TAKUN SAAKA 10
Ya ƙare maganar da takawa inda take maƙure a bango jikinta na rawa ya damƙi kunnenta da ƙarfi yana murzawa cikin yatsun hannunsa. Rawa jikinta ya farayi tana girgiza masa kanta saboda zafi.
Sakin kunnen nata yay yana dungure mata kai, yayinda sauran yayun nata da Ummi keta faman ambaton (innalillahi wa-inna ilaihirraji’un) a zukatansu. Yaya Abubakar ya cigaba da faɗin, “Ba wanann kaɗai bace damuwar Ummi, tunda har basu sami nasarar kamashi ba zargi zasu ɗarsa akanta itama. Dan zasu raba hankalinsu ne yanzu akan tunanin ko shine ya shirya komai wajen yin amfani da ita. Dan duk harin da jami’an tsaro ke kai masa ba’a taɓa cin nasara kamar nata ba da ya gudana cikin kanƙanin lokaci. Yanzu da zarar sun fitar da bayanai wa media cewar sun haresa, harin da kuma aka samu ci gaba a cikinsa fiye da na baya, to kowacce hukumar jami’an tsaro sai sun bibiyi yanda hakan ta kasance ta karƙashin ƙasa, walau jami’anmu nan gida kona ƙetare da ke nanuke cikin case ɗin kamar yanda suka saba mana kutse a cikin ayyukan daya shafi ƙasashenmu. Mu kuma bamu isa muyi koda tari akan nasu ba. A ƙarshe kowa ya bincika ita zai gano. Duk kuma zasu kasance wajen bibiyarta da mu kammu ba tsira zamuyi ba. Shima da ta aikata komai dominsa ba barinta zaiyi ba na sani.
“Ya ALLAH!”.
Ummi da ke neman faɗuwa ta faɗa tana fashewa da kuka. Da sauri sukai kanta gaba ɗaya suna ƙwala mata kira. A wani irin sarƙe numfashinta ya fara fita, ta fara tari.
Rikicewa suka sakeyi, yayinda kukan Hibbah ke ci musu zukata matuƙa. Cikin bada umarni Yaya Muhammad ya ce su dagata a kaita asibiti. Yanda ya faɗa ɗin haka sukai, sai dai suna fitowa harabar gidan ƴan sanda na shigowa. Basuyi yunkurin bi takansu ba. Sai dai muryar Abba da sukaji yana nuna Ammar da cewar shine ya kashe masa yaro ya saka hankalinsu rabuwa biyu.
A ɗan firgice Yaya Usman ya furta, “Kisa?”.
“Eh mara mutunci, ko ƙarya zan masa ne? Tun ɗazun likitoci suke akan Junaid amma babu alamar numfashi tare da shi, dan haka ku kamasa, inhar na rasa ɗana shima sai an kashesa.”
Tarin Ummi ne ya ƙara ƙarfi, sai ga jini na fitowa ta hancinta. Hankalinsu ne ya sake tashi. Sai a lokacinne Abba ya lura da halin da Ummi take a ciki. Maimakon ya saki batun ƴan sanda ya shiga sahun masu kula da ita, sai hakan ta gagara. A kausashe ya bama ƴan sandan damar kama Ammar yana tabbatar musu pretending Ummi keyi kawai.
Ganin duk sun shiga mota ƴan sanda kuma sun cukuykuye Ammar dake turjewa dan hankalinsa nakan halin da mahaifiyarsu ke ciki bata tasu yake ba. Yaya Muhammad ya cema Yaya Usman ya fita yabi ƴan sandan dan susan inda za’a kai Ammar ɗin. Su kuma zasu kai Ummin asibitin.
Badan yaso ba ya fita domin bin umarninsa. Dan duk da an haifesu babu wani yawan tazara a tsakaninsu hakan baya hanasu respecting junansu saboda ƙyaƙyƙyawan training da suka samu da ga mahaifiyarsu…….
★★★★★★★★★★★
A lokacin da wancan tashin hankali ke baibaye da ahalin Hibbah, anan headquarters ɗin ƴan sanda ƙoƙarin fitar da bayanan harin da Hibbah ta kaima master sukeyi. Sai dai kamar yanda Yaya Abubakar yay hasashe sunansu ne ya fito matsayin waɗanda sukai aikin. Sun kuma tabbatar nan da lokaci ƙanƙani zasu gurfanar da Master a saman gwiwoyinsa gaban duniya.
Babban abinda ya ɗauki hankalin jama’a da media baki ɗaya shine. Rahoton ƴan sanda na fita da mintuna uku kacal. Sai ga wani babban labari kuma da ga wannan shahararren ɓarawo mai suna *(MASTER)*. Ya fitar da jerin sunayen wasu manyan kaddarori na matar gwamna da mutane basu taɓa kawoma ransu hasashen tana da alaƙa da su ba a wani shafi nasa. Sannan ya rabasu a manyan gidajen redio da television ta hanyar tura musu saƙwanni kai tsaye a shafukansu na sada zumunta masu matuƙar muhimmanci da yawan mabiya.
Sosai ƙura ta tashi cikin lokaci ƙanƙani, manyan ƴan siyasa abokan takarar wannan jami’iyya suka samu damar baje kolin nasu faɗar albarkacin bakin dan dama tamkar kaɗan ake jira. Yayinda a gefe kuma da yawansu suke goyon bayan shi wanann master da ƙoƙarin wanke laifukansa a idanun mutane.
Fitar wannan kace nace keda wuya takardar gayyata ta bayyana da ga hukumar *(Yaƙi da ta’annatin kayan gwamnati)* zuwa ga matar gwamna. Acewarsu, suna gayyatarta zuwa ofishinsu da ga nan zuwa awanni ashirin da huɗu domin amsa musu wasu tambayoyi. Idan bataje da kanta ba, zasuje har gida su su ɗakkota.
Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga ɓangaren gidan gwamnati suma sun yunƙuro wajen maida murtani ta hanyar jifar abokan hamayyar TAKUN SAƘAAr nasu da dangantaka da Master. Suna mai tabbatar ma duniya lallai akwai lauje cikin naɗi. Sannan akwai ayar tambaya dangane da wanzuwar Master. Shin kodai? Kodai……????????.
Ta kowanne fanni gari ya ɗauka zafi, babu wani babban labari sai na wannan badaƙala ta TAKUN SAƘAA tsakanin Master da ya haɗa gurmin zuwa jami’an tsaro da na gwamnati. tare da ƴan siyasa da masu radin faɗin albarkacin baki. A gefe kuma ga talakawa ƴan bani na iya nata faman sharhi akan komai, kai kace agabansu aka ƙulla al’amarin……….
(????Wai, sunan wata karya. Sharaton. Bily aɗan dinga sassautawa dai????????????????????????????)
*________________________________*
Wani ƙayataccen murmushin da ya saka yaransa shagala a kallonsa ya saki lokacin da yake faman duba wasu da ga cikin Comments na mutane da ke wanzuwa a yanar gizo. Cikin salon ƙasaitarsa da izza ya wani juya kujerar da yake zaune cike da ƙwarewa yana lafewa a cikinta hankali kwance. Tare da wani salon da su kaɗai suke gane mi yake nufi idan yayi sa.
Dariya suka sanya cike da jin daɗin. Dan kobai faɗaba sunsan yana cikin farin ciki matuƙa. A duk sanda ya tada irin wannan ƙurar ya ga taja hankalin ƴan ƙasa da waɗanda yayi dominsu su kansu yakan yafe musu laifuka da sukai masa. Ko ya bisu da ƙyauta mai tsoka da ke sakasu farin ciki. Zai kuma kasance tare da su cike da nishaɗi duk da shiɗin ba mutum bane mai yawan magana akoda yaushe.
Da wannan damar Habib yay amfani wajen gabatar masa da rahoton binciken da ya gudanar akan aikin da ya basu ɗazun. Dan sun wuce adadin awannin da ya basu sosai. Kuma sunsan bawai ya manta bane, ya sharesu ne kawai bisa wani dalili nasa daban. Zatama iya yuwuwa shi tuni ya gama aikin binciken, suma ɗin ya sakasu yi ne kawai domin hukuntasu bisa laifin sakacinsu.
Komai baice akan takardun ba. Hasalima baiko buɗesu ba ya cigaba da duba sakwannin. Yayinda murmushi ke cike da ɓoyayyar fuskarsa da har ake ganin bayyanarsa bisa ta bogin da ke a kanta, wadda idan ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa cewa ba fuskarsa bace ba. Su kansu yaransa inda ace da ita kawai yake amfani baya canjawa tabbas zasu ce itace ainahin fuskarsa. Sai dai zuwa da mabanbanta da yakeyi ya sakasu fidda wanann hasashen a cikin ransu.
Ya kai tsahon lokaci tare da su yana bibiyar kowacce kafar yanar gizo da ta yaɗa labarai. Kafin ya miƙe yana faɗin, *“7:30am* zamu koma *L.E street.* Jahje na buƙatar bada ƙafa”.
Wani ihun farin ciki suka saka. Dan a gaba ɗaya gidajen da suke zama gidan *_L.E STREET_* yafi kowanne girma da ababen more rayuwa. Suna matukar mamakin yanda yake sama musu manyan gidajen da suke zama, a kuma manyan anguwanni batare da an farga shiɗin baneba. Tsabar hatsabibancinsa kuma a wasu lokutan sukan koma anguwannin talakawa su zauna har na tsahon wani lokaci. Haka suke tamkar fulanin tashi. Da wahala suyi zaman wata uku a gida batare da sun koma wani ba.