MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

3️⃣
_____hannu ta sa za ta murɗa handle ɗin ƙofar amma kafin ta kai ga yin hakan sai ji ta yi an janyota daga baya. Ɗago ido tayi a tsorace ta kalli mai wannan ƙarfin halin, Dr. Nasir ne hannun sa riƙe da kayan aiki. Kallon ta ya yi cikin mamaki yace, “me kuma kike yi a nan *UMMI?*”
Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tace, “bugun zuciyata ta tsananta…babu shakka maganin cutata yana cikin wannan ɗakin”.
Tsaki kawai Dr. ya yi don shi yanzu kam lamarin nata ya fara ba shi haushi yace, “gaskiya Umma akwai abinda yake damun kan wannan yarinyar…da akwai buƙatar akai ta asibitin motsattsu don a duba ta a can”.
Yana gama faɗin haka ya shige cikin ɗakin haɗe da banko ƙofar da ƙarfi bam!.
Sake kai hannu ta yi za ta buɗe cikin fushi Umma ta riƙe hannun na ta ba tare da tunanin komai ba ta wanke ta da mari. Nuna ta ta yi da ɗan yatsa kafin tace, “wannan haukar taki ta ishe ni haka! Na gaji da biye miki kina zubar mana da mutunci, *UMMI*. Da abinda za ki saka mana kenan?” Umma ta tambaya cikin ɓacin rai.
“…Yanzu mun cancanci irin haka daga wajen ki? Shikenan idan abinda kika zaɓa kenan….ALLAH ya ba ki sa’a”. Tana zuwa nan, fuuuu! Ta yi gaba ta bar ta tsaye a gurin.
Komawa ɗakin da aka ƙwantar da *Ummi* ta yi ta zauna duk abin duniya sun taru sun yi mata yawa. Tabbas ta san komai akan zancen *MUSADDAM* amma ita ba ta taɓa tunanin abin zai kai har haka ba.
“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un!” shi ne abinda kawai take iya faɗa da nanatawa.
*UMMI* kuwa ji ta yi kamar ta buɗe kofar ta shiga amma ganin yadda Umma ta bar ta a wajen tana sharar ƙwalla ne hakan yasa ta ji sam ba za ta iya barinta ta ta fi wata sabgar ba. Don dole ba don ta so ba, ta kama hanyar komawa ɗakin nata amma idanuwanta na kafe a kan ƙofar waccan ɗaki da ta so shiga, sai waiwayen kofar take.
*********
*MUSADDAM* kuwa baccin sa yake mai daɗi da kwanciyar hankali a sakamakon allurar da Dr ya yi masa. Jin wani irin mummunan bugun da zuciyarsa ta yi ne yasa shi farkawa a firgice bakin sa ɗauke da addu’a.
Dafe saitin kirjin nasa ya yi yana sauraron yadda bugun zuciyar ta sa ke ƙara tsananta wanda hakan ya yi daidai da lokacin shigowar wata nurse dake aiki a asibitin wadda ta shigo ne don duba halin da yake ciki. Inda ganin shi a wannan yanayin ne yasa ta koma da gudu don kirawo Dr.
*MUSADDAM* kuwa sake damƙe ƙirjinsa ya yi yana karanto duk wata addu’ar da ta zo bakinsa don ji yake tamkar ya zo gangarar barin duniya. Ɗaga kansa sama ya yi a galabaice yana faɗin, “ya ALLAH ina da tabbacin kai ka jarabe ni da son wadda ban taɓa gani ba, ALLAH kai ka san ta kuma kai ne wanda ya halicce ta. ALLAH ka bayyana min ita a duk inda take…” yana kai wa nan ya fashe da kuka duk da kuwa da kasancewarsa jarumi kuma mai juriya akan duk wata jarabawa da za ta riske shi, amma abin mamaki wannan karon sam ya kasa nuna irin dakewar zuciyar da ya saban saboda ji da yake a ransa cewa wannan yarinya ita ce komai nasa. So kenan mai sanya hawayen maza kwaranya kamar an ɓalle cibiyar ruwan teku.
Ganin halin da yake ciki ya sa Dr yi masa allurar bacci. Sosai wannan lamari na *MUSADDAM* ya ba shi mamaki. Domin da farko dai abinda ya karanta a tattare da shi gajiya ce sai kuma alamu na damuwa, yanzu kuma ga shi bugun zuciyar sa na ƙara sauri wanda hakan alama ce dake nuna cewa damuwar ta sa ta ninka wadda yake ciki a baya. Wasu magunguna ya rubuta masa sannan ya fice daga ɗakin.
Ko da ya fita sake yi wa mummy bayani ya yi akan sabon lamarin da ya nazarta a tattare da ɗan nata wanda shi kan sa ya yi matukar mamakin faruwar hakan.
Ajiyar zuciya kawai ta sauke cikin jimami kafin tace, “Ni dai don ALLAH ka taimake ni kar ka bari wani mummunan abin ya faru da ɗana…ka fi kowa sanin daga shi sai ƙanwar sa kawai na mallaka a duniyar nan” kuka ne ya kwace mata sosai.
Ganin haka yasa Dr ya kwantar mata da hankali tare da ba ta tabbacin zai yi iya iyawarsa don ganin ya koma daidai sannan ya samu ta dawo hayyacinta shi kuma ya nufi ofishinsa.
************
Yanzu ma kamar kullum, irin dai wannan mafarkin yake, wata yarinya ya gani zaune tana zubda hawaye tana kiran sunan sa, ” *MUSADDAM* kana ina? Ka zo ka taimake ni…zuciya ta za ta fashe. Ka sani kai ne kawai nake da burin kasancewa da shi cikin duniyar nan. Don ALLAH ka zo kar ka bari su tafi da ni…”
Suna cikin haka wasu mutane wanda ba ya iya ganin fuskar su kamar dai yadda ita ma ba ya ganin fuskarta sosai suka zo suka tafi da ita. Kuka take mai sauti tana kiran ” *MUSADDAM* kar ka bari su tafi da ni don ALLAH ka cece ni”.
Wani irin ihu ya yi yana mai kiran sunan ta hakan ya yi daidai da shigowar mummy wanda ihun sa yasa ta banko ƙofar da dukkan karfinta ta shigo.
Kallon kallon suka yi wa juna sai a yanzu ne kuma ya fahimci har ila yau dai ashe mafarki yake. Sadda kai yayi ƙasa tare da dafe sa da hannu guda yana tunani. Inda yake kwance mummy ta zo ta riƙe masa hannu tana cewa, “me ke damun ka ne ɗan nan? Ka faɗa min mana….shin kana da wacce zaka faɗawa damuwar ka sama da ni ne abcikin duniyar nan? Shin ba ka san cewa kai ne sanyin idaniya ta ba? Dubi duk yadda hankalina ya tashi saboda rashin kwanciyar hankalinka…Don ALLAH kar ka bari damuwa ta sa na rasa ka ka ji ɗan nan?”.
Kuka mummy take sosai, gabaki ɗaya jijiyoyin kan sa suka mimmiƙe saboda tsabar yadda yake jin raɗaɗi a zuciyar sa, “wai saboda ni mummy take zubda hawaye?”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!!!” Damƙe hannun ta yayi a cikin nasa yace,”momma na yi miki alƙawarin daga yau ba za ki sake ganin damuwa akan fuskanta ba, don ALLAH ki daina kuka wallàhi kukan ki ƙona min rai yake”.
Murmushi ta yi dukda hawayen dake cigaba da gangarowa bisa fuskarta tace, “idan ka yi min haka zan yi farinciki sosai”.
“Na yi miki alƙawarin haka momma”. Da haka suka shiga wata hirar har dai ya ji komai ya lafa na daga wancan mafarki da ya yi amma abin na can ƙasan zuciyarsa.
***********
*UMMI* kuwa tana komawa ɗakin ta iske Umma tana zubda hawaye zuwa ta yi ta rungume ta ita ma kukan take sosai don kuwa har yanzu tana jin wannan matsanancin bugawar zuciyar wanda tsabar bugawar da ƙirjin nake yake da karfin gaske ji take tamkar zuciyar ta ta za ta faso ta fito waje.
Sai da suka yi mai isar su sannan *Ummi* tace, “umma don ALLAH ki gafarce ni, ni dai kawai addu’a nake da buƙata a gunki ba komai ba, Umma kin sani wannan kukan naki babu abinda zai haifar sai ƙarin damuwa a guna”.
Janyo ta umma ta sake yi jikinta tace, “na fahimci halin da kike ciki amma don ALLAH ki rinƙa sassautawa kanki…idan har addu’ar uwa ba ta da shamaki kuma idan har *MUSADDAM* alkairi ne a gurinki ina mai tabbatar miki duk tsayin lokaci zai iso gare ki insha ALLAH”.
Nodding da kanta kawai ta iya yi alamar gamsuwa. A rungume jikin umma ta yi bacci mai cike da mafarkan *MUSADDAM* ɗinta. Ganin ta yi baccin ne yasa Umma ta kwantar da ita. Lura da yadda bakin ta ke motsi a hankali ne yasa Umma kasa kunne don jin abinda take faɗa, “Umma *MUSADDAM* ne zaɓi na da shi kawai nake son yin rayuwa..Umma ku taimaka ku ba ni *MUSADDAM*”.
Share hawayenta Umma ta yi tace, “ALLAH ka kawo mana mafita cikin wannan lamarin, ALLAH idan wannan buri na ta shi ne alkairi ALLAH ka tabbatar mana”.