Hausa Novels

Lu’u Lu’u 44

*44*

 

Saida ta dasa aya ya kalli idonta yace “Wani abu ne ya ke damunki to?”

Kyab’e baki tayi a sanyaye tace “Ni ma ban sani ba.”

Jinjina kai yayi ya d’an ja baya kad’an yace “To ci.”

Da sauri ta gyara tsayuwarta ta kai sandwich d’in nan data had’a baki ta gutsira, lumshe ido tayi tana taunawa tana jin dad’inshi a bakinta har kwanyar kanta, kallonta yake shi kuma ya gyara tsayiwarshi kamar ya samu tv.

Tana tsaka da ci ko rabi bata ci ba wata hadimar ta shigo ciki, da girmamawa ta sunkuyawa tace “Uwar gijiyata, mai martaba sarki na son ganinki yanzu.”

Kallon sandwich d’inta tayi sannan ta kalli Umad, ajewa tayi ranta a jagule sannan ta nufi hanyar fit, da kallo ya bita har ta fita sannan shi ma ya bi bayansu.

Tana zuwa ta samesu duk tsatsaye, da mamakin yanda suke tsaye wurin da kuma cika d’akin taron da ya sake yi da mutane wanda ke nuni yanzun kamar jama’ar gari ne kuma duk gasu tsaye ta k’arasa ta tsaya tsakiyarsu, gashi duk hankalin mutane ya dawo kansu yanzu, kallon Juman tayi tace “Mah, lafiya ?”

Lumshe mata ido tayi alamar lafiya lau, Umad ma na fitowa kai tsaye wajen grp d’inshi na aika ya nufa inda Haman ma na tare da su har kuma shugaban su da sauran abokanan aikin, shi ma dawo da hankalinshi yayi kansu saodai idonshi na kan Ayam, duk wani motsinta a idonshi yake wakana.

Sarki Musail ne ya d’anyi gaba kad’an sannan ya d’aga murya yace “Jam’ar Khazira d kewayenta, yau babbar rana ce a gareni da ku baki d’aya, rana da kuka jima kuna tsammanin zuwanta, ranar da wasunku suka shafe shekaru suna mafarkin tambayar yaushe za ta zo? To ga ta ta zo yau, yau rana ce da ni sarki Musail zan yi murabus daga kujerata, sannan na d’ora wacce ta fi cancanta, wacce ku ka dinga tsumayin ganin ranar da zata karb’i mulki daga hannu na, Zafeera.”

Ya fad’a yana juyowa inda take tsaye sai zazzaro ido take kamar ta had’iyi kunama, sake maida hankalinshi yayi kan mutane yace” Har cikin ziciyata na yarda da sabon tsarin da za ta gina muku, tun kafin na haifi abuta na san da zata kawo haske a k’asar nan, dan haka ina mai baku shawara da ku mata mubaya’a ku bita a cikin tsarin mulkinta, dan wainar da zata toya sai da ku zata toyata, idan har kun amince da haka sai ku fad’a mu ji.”

Cikin d’aga murya maza da matan suka amsa tare da d’aga hannunsu suka ce” Mun amince, mun amince.”

Murmusawa yayi ya juyo ya kalli Ayam ya kamo hannunta, irin tsoron dake fuskarta yasa shi d’an rusunawa cikin rad’a yace” Ke fa yanzu sarauniya ce, wannan fuskar tsoron na ki za ta sa talakawanki su rainaki, sannan su miki kallon wacce ba jaruma ba.”

A marairaice tace” Amma Pah ai dama ni ba jaruma ba ce ko?”

Girgiza kai yayi tare da lumshe ido yace” Ba dai ‘yata ba, da ba daga tsatsona kika fito ba, sai na yarda idan kin fad’i haka, now smile.”

Kallon mutanen tayi ta saki murmushi mai kama da kuka, kama hannunta yayi ya d’aga sama alamar ta karb’i mubaya’ar da suka mata, hakan yasa d’akin taro ya kwashi wani irin ihu mai k’arfi da hayaniyar mutane tare da tapawarsu.

Har su Musail d’in da su Juman Abdallah duka dake nan tare da ita tapi suke mata suna murmushi, hadimai biyun dake tsaye gefe da wani abu kan faranti ne suka matso kusa, juyo da ita Musail yayi suka fuskanci juna yace “Gwiwarki d’aya k’asa dan karb’an kambunki.”

Idonta taf da hawaye tace “Pah kar ka d’ora min nauyin jama’a, bana da sha’awar hakan.”

Cike da k’auna ya shafa kumatunta yace “In Shaa Allah, da izinin Allah subhanahu wata’ala za ki iya Ayam.”

Tar tar ta kalli k’wayar idonshi cikin na ta, kamar sub’utar baki ba tare da tasan bakinta zai fad’a ba tace “To Pah *mijina* fa? Ya zan yi da aurenshi da ke kaina?”

Juyawa yayi ya kalli Umad, wani murmushin shak’iyanci Musail d’in yayi, yaron na birgeshi sosai saboda shu’umi ne, wato har ya gama kassara masa yarinyar sa dai ta ciki da ta waje ? Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya kalleta yace” Kar ki damu da shi, ya amince da hakan.”

Sake langab’ewa tayi zatayi magana sai ya had’e fuska dole ta k’yale, a sannu sannu ta durk’usa yanda gaba d’aya rigarta ta rufe komai na ta ko k’afafunta ba’a gani, duka gwiwan ta durk’usa ta sunkuyar da kanta, hakan da tayi yasa Musail cire kambun dake kan shi na gwal ya d’ora mata kan babban mayafinta dake saman kai har yana jan k’asa, jin kambun ya hau kanta mutane kuma sun sake kaurewa da tapi da fad’in “Jinjina, sai kin yi sarauniya Zafeera, abun bauta ya tsareki.”

Sharrrr ! Hawaye suka wanke mata fuska, tallabota yayi ta mik’e ya d’ago fuskarta, girgiza mata kai yayi ganin tana hawaye yace “Bana so fa.”

Maida kallonshi yayi ga hadiman nan biyu da suka matso, bud’e kyalen sukayi mai k’yalli kalar ruwan zaiba, hakan ya bayyanar da wata kyakyawar sark’a mai kalar ruwan zaiba ita ma sai wani dutsi a tsakiyarta ja mai suffar kan zaki, d’auka yayi ya nufi wuyanta yana fad’in “Yanzu za ki zama sarauniyar Khazira, daga yanzu nauyinsu ya bar kai na zai koma kan…”

Sautin k’akk’arfan numfashin Musail ne kawai ya ratsa wurin amma ba’a ji k’arar harbi ba, Ayam dake daf da shi jinin jikinshi ne ya fallatsa zuwa fuskarta da jikinta baki d’aya, kafin ta fahimci me ya faru? Sai ihu da hayanyar mutane ce ta gauraye wurin.

Tartsatsin ihun Juman ne ya sa ta firgita ta juya ta kalleta sabda yanda tayi ihun ta fashe da kuka, hakan yasa a rikice ta kalli inda mahaifinta ke tsaye, saidai ina kwance ta ganshi sai neman rai yake amma yana k’i ya ma sa, sai numfashi yake sama sama yana had’iyar abu a mak’oshi, a hankali a hankali kuma idonshi sai suka fara lumshewa, labb’anshi ta kalla da yake furta “La’ilaha illallah, Muhammad rasulillah sallalahu alaihi wa’sallam.”

D’ago hannu yayi yana son rik’o hannun Ayam saidai take rai yayi halinshi, duka tana kallon komai dake faruwa, a gaban idonta har ya cika da kalmar shahada, sark’ar da yake shirin saka mata ta kalla wacce ya saketa ta fad’i k’asa.

Tunda suka ga abinda ya faru Haman da tawagarsu suka bazama da azama tare da sanar da hadiman sarakunan uku cewa su shiga ko ina su duba, Haman da wasu daga cikin yan tawagarsu da gudu suka haura ta inda harbin ya fito, saidai suna zuwa suka samu d’aya daga cikin fadawan sarki Musail kwance shi ma cikin jini an harbeshi, kuma ga dukkan alama shi ne yayi harbin dan kar ya tona asiri shi ma aka kashe shi.

Sanda mutane ke ta hayaniya wasu na son fita daga wurin wasu kuma suna lek’a abinda ke faruwa, lokacin Ayam ta dawo daga d’imuwar da tayi na wasu sakanni.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button