TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAKA 17

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._**_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

Chapter Seventeen_*

…………Haushi da takaicine ya turnike Hibbah lokacin da ta iso gida ta buɗe jakar da saurayin ya bata. Babu komai a ciki sai ƙaramar waya da ko number guda ɗaya babu a ciki. Sai wani shegen voice recording guda ɗaya da taji bata buƙatar sanin kona uwar miye. Wadrobe ɗinta ta buɗe ta cilla wayar ciki tana jan tagwayen tsaki. 

       Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai fita harkar waɗan nan ƴan sandan. Dan ta fahimci babu abinda zasu mata sai amfani da ita domin samin cikar burinsu tamkar yanda Yaya Abubakar ya faɗa. Inko hakane tayi alƙawarin bazasu sake ganinta ba……..

           Sallamar Ummi da tajiyo ne ya sata ajiye komai ta fito tana amsawa. Ummi ta kalleta da mamakin ganin yanayinta. “Tanee kina lafiya kuwa?”.

     “Lafiya lau Ummi, kainane kawai ke ciwo amma nasha magani.”

         “To ALLAH ya ƙara sauƙi. Kije ki kwanta kozai faɗa miki mu gani”.

           Kanta ta jinjinama Ummin dan dama haka take buƙata. Da wannan damar ta koma ɗakinta ta cigaba da nazarin neman mafitar da ya dace ta kuɓutar da ahalinta da ga abinda ƴan uwan mahaifin nasu suke shirin ƙulla musu.

        

       Koda Yayunta suka dawo ma tana jinsu ta kasa fita ayi hira da ita. Tana jiyo duk wanda ya tambayeta sai Ummi tace tayi barci kanta ke ciwo. Duk sun jajanta tare da nuna damuwa tamkar yanda suka saba. Daga nan suka ɗan taɓa hira kowa ya kama gabansa zuwa makwanci. 

      Duk yanda Hibbah taso yin barci a wannan daren ya gagara, babu abinda take sai saƙawa da kwancewa har asubahi, tana kuma idar da salla ta yo waje ta hau aiki. Lokacin da yayunta suka dawo salla suka samu tana aikin ba ƙaramin mamaki bane ya kamasu. cikin jan faɗa Ammar ya rike baki da faɗin, “Auta halan yau mafarkin zakici bulala hanun Ummi kikai ko? Inba hakaba kece yau da aiki a wannan sanyin safiyar”.

        Fuska Hibba ta ƙwaɓe kamar zatai kuka. “Yaya Muhammad ka gansa ko! Ni dai ai ban tankashi ba zai kama jana faɗa da safen nan”.

    Ranƙwashi Yaya Muhammad ya kaima Ammar akai, shi kuma ya kauce da sauri yana dariya da yima Hibbah gwalo. Su kansu su Yaya Usman dariyar suke ƙoƙarin dannewa. dan kowa dai yasan ɗan karan lalacin Hibbah akan aikin safe. Tanada kazar-kazar ɗin aiki amma banda na safe saboda shegen son barcinta. Ganin idan suka cigaba da tsiwa zata kufce musu yasa suka bar wajen da sauri. Itama sai ta cigaba da aikinta kawai.

       

     Ranar ita kaɗai tai aikin gidan, ta haɗa musu breakfast mai sauƙi sannan taje tai wanka ta fito. Yanzun kam gaba ɗayansu ido suka zuba mata ganin bata da walwala sam. Sai da taja kujera ta zauna Ummi da ke kallonta tace, “Ciwon kanne har yanzu?”.

      Kanta ta girgizama Ummi a sanyaye. “Ya daina Ummi, kawai dai banajin daɗin raina ne”.

         Shiru duk sukai suna kallonta cike da nazari. Yaya Usman da ke motsa shayi yace, “Auta akwai abinda kike ɓoye mana ƴan kwanakin nan. Sasai walwalarki ta ragu, kin bar zama hirar dare, ko yaushe kina cikin ɗaki. Shin kodai matsalar Shuraim ɗin ce har yanzun baki haƙura ba?”.

        Cikin ɗan rawar murya Hibbah tace, “A’a yaya ba shine ba. Ai nace muku na haƙura zan auresa. Dan nima zuwa yanzu na fahimci mutumin kirkine. Kawai dai ina tunanin ku ta yaya za’a raba ku da auren su Ameerah kamar yanda na samu kubuta daga auren Junaid. Yaya inaji a jikina akwai abinda su Abbah suke ƙullawa game da ku. Ni na rasa miyasa basa son mu? Mi muka tare musu ne a gidan nan? Minene laifinmu a garesu?….” takai ƙarshen maganar da saki kuka mai cin rai da ya saka su ajiye cokulan hannunsu su duka suka zuba mata idanu.

        Ummi ta rumtse kofin dake hannunta da ƙarfi. Wani irin ƙuna da ɗaci na sukar zuciyarta. Batare data farga ba harshenta ya suɓuce wajen faɗin, “Baku musu laifin komai ba Tanee. Sun tsaneku ne kawai saboda ni mahaifiyarku da ƙaddara ta kawoni cikinsu matsayin bara gurbi”.

      Gaba ɗayansu suka maida dubansu ga Ummi. yayinda kalmar bara gurbi data ambata tai matuƙar dakar zukatansu a lokaci guda.

      Cikin rawar harshe Ammar yace, “Ummi bara gurbi?”.

        “Eh Aliyu bara gurbi. Ƙwarai da gaske ni ɗin bara gurbi ce a cikinsu, domin kuwa samuwata ta kasance a jerin abinda mutane da yawa suke ƙyamata duk da muma ba laifinmu bane. Ba mune mukace a haifemu a haka ba. Bada son ranmu aka haifemu a haka ba. Kosu iyayen namu da ke haihuwarmu a hakan da yawansu badan sun so ba ne. Wasu ƙaddara ce ta jefesu da mu kawai.”

          “Kamar yanda kuka sani sunana Asiya. Mahaifina Sulaiman da mahaifiyata Muhibbah duk ƴan gida ɗaya ne. Dan kuwa ƴaƴan wa dana ƙani suke. Tun fil azal mahaifina bayajin magana. Dan mutumne gagararre na gaske da babu mai iya tanƙwarasa balle sakashi da hanawa.  Ba a asalin ƙauyenmu kawai ba, hatta da wasu kauyuka na gefenmu ana shakkarsa matuƙa gaya. Dan saboda hatsabibancinsa hatta da ɓarayi tsoron ratsa ƙauyenmu sukeyi. Tun tasowar mahaifiyata mahaifina ya nuna yana sonta, sai dai babanta yace sam bazai bashi ba, dan bai cika mutum ba. Wanann magana ta ƙona ran mahaifina, har takaisa ga yanke mummunar shawarar keta mutuncin mahaifiyata. A tunaninsa hakan kawai zaiyi a bashi aurenta. Dan ƙwarai da gaske yana son nata da gaken gaske.”

        “Gudun abinda zaije ya dawo ya saka baban mahaifiyata saka mata ranar aure da wani saurayi dake zuwa wajenta. Wannan abu ya ƙona ran mahaifina matuƙa, dan haka hamar yanda ya ƙudira haka ya zartar da wani yammaci, lokacin mahaifiyata ta dawo da ga aiken da akai mata gidan kakanninta, ya tareta a hanya yaransa suka ɗaukar masa ita. Kamar yanda aka sanarmin a wanann daren ya rabata da mutuncinta ta hanyar yi mata fyaɗe, ya kuma gudu ya bar garin washe gari da safe bayan fasuwar zancen da tsintar mahaifiyata da akai a yashe babu alamar rai tare da ita. Hankalin kowa ya tashi a ƙauyenmu, dan wannan shine na farko daya taɓa faruwa. Cikin ƙanƙanin lokaci magana ta yaɗu har ƙauyukan ƙetare, inda anan gida kuma kakaknina keta kai kawo akan ganin mahaifiyata ta farfaɗo. Da ƙyar aka samu ta farfaɗo, sai dai ta zama tamkar wata zautacciya, hakan yasa komai ya cuɗema iyayenta. Ga cece kucen jama’ar gari, gana ciwonta. Gana ALLAH ƙara da dangi suke musu akan tun farko su suka jamata. Inda sunyi haƙuri sun bama mahaifina aurenta da ba’akai ga haka ba. Maybe ma ya zama silar shiryuwarsa. In takaice muku zance sunsha matuƙar wahala kafin su ɗan samu kanta ta fara fahimtar abubuwa, sai dai kuma bayyanar samuwar ciki a jikinta ya sake rikita komai. Komai ya dawo sabo, dan kuwa sabon magana ya ɓalle ta kowacce kusurwar ƙauyenmu, kowa ya manta da ba laifin mahaifiyata bane, bakuma ta aikata da ganganba ƙaddarartace kawai tazo da hakan. Duk yanda kuke tunanin kakannina sunyi iya ƙoƙari na ganin cikin jikin mahaifiyata ya salwanta, sai dai hakan bata faru ba dan ALLAH yayi alƙawarin sai nazo duniya. ALLAH ya riga da ya ƙaddara sai mahaifiyata ta haifeni, dan haka ciki sai da ya kai har watannin haihuwa ta haifeni a wani dare na juma’a. Ina canyara kuka kakana na yanke jiki ya faɗi, faɗuwar da daga ita ko shurawa baiyi ba dan ya mutu. Hakama mahaifiyata tunda ALLAH yasa na fito da ga jikinta ta tada kanta da ƙyar ta kalleni hawaye na kwaranya a idanunta, tai murmushi mai ciwo da faɗin, “ALLAH ya albarkaci rayuwarki, ya ɗaga darajarki, ya kareki da dukkan sharri. ya saka haƙuri da juriyar duk abinda zaki gani a rayuwarki cikin zuciyarki” sai ta shafa kaina ta maida kanta ta kwantar shikenan anyita an gama.”

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button