HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga gabatar da wasu ayoyi cikin Alkur’ani mai girma yana hurawa cikin ruwa, saida ya shafe kusan awanni uku yana abu ɗaya ba tare da nuna gajiya ko kuma ƙosawa ba,rerawa yake ciki shauki da nuna tsantsan jin daɗin sa a fili.

Saida ya gama tsaf sannan ya umarci faruq daya shafe masa duk kan ilahirin jikin sa da wannan ruwa.

Haka kuwa akayi Allah cikin ikon sa *Musaddam* ya fara motsawa, buɗe idanuwan sa yayi tangaran yana kallon kuwa,abin mamaki so yake yayi magana amma bakin sa yaƙi buɗuwa, nuni ya fara yiwa faruq da bakin sa hawaye masu zafi suna kwarara a kuncin sa.

Kallon sa *Ummi* tayi ta fashe da kuka tana cewa,”Yaya faruq cewa yake baya iya magana bakin sa baya buɗe wa Shikenan na shiga uku na”.

Sai a sannan Faruq da sauran jama’ar ɗakin suka fahimci abinda yake faɗa……

*Safnah Aliyu jawabi* 08136746004
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

*_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_*

3️⃣0️⃣

 

“_*Don’t judge a person based on just one particular clip you saw of them. It’s unfair. It could be fake, edited or taken totally out of context. Be mindful. The damage we’re doing to ourselves and others by such opinions can have disastrous effects on us in this world and the next.”*_

 

_________ Abin mamaki sosai *Ummi* take kuka kamar ran ta zai fita, kallon ta kawai *Musaddam* yake duk da kuwa yana cikin tashin hankali amma hakan bai hana shi mamakin wannan kukan ba, gaba ki ɗaya sai yaji ya mu zanta saboda shi mace take kuka haka”?

Yanayin kallon da yake mata yasa ta share hawayen ta cikin sauri, dawowa kusa dashi tayi tace, “Sannu kaji Yaya na in sha Allah zaka warke kuma na daina kuka zanyi maka addu’a sosai kaji? kuma kai ma ka daina dan Allah”.

Nodding da kai kawai yayi mata yana matuƙar mamakin yanda akayi take fahimtar abinda yake faɗa koda kuwa bai furtata a baki ba.

Murmushi kawai Ka’ka yayi yace, “Tabbas akwai abinda ya gani wanda basa so  ya tona musu asiri, to Allah cikin ikon sa wannan mai rawar kan tana fahimtar zancan sa koda kuwa bai furta ba”.

Sunne kanta kasa tayi tana mai saka jin daɗi da farin ciki yana lulluɓe ta. Allah cikin ikon sa kuwa aka fara magani cikin nasara, cikin gari faruq ya shiga ya harhaɗo masa magunguna kama daga habbatus sauda da dai sauran magungunan da suka shafi gargajiya,a gefe guda kuma ga Dr yana zuwa domin duba ciwon kan dake jikin sa.

 

Shaƙuwa ce mai ƙarfi tsakanin *Musaddam*  da  *Ummi* dan kuwa komai yanzu tare suke yi idan ta tafi kasuwa har ta dawo ba zaka taɓa ganin fara’ar sa ba har sai ta dawo, abinci ma a tare suke ci sai dai shi Faruq ke bashi a baki ita kuma tana daga gefe tana cin na ta, abin dai gwanin burgewa. sosai *Ummi* take bashi kulawa ta musamman dan kuwa lokuta da dama  ba yunwan take ji ba, amma sanin cewar idan bata ci abincin ba shima fa baci zaiyi ba, haka yasa take daurewa taci wani lokacin tana gama ci take amayar dashi gabaki ɗaya.

 

Lokuta da dama shi kanshi yana mamakin yanda akayi yake jin yarinyar a jikin shi irin haka, abinda ya sani shine yana matuƙar jin cewar yana da gata idan har yana tare da ita, yana jin cewa itace jinsa da ganin sa dan kuwa ita kaɗai take iya fahimtar sa koda kuwa motsi yayi, sosai lamarin yake bashi mamaki, yau ma kamar kullum zauna yake ya jingina bayan sa da bangwan ɗakin kamar yanda Ka’ka yace, lumshe idanuwansa yayi yana karanto suffofinta masu ɗaukar hankali…..Murmushin ta rigimar da suke da Ka’ka yanda take masa shagwaɓa ko magiya idan yaki shan magani ko abinci, yanda take tsare shi da idanuwa idan ya kalle ta tayi saurin sunkuyar da kai, yanda take kuka idan jikinsa ya tashi, yanda take bashi kulawa, yanda take saka shi gaban tana masa kira’a .

komai  nata abin birgewa ne, wani ƙasaitaccan murmushi ne ya suɓuce masa yana mai shafa sajan fuskar sa.

Motsin da yaji kusa da shine yasa yayi saurin buɗe idanuwan sa, itace dai tsaye fuskar ta dauke da murmushi, ina kwana tayi masa tana mai ɗan durku sawa.

Hararar ta yayi cikin wasa yana wani ɓata fuska.

Marairaice fuska tayi tace, “kayi haƙuri banzo da wuri ba, wannan tsohuwar itace ta sakani aiki da sassafe haka, kawai ni dai na lura so take taga na tsofa da wuri na koma kamar ta”.

Dariya ne ya kubce masa dan kuwa duk yanda yaso ya riƙe dariyar abin ya faskara wannan yarinya akwai rigima, idan ba haka ba ta ya ya daga yin aiki sai ki tsufa”?

Murmushi tayi tace, “Nasan mamakin magana ta kake ko Yaya *Musaddam?* to Allah da gaske yawan aiki yana tsufar da yara irin mu”.

Wannan karon murmushi kawai yayi. yayi mata nuni da ta zauna , tambayar ta yayi da hannun alamar shekarun ta nawa, rufe fuskar ta tayi alamun kunya tace, “Karfa ka min dariya idan na faɗa maka tom’”.

“Shekaru na ashirin da ɗaya yanzu”.

Buɗe baki yayi yana mamakin girman jiki irin na wannan yarinya duk da kuwa ita ɗin ba mai jiki bane ba amma dai kallo ɗaya ba zaka taɓa kawowa iya shekarun ta kenan ba.

“Yaya *Musaddam* kar dai mamaki kake dan kaji shekaru na?”

Girgiza kan sa yayi yana kunshe dariyar sa, haka dai suka cigaba da hirar su,har lokacin sallah yayi Faruq yayi masa alwala ita kuma ta shige gida cike da jin kewar muradin ran ta.

 

Abu kamar wasa jikin Musaddam yayi sauki sosai yanzu haka yana iya furta wasu tsiraron kalamomi wanda basu da tsawo duk da suma ba wani fita suke sosai ba.

Sosai Ka’ka yake tsaye dan ganin lafiyar *Musaddam* ya samu duk da kuwa barazanar da yake fuskanta, shi kansa abin mamaki yake bashi dan kuwa alamu sun nuna ba hannun mutum ɗaya bane cikin wannan lamarin dalili kuwa shine yanayin maganganun da ake zuwa masa dashi ya bambamta da juna, na farko cewa ake karya saka hannun sa ciki abinda babu ruwan sa domin kuwa wannan faɗan dangi ne.

Na biyu kuma gargaɗi ake masa da karya yarda yayi wani yunkuri akan wannan lamarin dan kuwa sun bi hanya mafi sauki amma abu ya faskara saboda haka wannan itace kawai hanya mafi sauki dan ganin sun nuna masa iyakar sa.

“Su waye bayin Allan nan? Menene wannan yaron ya tsare musu haka? Shin basa tunanin makomar su ne”? Allah ka bashi lafiya”.

Daga nesa yaji an amsa da “amin”.

Juyawa yayi cikin sauri yana mata daƙuwa yace”Yau naji ja’iran yarinyar wai meyasa kike bibiya nane duk inda na bi? Nace ba nayi ba nayi wai ana dole ne”.?

Dariya *Ummi* take sosai tace, “Tab nice zanbi ka bayan duk ka tsufa ka koɗe shine zaka wani min sharri, tab ko daura min kai akayi a ƙafa Allah sai na kwance”.

Shi kansa dariya yake dan kuwa duk cikin jikokin sa yafi son ta da kaunar ta, sai dai babu wanda zai iya fahimtar haka saboda ko da wasa baya nuna wa, yafito ta yayi da hannun alamar ta zo kusa dashi, rusunawa tayi ta yanda zata ji abinda yake faɗa, daidaita kanta yayi ya sakar mata rankwashi yana cewa, “Idan baki so tsoho ba ai gashi kina son kurma kuma mai almatsotsai”.

 

Ɗagowa tayi cike da mamakin yanda akayi wannan tsohon ya gano ta da wuri haka wanda har yanzu faruq shi sam bai ɗago komai ba, tashi tayi da gudu ta nufi ɗakin da take ƙwana ciki tsananin kunya, sam bata taɓa kawowa yana lura da ita haka ba….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button