HAUSA NOVELNOVELSSADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI

 

 

 

……………Wani matashin saurayi nehh wanda bazai wuce shekara goma sha hudu ba saurayin yana rike da wata jaririya wadda bazata haura wata uku ba a duniya

 

 

Gudu yake yi na fitar hankali wanda da gani gudun ceton rai nehh yana gudu yana waigawa bayan sa a matukar tsorace sabida gani yakeyi a koh da yaushe dakarun birnin Hindu zasu iya cimmasa

 

 

 

Bai gushe ba yana wannan gudu ba tun safe har rana ta soma faduwa anan nehh gajiya ta riskeshi ya zube kasa yana mai fitar da numfashi sama sama a yayin da ya yar da yar jaririyar dake hannun sa chan gefe daya tana mai tsala kuka

 

 

 

Bayan wani dan lokaci nehh wannan ya jiyo sukuwar dawakai ta koh ina suna masu kusantoshi da alama sun zagayeshi ta koh ina

 

 

 

 

Da sauri ya dauki jaririyar nan yana mai rufe mata baki sabida ta daina kukan da takeyi

 

 

Amma ina aikin gama ya gama sabida wannan jaririyar ta Riga da ta fallasa shi sakamakon kukan da takeyi tun dazun

 

 

 

A hankali yaji takun sahun dawakan yana mai kara kusantoshi nan take hankalin sa yayi masifar tashi sabida baisan yarda zaiyi ba dabarar sa ta kare yana cikin wannan yanayin nehh ya hango wani kogo daga chan nesa dashi kadan

 

 

 

Da sauki ya tashi yana tafiyar sanda dan kada suji takun sahun tafiyar sa yana isa kusa da kogon bishiyar ya fara kokarin shiga ciki amma ina bakin kogon yayi kankanta da yawa bazai yuwu ya shiga ba

 

 

 

Sabida haka nehh hankalin sa ya Kuma tashi ya rasa dabarar da ya kamata yayi

 

 

 

Bayan wadansu yan dakiku nehh wata dabara ta fado masa kawai sai ya zagaya bayan wannan bishiya ya labe yana buya kuwa sai ga dakarun sun iso kimanin su ashirun da doriya

 

 

 

Dakarun kowa yana rike da zabga zabga takubba masu matukar kaifi da tsini

 

 

Dakarun sin kasance zabga zabga tamkar bishiyar kuka sannan suna da kira tamkar mutanen farko ni kaina da naga wadannan dakaru sai da na tsorata

 

 

 

Wannan Matashin yaro yana make a bayan wannan bishiyar ya xuba musu idanu a matukar tsorace saida ya tabbatar da da sun kusa iso wa inda yake nehh yayi sauri ya ya cire rigarsa ya Goya wannan jaririya a bayan sa saida ya tabbatar y daure da kyau sannan ya dauki wani itace mai tsini da ya gani a kusa dashi ya gyara tsayuwarsa

 

 

 

 

Sai da ya tabbatar sun iso daf dashi sannan yayi fitar burgu daga bayan bishiyar yana mai kwala ihu kai tsaye yayi kan wani badakare yana mai tsala ihu yana isa daf dashi kafin badakaren yayi wani yunkuri tuni wannan matashin saurayi ya da ka tsalle ya kirbawa dokin nan wannan icen a yuwa take icen ya fasa wuyan dokin ya bullo ta daya bangaren nan take dokin ya sulale kasa matacce

 

 

 

Shiko wannan saurayi koh da yaga ya samu hanya saiko ya dauki hsnyar nan ya fita da azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya

 

 

 

Duk da ba ganin hanya yake yi ba sosae sakamakon duhun da ya fara mamaye gurin baki daya

 

 

 

Suke wadannan dakaru koh da suka ga abinda ya faru da dan uwan su sai suka kuma tunzura suka rufah masa baya

 

 

 

Abu daya nehh yake basu mamaki a game da wannan saurayi wato tsananin karfin gudun sa gashi dai karamin yaro mai karamar halitta amma idan ya huce gaban Abu to har abada bazai kamu ba fahh saidai idan shi ya tsaya da kansa………….

 

 

 

Wannan kenan idan naga yawan comments zanci gaba da typing idan naga akasin hakan to zan tsaya anan fatan alkhairi fans

 

 

WhatsApp number 08143314152

 

 

Vote
Comment and shared

 

 

 

By fast class
????????????????????
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
????????????????????

 

Writing by

ALIYU H ISHAQ
(fast class)

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

 

 

DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now

SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)

 

???? 5↔10

 

 

Dedicated to All my fans

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI

 

 

…………..Gudu wannan saurayin yake iya karfin sa iya kar iyawarsa dan ya tsere wa wadannan miyagun dakaru amma daya juyo bayan sa sai ya gansu daf dashi tamkar su mika hannu su damko shi amma ba damar hakan dan zullewa yakeyi tako ta ina

 

 

 

Koh da yaga wannan gudun bazai kai masa ba sai ya fara tunanin mafita sabida a koh da yaushe zai iya sarewa kuma ga wata yunwa dake nukurkusar cikin sa dan rabon sa da abinchi tun na jiya da safe da ya kwaci wata gurasa a hannun wani badakare ya gudu to shine wadannan dakaru suke ta binsa dan ganin sun kamashi su kai shi gurin sarkin su dan ya yanke masa hukunchi abisa laifin satar daya aikata da kuma dukan badakare

 

 

 

Yana cikin wannan gudun nehh ya tuna da jaririyar kanwarsa dake bayan sa ya Shafa yaji bata wani Motsi Alamar tana da rai nan take hankalin sa yayi masifar tashi ya juya yaga wadannan dakaru na Neman cim masa kawai sai ya dage ya kwala ihu dai dai karfin sa ya fita da wani mahaukacin gudu wanda bai taba yin kamarsa ba a rayuwarsa

 

 

 

Aiko kan kace wani Abu ya basu mahaukaciyar rata sai da ya zamana cewa basa Iya hango koh da kurar sa a cikin wannan Daji a wannan lokacin nehh ya hango wani kogon dutse mai matukar duhu duk yana ta rufe bakin sa

 

 

 

Ba tare da tsoron komai ba ya kuna kai cikin kogon sai da yayi tafiya Rabin sa a sannan ya isa karshen kogon

 

 

Yana isa ya zube sharaf a kasa sumamme ,

 

 

 

Suke wadannan dakaru koh da suka ga sun daina hango shi sai suka juya suka kada dawakan su suka koma da baya cikin matukar takaici dan wannan shine lokaci na farko da wani mahaluki ya taba sira daga sharrin su

 

 

 

Bayan wasu yan sa’o’i nehh wadannan dakaru suka isa cikin birnin Hindu fuskarsu ba Alamar annuri duk wanda yaga wadannan dakaru a wannan lokacin sai dai kaga ya dare ya basu hanya dan kowa tsoron su yake ji sakamakon dan ban zan zalincin su a cikin wannan birnin sarkin garin ya basu damar yin duk abinda suka ga dama acikin birnin sa sabida a kaf cikin dakarun birnin yafiji dasu har yana  musu lakabi da DAWAKAN AZABA,

 

 

Wadannan dakaru basu tsaya ako ina ba sai a gidan sarautar birnin tsayawa fadin yarda gidan sarautar ya tsaru ma bata lokacine fans ta tsaru matukar tsaruwa

 

 

 

Kai tsaye suka wuce cikin fadar SARKI DARRAJU IBN KULMAN dan dama basuda wani shamaki acikin wadannan gidan sarautar

 

Wata tamgamemiyar kofahh ta zallar zinare ita kanta kofar abar kallo ce kai tsaye suka kunna kai cikin fadar

 

 

Lokacin da nayi ido hudu da fadar sarki darraju saida hankalina ya kusa Barin jikina bansan sanda yawu ya rika diga daga bakina ba ba abinda ya bani mamaki sai yarda naga tsarin fadar yake gabaki daya ginin fadar anyi shi nehh da zallar zinare da yakuta da jauhari da sauransu girman fadar ya kai girman gari guda

 

 

Tako ina jama’a nehh makil an cika ana ta fadan ci daga chan nesa kadan na hango wasu tsala tsalan yan mata sun zage sai tikar rawa sukeyi gefe daya makada nehh da maroka suke ta aikin su na koda sarkin

 

 

 

Daga Chan sama na hango wata rangadediyar kujera ta zallar zinare a bisa wannan kujera SARKI DARRAJU nehh zaune ya hakin ce akan kujerar nan fuskarsa tamkar bai taba Dariya ba a duniya

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button