TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAKA 20

 *_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azbazb

_________________________

*_Chapter Twenty_*

………….A can wajen ɗaurin aure kuwa babu jimawa ƙanin Momy ya dawo. Ta gefen Sheikh Aliy yaɗan ranƙwafo yana magana a hankali cike da alamar ruɗani. “ALLAH ya gafarta malam akwai matsala fa. Na kira Alhaji Halilu yana faɗa min wai a jirasa kar a ɗaura yana zuwa akwai matsala”.

        Sheikh Aliy da ke saurarensa ya ɗan juyo ya dubesa cike da nazari, dan haka kawai sai yaga tamkar ba’a cikin hayyacinsa yake ba, saɓanin ɗazun da ya fita kiran Abba. Fahimtar hakan da Garba yay ne ya sashi sauri gyaɗa kansa cikin son kauda ma malam shakku. Ya sake buɗe murya da ƙyau yana satar kallon na kusa da shi daya ɗaura masa bindiga a kan gefen cikinsa ta cikin malun-malun . “Inaga fa akwai wani abune da bamu sani ba game da su yaran nan. Dan ƴar uwata ma ta kirani akan a dakata”.

        Cike da wasiwasi Sheikh Aliy yace, “To sai dai mu dakata da su na ɓangarensu ɗin, bara a ɗaura wannan. Idan ya iso kafin a kammala kaga sai muji ba’asi ko?”.

         Garba da ke ta faman sinne kai ƙasa wata irin mahaukaciyar zufa na cigaba da tsatstsafo masa ya gyaɗa kai da sauri. Gaba ɗaya jikinsa rawa yake zuciyarsa tamkar zata tsinke dan firgici. Tabbas da yasan abinda zaiyi gamo da shi kenan idan ya tashi kiran Abba da bai tashinba ya kirasa anan gaban su Sheikh Aliyn.

        Su Sheikh Aliy da basu fahimci halin da Garba ke a ciki ba babu ɓata lokaci suka fara gabatar da ɗaurin aure. An fara ɗaura na Yaya Muhammad da ɗiyar Sheikh Aliyu mai suna Maimunatu, sai Yaya Abubakar da Zahidah. Yaya Umar da tasa amaryar mai suna Farida. Sai yaya Usman da Hafsat. Yayinda Muhibbat Aliyu Hamza Gwarzo da angonta Muhammad Shuraim Aliyu suka kasance a ƙarshe.

        Kowa yasha matuƙar mamakin jin yanda al’amarin ya canja. Musamman abokan Abba da danginsu irinsu Kawu Bello. Cikin yanayin shiga ruɗani Kawu Hannafi yace, “ALLAH gafarta malam yaya akai hakan ta faru?. Abinda mukai tunani ba shine muka gani ba mu anan?”.

      Sheikh Aliy da ya dago ya dubesa cike da kamala da sanin darajar kai yace, “Eh lallai an samu tangarɗa ne a tsarin, amma tun farko a haka yake dama. Gaba ɗaya anguna za’a aura musu mataye bib-biyu ne kamar yanda na sani, idan ka cire Muhammad Shuraim mai auran Muhibbat kawai. To sai kuma na samu bayani da ga ɗan uwanku ga shinan.”

     Ya ƙare maganar da nuna musu Garba da shi kaɗai yasan a halin bala’in da yake ciki. Da ƙyar ya haɗiye bushashshen yawun da ya tokare maƙoshinsa tare da ɗan duban inda Shuraim ya ke zaune. Sai dai abinda zai baka mamaki shi Shuraim ɗin ma bashi yake kallo ba. Hankalinsa ma baki ɗaya yana kan gaisuwa da mutane. Ya ɗan muskuta da duban na kusa da shi a kaikaice kafin ya fara jawabi tamkar zai fashe da kuka a ƙasan zuciyarsa. “Eh na kira Alhaji Halilu ne saboda rashin isowarsa akan lokaci, to to shine yake min bayanin a dakata da ɗaura auren ƴaƴan wajen nasa yana zuwa akwai da… Da damuwa”.

        Damuwa?.

Suka haɗa baki kusan tare wajen tambaya. Kai kawai ya gyaɗa musu yana kai hannu ya shafe zufar da ke tsatstsafo masa a goshi.

        Tsofo mai furfura da ke amsa sunan ƙanin Hajiya mama ya mike a fusace. “Wanann ai zancen wofi ne. Anya kuwa Halilu na cikin hankalinsa. Kunga ku tashi muje gidan sai muji ba’asin wannan lalatar da ga ina ta fito haka ne?”.

        Garba ne farkon mikewa kafin kowa. Cikin rawar jiki ya shiga kutsawa tsakkiyar mutane domin samun damar gujema Idris. Shima ɗin bai bisa ba, sai wani shegen murmushin ƙeta da ya saki a kaikaice yay salute ɗin sauran ƴan uwansa da ke cikin taron a maban-banta waje.

          

      To su dai sauran mutane da basusan mike faruwa ba tuni sun mimmiƙe suna mai mikama angunan da suma suke a daskare da tunanin mike faruwa? hannu da tayasu murna. Cikin yaƙe kawai su Yaya Muhammad ke amsa musu. Dan tabbas sun shiga matsanancin ruɗani da wannan lamari. Tabbas basa tunanin Abba zai janye ɗaurin auren nan babu gaira babu dalili cikin sauƙi haka. A kuma shirin Ummi da Sheikh Aliy babu zancen ruguje auren. Dama sun shirya cewar za’a ɗaura auren, za kuma su zauna da matan bibbiyu. Da ga karshe su ginama Abba gadar zaren amfani da yaran wajen ganin dukiyarsu ta dawo hannayensu. Amma ta yaya Abba zai janye auren a wannan ƙurarren lokacin bayan sun san harda shi aka fito zuwa wajen ɗaurin auren ma.

          Duk yanda sukaso son tsayawa su gaisa da ƴan uwa da abokan arziki da suka taru dan tayasu murna hakan ya gagara. Dole suka kwashi tawagarsu suka nufi gida kamar yanda su Kawu Bellon sukayi. 

          Wani mugun murmushi Musbahu ya saki lokacin da tawagar su Kawu Bello ke rige-rigen shiga motoci domin tafiya gida. Hannu ya kai bisa kunnensa ya gyara abinda ke maƙale, kafin ya fara magana cike da girmamawa. Yanda yake magana  hankali ne yasa babu mai jinsa, sai jinjina kansa da yayi tayi da kai  dubansa ga Zaidu da ke facing nashi. Da idanu yay masa alamar ya bi bayansu. Da alama yayi hakanne bisa umarnin wanda yake wayar da shi.

       Cikin masa jinjina Zaidu ya kaɗa kai tare da saurin buɗe motar gefensa ya shige ya rufama su Yaya Muhammad da suka wuce a ƙarshe baya. 

        Shima janye jikinsa yay da ga cikin mutane yana yima sauran alama cikin inkiya. Motocin da duk sukazo a cikinsu suka shishshiga. Da sauri shima Rabi’u da ya tuƙo Musbahu da ke amsa sunan Shuraim a fuska ya buɗe masa motar da sukazo. Duk wanda ya ga a yanda suka bar massallacin zai ɗauka suma sunbi bayan su Yaya Muhammad ne. Sai dai sam ba haka bane. Dan suna hawa titi duk suka rarrabu.

       Rabi’u da ke ƙara gudun motar yace, “Musbahu kira Habib mu haɗu a roundabout”.

         Musbahu na ƙoƙarin zare malum-malum ɗin jikinsa ya amsa da faɗin, “Okay ka ƙara gudu mu samesu muma, dan Master yace karmu ɓata lokaci”. Yay maganar yana ƙoƙarin kiran Habib ɗin da ke can tare da Hibbah, wadda har zuwa yanzun a cikin sumar abinda suka shaƙa mata take.

        Musbahu ya ajiye wayar da kallon  Rabi’u ta mirror. “Insha ALLAHU zamu isa a tare dan shima yana hanya”.

       Kai Rabi’u ya jinjina masa yana cigaba da tuƙinsa. Yayinda Musbahu ya kuma shiga ƙokarin kiran waya again. Ana ɗagawa daga can ya fara magana cikin tattaro nutsuwarsa. “Master komai ya kammala gamu nan a hanya. Kamar yanda kace kuma Zaidu ya bisu can”. Ya ɗanyi shiru yana sauraren mi ake faɗi da ga can, kafin ya sake faɗin, “Okay sir” cikin girmamawa tamkar yana  gabansa.

       Yana ajiye wayar Rabi’u ya fara dariya. “Angon bogi sai ka cire facemask ɗin tunda mun baro wajen”. Dariya shima Musbahu ya sanya da kai hannu yana ƙoƙarin zame facemask ɗin. “Ai ka bari kawai ɗan uwa. A kullum al’amarin Master ƙara tsoratani yake. Shi wannan auren kuma ko miye manufarsa? Oho. Kaga dai komai ya tafi tamkar yanda ya tsara. Yarinyarnan ta saka kanta a ramin *Damisa*”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button