hawaye ga maganganu marasa Dadi da ‘yan uwansa suka ringa jifansa dasu
Mahaifiyar tasa kuwa ko qaunar ganin batayi hakan ta ringa hawaye tana jujjuyar dakai batason ganinsa yatafi yabarta kawai.

Nauyi zuciyarsa tayi ta yanda baisan mezaiyiba,

Mahaifiyarsa ta tsanesa Bata son ko ganin inuwarsa,
Yan uwansa ma sun tsanesa,

Yan uwan mahaifinsa Dana mahaifiyarsa sai Allah wadai sukeyi dashi.

Kiransa akai daga asibiti akan yazo ya tafi da babysa.

Baida wani zabi bayan zuwa ya karbota sbd bazai iya barinta acanba ayanzu da kowa yagama alaqanta shine mahaifinta.

Koda ya karbota ya dade Yana tunanin Inda zai kaita sbd dagashi har ita bazasu taba karbuwa ba a gidansu.

Hakanan ya daure ya iso gidan da ita saidai tun kafin ya shiga ainihin gidan su Anty safiyyah suka tabbatar Masa bazai zauna da ‘yar ba a gidan.

Zabi zaka dauka ko ka kaita gidan marayu kokuma kasan Inda zakaje ka raineta Dan bazai taba yiyuba ayi renon ‘yar qaddaraba a gaban hajiya sbd baka damu da damuwa ko baqin cikinka ya kasheta.

Bai tsaya ya sauraresuba ya wuce ciki da ‘yar a hannunsa rungume ya nufi dakinsa.

Cikin fada sosai da tsawa anty juwairiyyah tace”

Bakaji abinda safiyyah ta fada bane?
Ina zaka wuce ana magana?
Ka fice kakoma tun dare baimaba kakaita gidan marayu idanma bazasu karbaba ka maidawa mahaukaciyar uwarta idan taga dama ta Yar da ita…

Tsananin zafi da quncin da zuciyarsa me Masa yasa tafara bushewa a fusace yace”

Duk abinda zanyi da ita da Inda Zan kaita ba ruwan kowa bane matsalata ne tunda nine nakawota..

Idan sbd wannan ‘yar alhakin aketa tada hankali to naji nine ubanta zai raineta daga Nan har girmanta Kuma Babu Wanda ya Isa ya hana hakan…..

Nima ban isaba Amma Kuma na Isa danace kabar gidan Nan da ita tunda gidan bana uban nata bane.

Kai yanzu MAJEED har kayi nisan da yannanka suna magana kana mayar masu Kai me ‘ya?
To wlh wallhi wannan ‘yar dai bazata zauna a gidan banba,

Banason ganinku daga Kai har ita ka tattara ku koma gidan marayun har Kai sbd kaima kazama marayan daga yau…

A Rikice ya kalli hajiyar idanuwansa na sauyawa
Muryarsa na rawa yace”

umma nabar gida?????

Ban Isa bane?
Ai kakai tunda kazama uba yanzu.

Innalillahi wainna ilaihrrjiun””
Umma……..

Daga Masa hannuwa tayi tareda fashewa da kuka Mai ciwo da qunan zuciya tace”

Idan Ina ganinka zuciyata bugawa zatayi MAJEED Dan Allah ka tafi na daina ganinka da ‘yar nan.

Kaci amanar tarbiya da tsananin kaunar dana fifitaka akan ‘yan uwankw..

Maganganunta dukan zuciyarsa sukeyi suna yamutsa qwaqwalwarsa tareda zafafa kansa.

Daqyar ya daga qafafunsa zai matso gabanta ta Kuma fasa kuka tana ja da Baya.

Wani nauyi ne ya danne Masa zuciya ya juya ahankali ya shiga dakinsa ya tattaro kayan dazai buqata ya zubo a jaka ya fito.

Su Anty safiyyah na kallonsa da mamaki sosai ya fice gidan batareda yasake cewa komaiba.

Yana fita kuwa hajiya jikinta ya rikice Nan tafara numfashi daqyar
Hankali tashe aka kwasheta zuwa asibiti.

Baitaba sanin haka ‘dacin baqin ciki yakeba sai yanzu,

Zafi,ciwo,radadi,nauyi da tiriri zuciyarsa keyi duk lokaci daya,

Gidan Alhaji jamilu ya nufa Amma cin zarafin dayayi Masa yafi Wanda akayo Masa daga gida Dan haka yana baro gidansa Kai tsaye hotel yanufa yakamata daki ya kwantar da babyn tareda komawa gefe ya zube Yana riqe kansa dake neman tarwatsewa.

Babban qunci da dacin zuciyarsa yanda mahaifiyarsa da Yan uwansa dasuke jininsa suka zabi aibatasa da kalmomi mafi muni tareda tsanarsa..

Shin idan da gaske shine qaddarar haihuwar babyn ta sama haka zasu gujesa kenan?

Me yayiwa wannan baiwar Allah dazata ruguza rayuwarsa haka?

Kansa dake Neman bugawa ya juyo ya kalli babyn dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali..

Wani irin tausayinta yaji tareda qaunarta,
Me tayiwa mahaifiyarta dazata jefar da ita haka ga mutuminda batasaniba,
Batasan halayyarsaba,
Shin idan ga wani mugun mutum ne ta jefarda ‘yar Yaya takeson rayuwar wannan ‘yar alhakin tayi.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button