NOVELSUncategorized
GIDAN UNCLE 48
*G.U*
Kuka ta saka masa ta qanqameshi shima hawayen yake yana buga bayanta alamun rarrashi daqyar suka iya saita kansu ya sanya harshensa ya share mata hawayen ya bude motar ya riqota a jikinsa bai damu da yawan mutanen dake gdan ba kuma bai amsa gaisuwar da dangin Salma suketa yi masa ba yaja matarsa suka shige part dinta yana shiga yayi turus ganin Hajiya a zaune a parlourn da Aunty Jameelah da Zarah ga qawayen nata guda uku qanqameta yayi a jikinsa cikin rawar murya yace “shi… shikenan Hajiya tazo ta rabani da rayuwata Hajiya Umaimah rayuwa tace kada kice zaki rabamu wlh alhakin kisana zai rataya a wuyanki saboda inason matata Hajiya cikine da ita kada ki rabamu ki tausayawa yayan mu wlh mutuwa zanyi idan babu Umaimah a cikin gdana”
Miqewa Hajiya tayi tana zagaya parlourn tace “Zarah shiga ki hado mata kayanta ai ba wannan ne karon farko da mace take haihuwa a gda ba wlh Hameed bazan bar yar qanwata ta salwanta saboda kai ba kaidai na sallama ka tunda kai ka daukowa kanka kara da kiyashi dama ai hausawa sun fada jaye-jaye ke sanya jidali wlh baka fara kuka ba Hameed indai Salma ce gakanan gata ko kasheka zatayi babu abinda ya shafi Zulaiha amma Umaimah kam saika barta ko itace ke busa maka numfashi….”
Fuzgo hannun Umaimah tayi da qarfi shi kuma ya riqeta qam a qirjinsa yace “wlh Hajiya ko zaki tsinemin bazan rabu da matata ba saidai ki kasheni” tsayawa tayi sororo tana kallonsa yayi qasa da gwiwarsa ya durqushe yana wani irin kuka me ban tausayi jikinsa yana rawa yace “meyasa kullum tausayinki ya qare akan Umaimah Hajiya ni bakya tausayina meyasa bakwa yiwa rayuwata uzuri bayan bani na tsarota haka ba kuma ban isa na canzata ba meyasa kullum burinki nayi miki biyayya ni na cutu Hajiya ya kikeso nayi ya kikeso na kasance gwauro babu Umaimah ina Hajiya bazai yuwu ba bazan iya biyayyar dazan cutar da kaina ba…”
Sake jan jiki yayi kusa da Hajiya yace “Hajiya wlh aurena da Salma qaddara ce wlh tallahi billahillazi La’ilaha illah huwa Hajiya banajin ko digon soyayyar wata mace a raina bayan yar’uwata kuma matata Umaimah Hajiya na tsani ko tafiya ta tasomin wacce zata nisantani da kwanciya a jikin matata Umaimah Hajiya babu macen da nake samun nutsuwa da ita kuma nasa a raina zan samu bayan Umaimah Hajiya babu macen da zata iya dauke lalurar rayuwata bayan Umaimah saboda ita kadaice take sona domin Allah kuma ita kadaice take gamsar dani”
Yanda yake mgnr yana kuka muryarsa na daukewa ne yayi bala’in tsorata Umaimah ta fashe da kuka ta qanqameshi tace “Hajiya badon halinmu ba kiyi hqr wlh Hajiya inason mijina kuma baa kaina aka fara kishiya ba Hajiya shikenan idan kin rabani dashi haka zan rayu bazanyi wani auren ba idan har kin yarda zakita kallo na bazaki sake auradda ni ba to na amince ki rabamu idan kuwa kinsan zaki qara auraddani to kiyi hqr ki barni na rayu da dan’uwana Hajiya bansan waye zan aura ba meye halinsa matansa nawa idan bashida mata inada tabbacin wataran bazai min kishiya ba banida shi saboda haka Hajiya ki tayamu da addu’a Allah ya bamu ikon cinye jarabawarmu”
Ba qaramin sanyi kalamansu sukasa jikin Hajiya yayi ba ta dubesu a sanyaye ta tsugunna ta kama hanun Umaimah hawaye ya kwace mata tace “mar’atussaliha baki cancanci suna Umaimah ba duk da itama asalin mai sunan sahabiya ce kuma baiwar Allah amma naso ace sunanki Fadimatu saboda halayyarki tayi kama data Nana Fadima itace macen da har kullum take fifita farin cikin mijinta fiye da nata Umaimah da ace a zamanin annabi Muhammad (S.A.W) mukazo inada tabbacin kina cikin khulafa’ul rashidun ko kuma kina daya daga cikin matan da annabi ya dafa kawunansu yasa musu albarka kuma ya roqa musu albarkar ubangiji duniyarsu da lahirar su tabbas ina alfahari da samun ya a gareni kuma Ina alfahari da kasancewarki suruka a gareni Umaimah dama ace inada wani dan bayan Hameed wlh rayuwarki bata dace da azzalumin mutum irin Hameed ba da kullum baya sanin haqqin kowa sai nashi tabbas mgnrki gsky ce addu’a zan tayaki da ita Allah ya kareki da sharri da makirci irin na jinin Hajiya Talatu kishiya juji shidai daya debo da zafi ya qare a bakinsa”
Miqewa tayi ta taka zuwa tsakiyar parlourn ta tsaya ta sake share hawaye ta juyo tace “bazan maka mugun fata a cikin aurenka ba kuma zan tayaka da addu’a tunda kaima nawane ban isa na canza maka suna ba amma ka sani auranka da Salma babu wani alkhairi saboda haka bacci ba naku bane ku daure ku rinqa tashin tsakar dare kuna salatulduha sannan ku rinqa azumi da yawan karatun qur’ani hakan zai zame muku kariya daga sharrin shaidan da sihiri ko wanne iri ne duk da kaidai ka riga ka shiga hanu wlh na sani kuma na yarda auranka da Salma aikin sihiri ne”
Tana gama fadar haka ta fice daga parlourn suka kalli juna ita dashi taga yanda yake kwararar da hawaye masu dumi zuciyarsa tana wani fat² tayi saurin rungumeshi tace “ina tare dakai mijina a kowanne hali ina fatan kazama kaine mijina a jannatul-ma’awah” miqewa yayi ya dagata cak bai damu da yawan mutanen da suke gurin ba ya haura sama da gudunsa saboda bayason surutu.
Duk wanda ke gurin saida ya zubar musu da hawaye Saudat Alfah tayi ajiyar zuciya tace “bantaba ganin soyayya me ratsa zuciya daban tausayi irinta Umaimah da mijinta ba wlh ko soyayyar Aunty Murjanatun mu da Muhammad mijinta batakai wannan soyayyar dadin kallo da burgewa ba tabbas Umaimah yar aljannah ce kamar yanda Hajiya ta fada saboda dukkanmu na tabbata babu wadda zata iya yiwa mijinta wannan sadaukarwar qaunar akan kishiya kishiyar ma wacce take barazana ga rayuwarta da lafiyarta da mijin ma gaba daya dole mu jinjinawa Umaimah Umaimah na sallama miki kinyi nisan da bazamu tadda ke ba”
Sukuwa suna haurawa ya direta a gado ya fara romance dinta ta riqeshi da sauri tace “bloody muna da baqi fah a gdannan ka sani” lumshe idonsa yayi yaci gaba da matsata kamar lemon tsami yana cire mata kayan jikinta yana cewa wlh ko a gabansu zan iya turmusheki Hearty inajinki a duk wani bangare na jikina bloody soyayyar jini daban take da kowacce soyayya a duniya baayi kamarki a duniyata ba kuma ba zaayiba kece farko kece qarshe Umaimah ni da ke abu dayane zuciyarmu daya jininmu daya komai namu dayane Umaimah”
Da wadannan kalaman suka fara tsotse kansu suna shafe²nsu wanda Allah ya sani Umaimah badon dadi takeyi ba tanayi ne kawai donta faranta masa saboda ta lura yayi nisa sosai saida ta tabbatar ta gamsar dashi suka shiga sukayi wanka sukayi sallar azahar ya tayata ta shirya tsaf cikin wata atamfar Super Holland ja tayi kyau matuqa duk da ramar da tayi shima ya shirya cikin wani blue din yadi dake jikin atamfar tata da blue saiya zamana kamar anko sukayi nan fa suka bata lkc wajen yin hotuna sune har parlour ana suba selfie sudai su Aunty Jameelah da Aunty Zarah da Sa’ud da sauran mutane sai suka zama yan kallo a gdan suna sha’awar soyayyar ma’auratan.
Bayan sun gama haukan selfie dinsu suka zube a parlourn suna dariya dariyar tasu saida tasa kowa ma dariya harga Allah shidai ya manta da mutane a parlourn saida yaji sunyi dariya ya shafa kai cike da kunya yace “inajin yunwa bloody” miqewa tayi ta shiga kitchen ta zubo masa abincin da su Aunty Zarah suka girka ba kunya ya noqe kafada yace “muje na tayaki muyi namu ni duk abincin daba hanunki ne ya girka ba ba dadi yakeyi min ba”
*UMMUH HAIRAN CE…✍????*