NOVELSUncategorized

AHUMAGGAH 2

Motocin Suna gama parking agaban mu
Sai naga Wata kyakywar  hmsahkiyar mace ta fito da sauri tayo kan sa
 Salati ta fara yi sannan ta rusuna gabansa Tana jajantawa,shima da kyar yake mayar mata magana,

Ashe ma wani secret meeting ya fito da shugaban sojojin nigeria shine saii yan ta adda suka biyo sa

 sai naga sauran sojojin da suka fito daga toyotar sun tsaya sunyi jungum jungum anan dan dole aka sallame 
Saurayin nan aka karbe sunan shi da lambar sa,har soja guda daya ya raka shi har inda zaije 

Mukuma a cikin motar matan nan aka tafi damu.

Nidai sun bani mamaki sosai
Don A tunani na asibiti zamuje  sai naga kuma an dau wani  hanya
Anbi damu wata sabon anguwa 

Cikin wani boyayyen gida mai azabban kyau muka sauka

Sunan matar nan begham sahiba.

Tana da taushin hali ga yawan murmushi.tunda mutumin ya bata labari na take ta min murmushi da saukin hali

Anan naci abinci mai mugun dadi, nayi wanka na kwanta akan gado mai laushi 

Har sai washe  gari Kafin matar take tambaya na labarin meya faru,ban damu ba nayi mata bayani.
Kamar yadda shima mutumin ya gaya mata

anan tace min nayi kokari sosai dan kuwa bansan waye na taimaka a jiyan ba.

Tace nayi hakuri nadan zauna anan dan Babban hatsari ne su kyale ni na fita bare shikuma mai jinyar.

Dan haka ne tace ba zamu je asibiti ba sai an tabbatar da safetyn mu anga komai is set ba mai kuma bibiyar mu

Nikam bance komai ba nasan ko ansake ni ma bansan ina zan dosa ba,but Ni kaina Na fahimce cewa wannan din wani babban mutum ne,dan kuwa tsaro mai karfin bala’i aka saka acikin gidan
Da muke Wanda ya kasance daga ni sai shi sai wannan hamshakiyar mata.

Duk da ana bashi kulawa amma nima ina bada taimako na dai dai gwargwado

Wasa wasa har Sati biyu mai kyau mu kayi anan kafin har Allah yasa mutumin yawarke ya tashi akan kafar san.

Nan yasa aka kawo ni,muka gaisa sai yake tambaya ta tarihi na da inda za’a same iyaye na da gidan mu.

A wajen sa is a matter of my security shiyasa suka ajiye ni

 nikuwa ban boye mishi komai ba na fadi masa komai daga inda na fito.

Mutumin Yaji tausayi na sosai,sai ya aika aka kira begham sahiba.

Banji dai yace mata uffan daga abunda na fada mashi ba dai, sai ya danka mata ni amana A hannun ta,yace mata gani nan sai ta kula dani,na lura cewa Mutanen suna da kirki sosai dan har hakuri sukayi ta bani

Toh Tun Daga nan sai bansake ganin sa ba.

Da safiyar ranar aka saka shi awasu motocin kirarar bakaken Mecerdes maybech wanda kamannin su iri daya ne har bazaka gane wanne yake ciki ba.

Bansan ina za akaishi ba kuma ban tambaya ba. 


Nima Chan cikin dare bayan nayi isha’i na dan kwanta sai ga begahm sahiba,..
Kallo na tayi,sai na mike na zauna ina mai gaishe ta

Batare da wani dogon bayani ba tace min na biyo ta mu tafi
Sum sum na bita muka fita har waje,
 wata bakar jeep kirar nissan aka bude min tasha tinted babu tunanin zaka iya  gane komawa ne daga ciki

tare da begahm a seat din baya nayi zugum ana jan mu.

Tsawon awowi uku muna tafiya har bacci ya kwashe ni,sanda na bude ido na na ganni a wani gari wanda bansan inane ba.

Cikin wata katafaren gate aka bude aka shigar damu

A duk da bacci da gajiyan dake idanu na bai hanani kalle kalle ba dan kuwa rudewa ne kawai banyi ba.

Begham tace min sauko bahiyya ai mun iso ko.

Baki na dana wangale ina kallo na rufe Nace toh na sauko cikin ladabi da sanyin jiki na iso gare ta

 Dan tafiya kadan mukayi zuwa wani shashi, A hannun wata mata sanye da kayan aiki ta damka ni sai aka kaini wani waje
Aka bude min wata daki na shiga nikadai.

Juye juye nake yi ina tunani iri iri Anan Har bacci ya dauke ni ban sake ganin begahm ba!
#followSurayyahms

SHARE AND SHARE UR VIEWS
#SURAYYAHMS

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button