Allon Sihiri Book 4HAUSA NOVEL

Allon Sihiri Book 4

LOKACIN da Yarima Lubainu ya gama aiyana
haka a
zuciyarsa sai ya daga kai ya dubi Aljana Badi’atul
Sarira yace,yake wannan ma’abociyar kyau da
siffa ta
ban al’ajabi,kiyi sani cewa hakika kin zo mini da
babban al’amaro wanda bazan iya yin saurin
yanke
hukunci a kansa ba,saboda haka ina so ki bani
lokaci zuwa gobe da safe nayi tunani,sannan na
yanke shawara bisa abinda nake ganin zai
fissheni.Koda jin wannan batu sai Aljana
Badi’atul
Sarira taja dogon numfashi cikin alamun takaici
ta
dubi Yarima Lubainu tace,kaiconka ya kai
wannan
dan sarki,kayi sani cewa tabbas saikayi babbar
nadama idan kaki amfani da wannan dama dana
baka yanzu,domin kuwa har abada bukatarka
bazata
taba biya ba.Ina mai tabbatar maka da cewa
Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu
yaudararka zasuyi su gudu da wannan ALLON
SIHIRI,Shi kuwa wannan Bakon Jarumi indai ka yi
kuskuren karbar ADDININSA to har abada bazaka
warke ba daga wannan lalura taka,saidai ka
rungumi
kaddara.Lokacin da Aljana Badia’atul Sarira tazo
nan
a zancenta sai hankalin Yarima Lubainu ya sake
dugunzuma fiye da koyaushe.Nanfa ya kama
duru
duru ya rasa abinda zaiyi,kawai sai ya dubi
Badi’atul
Sarira yace,kiyi hakuri ni bana aiki da
gaggawa,dole
ne ki bari zuwa gobe da safe.Nayi miki alkawarin
zan dawo gareki da duku dukun safiya kafin
sauran
abokan tafiya su fito domin na sanar dake
hukuncin
dana yanke.Yarima Lubainu na gama fadin hakan
sai
ya juya da nufin ya fice daga cikin lambun,amma
sai
Badi’atul Sarira ta kira sunansa ya waigo da
sauri
suka dubi juna a lokacin dayaga hawaye na
cigaba
da tsartuwa akan kumatunta.Badi’atul Sarira ta
budi
baki tace,shikke na tunda ka kasa yanke hukunci
yanzu,ina son kayi min alkawarin cewa bazaka
sanar
da abokan tafiyarka labarina ba koda kuwa ka
yanke
hukuncin bazaka kwanceni ba daga cikin wannan
dauri daka riskeni a ciki?Sa’adda Yarima Lubainu
yaji wannan batu sai ya sake yin shiru yayi dan
guntun tunani sannan yace shike nan babu
matsala
nayi alkawarin zan rufe sirrinki.Yana gama fadin
hakan ya juya ya fice daga cikin lambun ya nufi
wani
dakin dabam ya fada cikinsa.Yana shiga yaga
ashe
falo ne guda daya,wato falle daya babu dakin
barci a
cikinsa,kuma babu komai a cikin falon face
shimfida
ta wani jan kilishi da kuma manyan dogayen
kujeru
masu taushi guda biyu.A tsakiyar kujerun kuma
an
ajiye wani farin tebur na azurfa.Koda ganin
wannan
tsari sai Yarima Lubainu ya aiyana a cikin ransa
cewa”duk yadda akayi wannan daki ne inda Boka
Darbusa ke Hutawa”.Take Yarima Lubainu ya tafi
izuwa kan daya daga cikin kujerun ya
kwanta.Kwanciyarsa keda wuya sai barci mai
karfi
ya saceshi saboda tsananin gajiya da tsamin jiki
sakamakon gumurzun da suka sha.Wannan shine
abinda ya garu gasu Yarima Lubainu bayan sun
sami nasarar dauko ALLON SIHIRI a gidan Boka
Darbusa.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
AMMA abinda basu sani ba shine,karbar wannan
ALLON SIHIRI na Boka Darbusa daidai yake da
ALLURA TA TONO GARMA!Domin duk halin da
suke
ciki Boka Darbusa ya gani a cikin MADUBIN
TSAFINSA a cikin wani kogon dutse dake wani
bangare dabam na wannan daji da suke
ciki.Shidai
wannan kogon dutse babu yadda za’ayi a gane
cewa
akwai mutum a cikinsa,saboda dutse ne
lailayayye
kuma fafaffe mai siffar kwai,amma sai Boka
Darbusa
yasa Aljanu suka fafe cikinsa suka gina masa
dakuna a ciki wadanda aka shiryawa kayan kawa
a
cikinsu tamkar aljannar duniya.A cikin wannan
gida
akwai hadima sama da guda dubu na jinsin
mutane
da aljanu,kuma suna rayuwa a cikinsa tamkar ba
a
cikin dutse suke ba saboda tsananin karfin sihirin
tsafi irin na Boka Darbusa.Bayan Boka Darbusa
yaga
yadda Bakon Jarumi ya sami nasarar tarwatsa
wannan bakaken aljanu daya turo su dauko
ALLON
SIHIRI sai ya takarkare ya bushe da dariyar
mugunta
yayita kyakyatawa kamar bazai daina
ba.Al’amarin
dayai matukar baiwa babban wazirinsa mamaki
kenan wanda ake kira da suna YAUHAN.Ya
dubeshi
a cikin alamun damuwa yace,haba ya shugabana
yaya kake ta faman yin dariya haka alhalin
makiyanmu ne suke samun galaba akanmu?Shin
ka
manta ne cewa sun koremu daga cikin ainihin
fadarmu kuma sun rabamu da Allonmu na Sihiri?
Koda jin wannan tambaya sai Boka Darbusa yayi
murmushi mai nuna jin kai gami da izza yace,ai
duk
wannan nasara dasu Bakon Jarumi suka samu ta
banza ce domin yanzu aka fara wannan mugun
wasa.Ka sani cewa ina da tarkuna guda arba’in
da
zan dana musu a cikin hanyoyinsu wadanda basu
isa su shallakesu ba har su iso KOGIN BAHAR
IMFAL ba tare da sun hallaka ba gaba
dayansu.Abinda ya bakanta mini rai a yanzu
shine
Yarima Lubainu ya san cewa shi dasu Akisatul
Sauwara bazasu iya karanta dalasiman tsafin
dake
jikin Allon Sihirin ba,Badi’atul Sarira ce kawai
zata
iya.To amma abin tambaya game da Yarima
Lubainu
a yanzu shine,shin zai iya taimakon Badi’atul
Sarira
har ya kwanceta,kuma idan ya taimaketan itama
zata
taimakeshi ne bazata ci amanarsa ba?Koda jin
wadannan tambayoyi sai hankalin Waziri Yauhan
ya
dugunzuma ainun ya dubi Boka Darbusa cikin
alamun damuwa yace,ya shugabana yanzu yaya
zamuyi kenan?Tabbas idan Yarima Lubainu da
Badi’atul Sarira suka hada kai suka taimaki
junansu
bada yaudara ko cin amana ba tamu ta
kare.Koda
jin wannan batu sai Boka Darbusa ya kyalkyale
da
dariya sannan ya daga kafadar waziri Yauhan
yace,ai
abinda ba zai taba yiyuwa bane Badi’atul Sarira
da
Yarima Lubainu su hada kai ba tare da dayansu
ya
yaudari dayan ba.Shin ka manta cewa dukkan
wani
MATSAFI mayaudari ne,kuma makaryaci?Ka zuba
ido
kawai kasha kallo kawai,zakaga yadda zata
wakana a
tsakaninsu.Shi kansa wannan
Bakon Jarumi sai yayi nadamar kulla alaka dasu
Sarauniya Akisatul Sauwara domin yaudararsa
zasuyi a karshe ba zasu taba karbar wannan
bakon
Addini nasa ba.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
A CAN BIRNIN ZAMRUL kuwa tun daga ranar da
Yarima Lubainu ya bar kasar domin tafiya neman
maganin lalurar da Yarima Mangul ya saka masa
sai
Amarya Yazarina ta kasance kullum cikin kuka da
bakin ciki dare da rana,har ya zamana cewa ta
fara
shiga wani mugun hali na rashin lafiya
sakamakon
yawan tunani da rashin cin isasshen
abinci.Al’amarin dayai matukar dugunzuma
hankalin
Sarki Sailur kenan da kuma mahaifinta Attajiri
Abu
Yazarina suka rasa yadda zasu bullowa al’amarin
saboda babu irin matakan da basu dauka ba
wajen
ganin ta daina kukan da bakin ciki gami da
yawan
tunani amma abun ya gagara.Lokacin da Tura
takai
Bango ya zamana cewa rashin lafiyar Yazarina
tayi
tsamarin da takai ga kwanciya sai likitan sarki
Sailur
ya bashi shawarar lallai a hanzarta yiwa Yazarina
maganin abinda yake damunta,idan ba haka ba
kuwa za’a iya rasa rayuwarta ma gaba
daya.Koda jin
wannan batu sai hankalin sarki sailur ya
tashi,take
ya tura aka kirawo Attajiri Abul Yazarina suka
kadaita
a cikin turakarsa.Sarki Sailur ya dubi Abul
Yazarina
cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai
abokina
na sani cewa a duniya kaf babu abinda kakeso
sama
da wannan ‘ya taka Yazarina wato matar ‘dana
Yarima Lubainu.Kuma nayi imamin kasan dukkan
wani hali da yanayi da take ciki dangane da
rashin
lafiyarta,to ka sani cewa a yau abin yayi tsamari
fiye
da koyaushe wanda sanadin hakan ne ma yasaka
likitana ya tabbatar mini da cewa idan har ba’a
sadata da mijinta ba da gaggawa wannan ciwo
nata
zai iya zama sanadin ajalinta.Koda jin wannan
batu
sai nan take idanun attajiri Abul Yazarina suka
ciko
da kwallah.Sarki Sailur ya cigaba da cewa,nidai
yanzu na kirawoka ne domin mu yanke shawara
bisa abinda nake gani zai kawo karshen wannan
matsala.Ka sani cewa ni kaina ina cikin mugun
tashin hankali tun daga ranar da dana Yarima
Lubainu yasa kafarsa yabar garin nan saboda
bani
da tabbacin cewa zai sami nasarar samo abinda
ya
fita nema ba tare daya rasa rayuwarsa
ba.Sannan
kuma idan har ya dawo ya iske Yazarina ta mutu
zai
iya kashe kansa koya susuce yadda bazai iya
gadar
karagata ba,yanzu menene abinda kake ganin ya
kamata muyi domin ceton rayuwar wadannan
‘ya’ya
namu.Sa’adda sarki Sailur yazo nan a zancensa
sai
Attajiri Abu Yazarina ya kawo gwauron numfashi
ya
ajiye kuma yayi shiru yana tunani har izuwa
tsawon
yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya
dubi
sarki Sailur yace yakai abokina kayi sani cewa
hanya
daya ce damu wacce zamu iya bi mu magance
wannan matsala.Dole ne mu hakura da zaman
‘yata
anan kasar mu hadata da amintattun dakarunmu
su
tafi neman Yarima Lubainu.Ina mai tabbatar
maka
da cewa ko a yanzu muka yiwa Yazarina bushara
da
hakan take zata sami lafiyar jikinta ta mike
tsaye.Yayin da sarki Sailur yai wannan shawara
sai
ya gyada kai cikin alamun murna yana
murmushi,sannan can kuma sai ya hade rai ya
dubi
Abu Yazarina cikin alamun matukar damuwa
yace,na
yarda da wannan shawara taka,amma fa kasani
cewa
akwai mugun hadari a cikinta.Hadari na farko
shine
zamu iya baiwa Yazarina cikakkiyar kariya ne
kadai
idan tana cikin wannan birni namu,amma idan
har
tasa kafarta ta fita koda mun hadata da dukkan
dakarun yakin kasar nan ba zasu iya kareta daga
harin mai son ta ba,wato YARIMA
MANGUL.Saidai
idan baisan cewa ta fito ba domin kuwa dole ya
tura
a satota a kaita gareshi.Hadari na biyu shine
wannan tafiya da zatayi izuwa inda Yarima
Lubainu
ya nufa tafi komai hadari domin takadiran
mutane da
aljanu da matsafa suka kwallafa ransu akan
wannan
ALLONSIHIRI kuma suna da yawa,kuma zasu iya
kawar da duk wanda ya shigo cikin al’amarin.Bisa
wannan dalili da hujjoji kaga kenan ‘yata zata iya
rasa rayuwarta tun kafin ma ta sadu da masoyin
nata Yarima Lubainu.Lokacin da attajiri Abul
Yazarina yazo nan a zancensa sai Sarki Sailur
yayi
ajiyar numfashi yace,tabbas duk abinda ka fada
gaskiya ne amma kuma akwai wani hanzari akan
haka.Da farko dai inaso ka sani cewa zamu iya
fitar
da ‘yarka daga cikin garin nan a sirrance ba tare
da
kowa ya sani ba bare har labarin hakan ya kai
izuwa
kunnen Yarima Mangul.Kuma koda ace ma yaji
din
kuma ya sami nasarar saceta ai garinsu zai
kaita,kasan kuwa indai Sarki ALKAS na
raye,bazai
taba barin shi ya aureta ba bisa dole,kuma zai
karbeta ne ya dawo da ita garemu.Dangane da
batun hadarin dake cikin tafiyar zatayi kuwa,ina
son
na tambayeka.Shin da zamanta a gabanmu cikin
mayuwacin halin rashin lafiyar da zata iya zama
sanadin ajalinta a ko yaushe da kuma tafiyarta
cikin
koshin lafiya bisa burin saduwa da masoyinta
wanne
ne yafi mana sauki?Koda jin wanna batu sai
Attajiri
Abul Yazarina ya sunkui da kansa kas yayi shiru
yana tunani sannan ya dago kai ya dubi sarki
Sailur
yace,hakika shawararka itace mafi kyau,don haka
inason ka zabo BABBAN JARUMI daga cikin
mayakanka wanda ka aminta dashi ainun ka
hadashi
da wadannan AMINTATTUN DAKARUNKA suyiwa
‘yata rakiya a cikin wannan tafiya.Amma abinda
danake so dakai shine,dasu da ita zasuyi bad-da-
kama ne ma’ana suyi shiga kawai irin ta FATAKE
su
fice daga cikin garin nan a sirrance ba tare da
wani
ya shaidasu ba.Koda jin wannan batu sai farinciki
ya
lullibe sarki Sailur yace,nima na karbi wannan
shawara dakazo da ita,kuma na umarceka daka
tafi
izuwa bangaren da yarka take a cikin wannan
gidan
sarauta nawa kayi mata wannan kyakyawan
ALBISHIR da duk wani abu da muka shirya
yanzu.Kuma ka gaya mata cewa a yau dinnan
zan
kammala
dukkan wani shirye shirye na wannan tafiya
tasu,kuma a tsakiyar dare zasu fita daga cikin
garin
nan.Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube
Attajiri Abu Yazarina ya zube lasa a gaba sarki
Sailur ya kama godiya.Koda ganin haka sai Sarki
Sailur yayi sauri ya sunkuya ya kama kafadunsa
ya
tasheshi tsaye,ya sallameshi ya tafi izuwa
bangaren
da turakar Yazarina take.Fitar Attajiri Abul
Yazarina
keda wuya daga cikin turarkar sarki Sailur ya nufi
cikin gidan Sarautar bangaren ‘yarsa Yazarina,sai
sarki Sailur ya tura aka kirawo masa mataimakin
sarkin yakin kasar wanda ake kira da suna
BARDE
RUHAISU.Barde Ruhaisu ya kasance saurayi
kyakyawa dan kimanin shekaru ashirin da
takwas,amma kuma GWARZON JARUMI NE mai
TARWATSA MAZA a FILIN DAGA.Sau bakwai
Barde
Ruhaisu yana jagorantar rundunar yaki a birnin
Zamrul ana samin nasara na tare da anyi wata
mummunar asara ba ta rayukan DAKARUN
YAKI.Allah ya horewa Ruhaisu baiwar sanin YAKI
da
TUGGUNSA kuma yana da matukar TUNANI mai
kyau
gami da HANGEN NESA.Duk da cewa sarkin
yakin
kasar yafi barde Ruhaisu KARFIN DAMTSE da iya
yaki da kuma kwarewa akan sanin tuggun yaki
amma sarki sailur yafi aminta da Barde Ruhaisu
dari
bisa dari saboda ya jarraba amanarsa ya gani.Shi
kuwa sarkin yaki mutum ne mai tsananin son
abin
duniya gami da MULKI,don haka sarki Sailur yana
tsoron cewa wata rana zai iya cin amanarsa don
cika
burin rayuwarsa.Bisa wannan dalili ne sarki Sailur
yake shirya komai nasa na sirri da Barde
Ruhaisu,shi kuwa sarkin yaki sai ya bar masa
abubuwan da basa bukatar sirri na cigaban kasa
da
kuma kare kasar daga yan hari ko ABOKAN
GABA.Sarki Sailur yana zaune a cikin falon
turakarsa
yayi tagumi yana tunani da nazarin abinda ke
gabansa,sai ga Barde Ruhaisu ya shigo.Tun daga
nesa kadan Barde Ruhaisu ya cire takalminsa
saboda biyayya,yana kara matsowa kusa da sarki
Sailur sai ya zube kasa wanwar ya kwashi
gaisuwa.Cikin hanzari sarki Sailur ya mike daga
kan
kujerar dayake zaune ya kama kafadunsa ya
tasheshi tsaye kuma ya rike hannunsa yajashi
izuwa
kan kujerar da yake zaune suka zauna tare.Sarki
Sailur ya gyara zama ya dubi Barde Ruhaisu cikin
nutsuwa yace,yakai JARUMIN JARUMAI kuma
BABBAR DIRKA ta birnin Zamrul,ka sani cewa
ban
kirawoka nan ba sai domin na baka wani
gagarumin
aiki mai mugun hadari wanda nakeson ka gabatar
dashi a cikin sirri.Kafin na sanar dakai yanayin
wannan aiki inason nayi maka wadansu
tambayoyi
guda biyu.ALLON SIHIRI
Littafi na Hudu (4)
Part B
Kafin na sanar dakai yanayin wannan aiki inason
nayi maka wadansu tambayoyi guda
biyu.Tambaya
ta farko itace shin zaka iya sadaukar da
rayuwarka
don ceton ta wanda nake kauna fiye da komai a
duniya?Koda jin wannan tambaya sai nan take
idanun Barde Ruhaisu suka ciko da kwalla ya
dubi
Sarki Sailur yace tayaya zan kasa fansar da raina
ga
wanda ya raineni ya rikeni tamkar dan cikinsa
alhalin
na kasance tsintaccen bawa da baisan iyayensa
ba
kuma bai san asalinsa ba?Koda jin wannan batu
sai
shima Sarki Sailur yaji hawaye ya subuto masa
amma sai yai sauri ya sunkui da kansa kas
yace,yakai Barde Ruhaisu shin zaka iya rabuwa
da
amaryarka wacce ke dauke da juna biyu na
tsawon
wata takwas tana shirin haife maka ‘da ko ‘ya
don
zuwa cika aikina alhalin ganin ‘danka ko ‘yarka a
yanzu shine babban burinka a rayuwa?Da jin
wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Barde
Ruhaisu yace,ya shugabana kasani cewa dani da
duk
abinda na mallaka zan iya bayar dashi FANSA
akan
halaccin da kayi mini a rayuwa,kuma a kaso dari
ban
saka maka da kaso goma ba.Koda jin wannan
batu
sai sarki Sailur ya rungume Barde Ruhaisu duk su
biyun suka fashe da kuka.Tsakanin Sarki Sailur
da
Barde Ruhaisu akwai tsananin kauna da shakuwa
domin kafin Allah ya baiwa Matar Sarki Sailur
haihuwar Yarima Lubainu saida suka shekara
goma
sha shida da aure ko batan wata bata bata
yiba.A
wannan lokaci babu irin kokarin da Sarki Sailur
da
matarsa basuyi ba akan su sami haihuwa har
saida
suka hakura suka rungumi kaddara.Wata rana
sarki
Sailur ya fita wani gagarumin yaki a wata kasa
da
ake kira DARNIS,wadanda tun iyaye da kakanni
akeyin mummunar gaba a tsakanin kasashen
biyu,sai Allah ya basu nasara suka kashe gaba
dayan dakarun yakin birnin Darnis,kuma suka
balle
kofar birnin suka cigaba da kashe dukkan
mazajen
garin manya da kanana banda yan kasa da
shekara
goma saida ya zamana cewa sun gama da
dukkan
wani namiji mai karfi a jika wanda zai iya tabuka
wani abin arziki.Ba komai ne yasa su sarki Sailur
sukayi wannan rashin imani ba face akwai
lokacin da
gaba daya mazajen garin suka kai musu harin
sumame suka kashe sama da mutane miliyan
uku,da kyar da sidin goshi aka koresu daga cikin
birnin Zamrul bayan sunyi mummunar barna sun
kama bayi kuma sun kwashe dukiya mai yawan
gaske sun kone kusan rabin birnin.Da gaiya Su
Sarki Sailur su kayi ta ragargazarsu baji ba
gani,kuma ba sassauci sannan suka yi ta kama
matayensu a matsayin bayi,yara da tsofaffi ne
kadai
suka kai labari.Lokacin da Sarki Sailur ya shiga
cikin
gidan sarautar birnin Darnis ya sami nasarar
kashe
sarkinsu,ya kama matayensa a matsayin bayi da
‘ya’yansa kanana saiya kunna kai izuwa cikin
turakarsa.Yana shiga cikin turakar ne ya iske
wani
yaro dan kimanin shekaru goma kwance a kas an
dora masa wani katon dutse a ciki yana ta
numfarfashi kamar ransa zai fita.Koda ganin
wannan
yaro a cikin wannan halo sai Sarki Sailur ya ruga
da
gudu izuwa ga yaron yai sauri ya dauke dutsen
daga
kan cikin yaron sannan ya tasheshi zaune.Koda
ya
kalli fuskar yaron yaga yadda lebensa ya bushe
saboda tsabar kishirwa da kuma yadda ya
galabaita. ainun sai ya kamu da tsananin tausayinsa.Nan
take
yai sauri yaje ya nemo ruwa ya baiwa yaron
yasha.Saida yaron ya dawo cikin hayyacinsa
sannan
sarki Sailur ya dubeshi cikin nutsuwa yace,yakai
wannan yaro waye yayi maka wannan muguwar
azaba haka yake neman hallaka ka?Koda jin
wannan
tambaya sai yaron ya budi baki da kyar
yace,sarki
ne yayi mini wannan azaba saboda bani da lafiya
na
kasa aiwatar da aikin dana sabayi a kullum.Cikin
mamaki sarki Sailur ya sake duban yaron
yace,aikin
ne kakeyi masa na bauta?Yaron yace nine mai
wanke masa kwanukan abinci da kofuna.Sarki
Sailur
ya girgiza kai yace,shin kai haifaffen nan garin
ne?
Yaron ya girgiza kai yace NI BAWA ne bansan
ASALINA ba,bansan IYAYENA ba,kawai na taso
ne
na tsinci kaina a cikin wannan gidan sarauta tun
banyi wayo haka ba ina aikin bauta.Koda jin
wannan
batu sai sarki Sailur yaji ya kamu da tsananin
tausayin yaron fiye da koyaushe ya dafa
kafadarsa
yace mene ne sunanka?Yaeon yace Sunana
RUHAISU.Cikin murna da murmushi sarki Sailur
ya
dubi Ruhaisu kayi sani cewa daga yau ka zama
dana,kuma nayi maka alkawarin cewar zan rikeka
tamkar dan dana haifa a cikina,kuma zan duba
abinda kafi cancanta dashi a rayuwa na doraka a
kansa.Koda Yaron Ruhaisu yaji wannan batu sai
fuskarsa ta fadada da murmushi ya kamu da
tsananin farin ciki ya dubi Sailur yace,wane ne
kai,kuma menene dalilin da yasa kukazo garin
nan
kuka afka mana da yaki?Shin kun kashe sarki ne
ko
kuwa kun kamashi a raye.Koda jin wannan
tambaya
sai sarki Sailur yayi murmushi yace Sunana
SARKI
SAILUR nai mulkin BIRNIN ZAMRUL.Ya kai
Ruhaisu
kayi sani cewa tsakanin kasata da wannan birni
na
azzalumin sarkinku akwai TSOHUWAR GABA tun
iyaye da kakanni,kuma kimanin shekaru uku baya
sarkinka da mayankansa sunje birnina sunyi mini
mummunar barna shine mu ma yanzu mukazo
mukayi RAMUWAR GAYYA.Tuni sarkinka ya dade
da
shekawa BARZAHU.Daga yau na yantaka kashi
daga
matsayin bawa ka zama cikakken da kuma dan
sarki
ba wai talakan gari ba.Koda gama fadin hakan
sai
sarki Sailur ya kama hannun yaro Ruhaisu yajashi
suka fice daga cikin turakar.Ai kuwa suna fitowa
kofar turakar ne yaro Ruhaisu yayi tuntube da
gawar
azzalumin sarkinsa.Kawai saiya tofawa gawar
yawu
yace,tur dakai azzalumi,azaba ninkin wadda ka
yimini sau dubu ta tabbata a gareka a cikin
kabarinka.Koda jin wannan batu sai sarki sailur
ya
fahimci cewar tabbas yaro Ruhaisu yasha bakar
wahala ta gaske a hannun wannan sarki.
Tun daga wannan rana kasar Darnis ta dawo
karkashin mulkin birnin Zamrul,aka mayar da ita
bbabar jaha kuma babbar cibiya ta kasuwanci.
¤¤¤
¤¤¤ ¤¤¤
LOKACIN da Sarki Sailur yazo da yaro Ruhaisu
gida
sai ya tara gaba dayan yan majalisarsa da
fadawansa ya gabatar da yaro Ruhaisu a garesu
kuma yace dasu daga yau sunan wannan yaro
Yarima Ruhaisu.Bawa ne amma na yantashi na
maishe dashi tamkar dan cikina.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya turnuke kowa fadawa suka
kama
kace nace.Wasu suce yama za’ayi sarki ya dauko
bawan da bashi da asali yace ya maishe dashi
dansa,harma ya kirashi a matsayin yarima mai
jiran
gado!Au wannan abin kunyane abin gori a gareshi
dama masarauatar birnin gaba daya!!!Wasu kuwa
sai
suka rinka cewa ai bazata sabi ba BINDIGA A
RUWA
a kawo bare wanda ba an kasa ba ace nan gaba
shine zai mulkesu.Koda sarki Sailur yaji irin
surutun
da yan majalisarsu da fadawansa sukeyi sai
ransa ya
baci,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata
kone bai
san sa’adda ya mike tsaye ba zumbur daga kan
KARAGAR MULKINsa ya daka kakkafar TSAWA
wadda
tasa hantar cikin kowa ta kada saboda tsananin
tsoronsa da akeji.Nan ake fadar tayi tsit kowa ya
sunkui da kansa kasa kamar ruwa yaci su.A
sannan
ne sarki Sailur yace,nine sarki a wannan birni na
Zamrul,babu wani mai matsayin dayafini don
haka
idan har na gabatar da HUKUNCI babu wanda ya
isa
ya sauya mini shi.Wannan Yaro Ruhaisu shine
Yarima na,wanda duk ya kara magana akan haka
da
hannuna zan cisge masa kansa!!!Koda jin wannan
batu sai gaba dayan mutanen dake cikin fadar
suka
sake shiga taitayinsu aka rasa wanda ma zai iya
daga kansa sama ya dubi sarki Sailur.Koda Yaro
Ruhaisu yaga abinda ya faru tsakanin sarki Sailur
da
mutanensa sai ya fashe da kuka ya durkusa bisa
gwiwoyinsa a gaban sarki saiur.Al’marin daya
baiwa
kowa mamaki kenan a fadar aka kurawa sarki
Sailur
da Yaro Ruhaisu idanu.Shi kuwa sarki sailur sai
hankalinsa ya DUGUNZUMA shima ya durkusa a
gaban Ruhaisu ya kama kafadarsa ya rike kuma
ya
dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da
fargaba
ya ce yakai dana ina dalilin wannan kuka naka?
Yaro
Ruhaisu ya dubi sarki Sailur cikin nutsuwa
yace,yakai wannan sarki mai daraja,kayi sani
cewa
babu wani jin dadi ko kwanciyar hankali ga
kowanne
sarki komai arzikinsa da daukakarsa face ya sami
soyayya da kaunarsa a cikin zukatan jama’arsa
sannan ya cika sarki mai kima da daraja,domin a
sannan ne jama’ar tasa zasu iya siyar da
rayukansu
domin tsare lafiyarsa da mutuncinsa.Ya kai
wannan
sarki mai daraja,mai adalci,bana son ka rasa
wannan
babbar dama saboda ni don haka na roke ka don
darajar karagarka daka janye wannan matsayi
daka
bani na Yarimanka,ni kuma nayi alkawarin cewar
zan
cigaba da nuna maka SO da KAUNA kamar yadda
kowanne da ke nunawa ubansa.Koda Yaro
Ruhaisu
yazo nan a zancensa sai gaba dayan jama’ar
dake
fadar suka cika da tsananin mamakin hankalinsa
da
basirarsa ta iya magana da sanin yakamata da
kuma
hangen nesa.Kawai sai jama’a suka kama yiwa
yaro
Ruhaisu tafi.Al’amarin daya aurewa sarki Sailur
kai
kenan,kuma yaji ya kara kamuwa da tsananin son
yaro Ruhaisu fiye da koyaushe a rayuwarsa,don
haka
sai ya tashe shi tsaye ya rungumeshi yana mai
cewa
tabbas ka cika da na gari abin alfahari.Lallai na
yarda da wanan shawara taka kuma zanyi aiki da
ita.Koda jama’a suka ji haka sai suka rude da
shewa,suka kama yiwa sarki Sailur jinjina da
kirari
suna masu nuna soyayyarsu a gareshi.Tun daga
wannan rana Ruhaisu ya tunawa sarki Sailur
cewa
babu abinda yakeso a rayuwarsa sama da ya
koyi
YAKI.Ai kuwa ba tare da wata gardamar komai
ba
sarki Sailur ya shiga koya masa yaki da kansa,ya
zamana cewa a kullum sarki sailur yana shafe
kimanin sa’a guda yana koyawa Ruhaisu yaki.Da
safe suyi sa’a biyu,haka ma da rana da kuma
daddare.A cikin kwanaki goma sha hudu Kacal
Ruhaisu ya iya sarrafa takobi ainun,kuma ya iya
kare
dukkan irin harin da sarki Sailur ke kawo
masa.Koda aka shiga sati na uku kuwa sai gashi
yana iya maidawa sarki sailur martanin kai
hari,har
ma akwai lokacin da saura kiris ya yiwa sarki
Sailur
rauni a lokacin daya kawo masa wani wawan
sara
aka,ya matsa baya cikin zafin nama,amma duk
da
haka sai da kaifin takobin tasa ta zabtare wani
bangare kadan na rawaninsa.Shi kansa sarki
sailur
bai san sa’adda ya kama yiwa yiwa Yaro Ruhaisu
tafi ba.Daga wannan rana ne sarki Sailur yakai
Ruhaisu cikin manyan dakarun yakin kasar ya
cigaba
da daukar HORON YAKI a cikinsu.Abi dai kamar
wasa sai gashi Ruhaisu yana iya jure duk irin
wahalar da manya ke jurewa a matsayinsa na
yaro
karami dan shekara goma.Ashe wannan juriya
tasa
ta samo asalo ne tun daga azabar da sarkin
birnin
Darmis ya rinka yi amsa shi kuma yana
shanyeta.Kai
saida takai cewa barde Ruhaisu yana iya yin yaki
da
karti hudu yana yaro amma duk sai ya kaisu
kasa.Lokacin daya cika shekara goma sha
takwas a
duniya kuwa sai gashi shi kadai yana iya
tarwatsa
mutum arba’in.A wannan shekarar ne aka jarraba
iya
yakin Ruhaisu inda aka shirya wata gagarumar
GASA
ta JARUMAI akan akarfin damtsensu da iya
Yakinsu.Jaruman gasar su dari da goma sha
hudu
ne,amma RUHAISU ne ya karbi KAMBUN
GASAR.Daga wannan lokaci ne sarki sarki ya
sake
jan barde Ruhaisu a jikinsa ainun ya zamana
cewa
duk wani abu da zaiyi na sirri tare dashi
yakeyi.Al’amarin dayasa sarkin yaki ya fara
kyashi
da hassada dashi kenan,kuma ya tsaneshi
ainun,amma sai Ruhaisu ya zame masa
kadangaren
bakin Tulu.Babu irin tuggu da makircin da sarkin
yaki bai shiryawa Barde Ruhaisu ba amma sai
sarki
sailur ya rinka kareshi a boye ba tare da ya sani
ba.Kai sau tari ma akwai
mugayen tarkuna da Ruhaisu yake fadawa ya
kasa
fitar da kansa,amma sai yaga wani yazo tsulum
ya
ceceshi,kuma wanda ya ceceshin ya rufe
fuskarsa da
bakin rawani idanunsa kadai ake gani gaba dayan
kayan jikinsa ma bakake ne.Saida akayi hakan
kusan
sau hudu.Abinda ya faru a karo na hudun shine.
pls Like and comments
15 hrs · PublicALLON SIHIRI
Littafi na Hudu (4)
Part C
A BINDA YA Faru a karo na hudun shine,wata
rana
da magriba Ruhaisu ya dawo daga FARAUTA a
daji
kawai sai yaga wadansu dakarun sumame
kimanin
su arba’in sanye da jajayen tufafi sun dako tsalle
a
sama sun kewayeshi.Su duka sai suka zare
takubbansu suka ja tunga cikin shirin afka
masa.Tunda Barde Ruhaisu yazo duniya bai taba
ganin ZARATAN DAKARU masu kwarjini da kirar
SADAUKAI ba irin wadannan.Nan take jikinsa ya
bashi cewa yau fa ya gamu da gamonsa,amma
da
yake shima jarumi ne mai DAKAKKIYAR ZUCIYA
ko
kadan baiji tsoron yayi kokarin ceton kansa
ba.Abinda ya aiyana aransa shine ko ba komai
sai
yayi iya bakin kokarinsa yaga cewa bai mutu shi
kadai ba.A kalla yana son ya sami nasarar kashe
koda mutum goma ne daga cikin wadannan
zaratan
jarumai da suka kawo masa MAMAYAR
BAZATO.Lokacin da dakarun suka ga Ruhaisu ya
gyara tsayuwarsa yana dafe kufen takobinsa ba
tare
daya nuna alamun tsoro ba ko tunanin
guduwa,sai
su ma suka sha jinin jikinsu,suka fahimci cewa
lallai
shima JAN IDO ne,kuma zai iya yin barna kafin a
gama dashi.Hakan ne yasa dakarun basuyi saurin
afka masa ba suka tsaya daga baya baya suna
nazarinsa tukunna.Shi dai wannan wuri inda
DAKARUN SUMAMEN suka ritsa Ruhaisu wajen
gari
ne sosai a tsakiyar daji inda babu gida gaba ko
baya,kuma babu wani mahaluki dazai tsaya a
wajen
tsawon dakika goma batare daya firgita ba
saboda
waje ne mai yanayi na ban tsoro.Akwai dogayen
bishiyoyi masu duhuwoyi gami da manyan
tsaunika
wanda dole ne baza a rasa mugayen dabbobin
daji
ba akansu.Ko yaushe wajen tsit yake tamkar
babu
wata halitta mai rai a wajen,kai da gani kasan
cewa
ba za’a rasa mugayen MUTANEN BOYE ba a
wajen.Ana cikin wannan hali ne sai tsulum
dakarun
sumamen sukaga wani Badakaren a cikin shigar
bakaken kaya rike da takobi ya duro tsakiyarsu
daga
can sama daga kan wata doguwar bishiya ya
tsaya
daf da Ruhaisu suka hada baya alamar ce
Ruhaisu
ya kawowa dauki.Koda ganin haka sai shugaban
dakarun sumamen yabaiwa sauran yan uwansa
inkiya suka afkawa su Ruhaisu.Nanfa aka
ruguntsume da azababben masifaffen yaki mai
matukar tayar da hankali da muni.Ana fara yin
wannan gumurzu ne kowa ya san cewa KARO DA
KARO sai RAGO!Kamar yadda dakarun sumamen
suke da KARFIN DAMTSE da iya yaki,zafin nama
da
bakin naci,haka Ruhaisu ma da mai bakaken
kayan
nan suke dashi,don haka saida aka shafe sa’a
biyu
da rabi ana dauki ba dadi,in banda karar haduwar
takubba gami da sautin naushin jiki babu abinda
kunne yakeji.Gashi dai an kasa koda lakutar jikin
mutum daya a GUMURZUN bare a fitar masa da
JINI
mai yawa,amma kuma ana naushin juna yadda
yakamata kuma ana shanye naushin sai kace
jikin
kowa bana jini da tsoka bane.Duk wanda ka duba
saidai kaga hancinsa da bakinsa na yoyon
jini.Koda
shugaban sakarun sumamen yaga an bata
wannan
lokaci mai tsawo haka ba tare da sun sami wata
nasara ba saiya fusata ainun ya bayar da wata
inkiya.Take dakarun sumamen suka ja da baya su
duka alokaci guda suka zaro wadansu adduna
guda
dai dai wato ya zamana cewa kowannasu na rike
da
makamai biyu a jikinsa ga TAKOBI ga kuma
ADDA.Koda ganin haka sai wannan badakare mai
bakaken tufafi yai wuf ya zaro wadansu Wukake
guda
biyu a cikin jikinsa ya mikawa Ruhaisu guda ya
karba,suma suka dubi juna sukayi wata inkiya iri
daya.Koda Ruhaisu yaga sunyi inkiya iri daya shi
da
wannan badakare mai bakaken kaya sai
zuciyarsa ta
buga da karfi kuma tsoro ya shigeshi.Ba komai
ne
yasa masa wannan tsoro ba face ya gane cewa
ba
wani bane wannan badakare mai bakaken kaya
face
SARKI SAILUR.Take Ruhaisu ya tambayi kansa a
cikin zuciyarsa yace,saboda ne sarki yake siyar
da
rayuwarsa don ceton tawa rayuwar?Ai wannan ba
karamin ganganci bane a matsayinsa na sarki
yayi
haka kuma idan wani abu ya sameshi nima na
shiga
wani bala’in.Yana cikin wannan tunani ne
dakarun
sumamen suka sake afko musu aka sake
ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki a karo
na
biyu wanda yafi na farko tashin hankali da bala’i
domin wannan karon wani irin sabon salon yaki
dakarun sukazo dashi ya zamana cewa sun hada
da
tsalle tsalle da kwance kwance suna yawo a
saman
su Ruhaisu da kasansu suna kai musu hari ta ko
ina.Faruwar hakan keda wuya kuwa sai suka fara
ruda sarki Sailur da Ruhaisu nan take suka sami
nasarar yankar kowannansu sau uku uku,jini yai
tsartuwa daga jikinsu suka kurma ihu sakamakon
tsananin zafi da zogin da suka ji.Nan take jiri ya
kwashi Ruhaisu ya durkushe kasa yana mai cake
takobinsa cikin kasa don kare kansa daga
faduwa.Koda ganin haka sai shugaban dakarun
sumamen ya dako tsalle sama cikin shammace
da
zafin nama ya daga makaman nasa biyu sama da
nufin ya fille masa kai.Koda Sarki Sailur yaga
abinda
ke shirin afkuwa gashi yana yaki da sauran
dakarun
sumamen shi kadai ya hanasu kusantar Ruhaisu
sai
ya daka tsalle sama yayi wata irin katantanwa da
kafafunsa a tsakiya dakarun sumamen ya
tarwatsa
su kuma ya kare saran da shugaban dakarun
sumamen ya kawowa Ruhaisu a gadon
bayansa.Taka takobin da Addar suka datsa
bayan
sarki Sailur jini yai feshi a lokacin da sarki sailur
ya
kurma uban ihu kuma ya fadi kasa tim a
sume.Koda
Ruhaisu yaga abinda ya faru ga Sarki sai ya
kurma
ihun daya ninka na sarki Sailur sau goma kamar
MAHAUKACIN ZAKI ya faso gari.Take gaba
dayan
dakarun sumamen suka firgita suka ja da
baya.Shi
kuwa Ruhaisu zuciyarsa ce ta kekashe ga barin
jin
dukkan tsoro da kasala saboda tafarfasa data
kamayi kamar zata kone saboda fishi bisa ganin
halin da sarki ya shiga,kawai sai gani akayi
Ruhaisu
ya daka tsalle sama tamkar daga cikin BAKA aka
harboshi ya sare kan shugaban na
su kuma ya soka masa wuka a tsakiyar kirjinsa
ta
fullo ta gadon bayansa.Take gangar jikin
shugaban
dakarun sumamen ta sulale kasa matacciya.Shi
kansa Jarumi Ruhaisu yayi matukar mamakin
yadda
akayiyayi wannan gagarumar BAJINTA da
JARUMTAKA.Koda sauran dakarun sumamen
suka
ga yadda Ruhaisu yayi da abin dogaronsu,wato
shugaban nasu sai suka firgice suka zubar da
makamansu suka cika wandunansu da iska.Kafin
kace wani abu babu dayansu a kusa.A sannan ne
Ruhaisu ya fashe da kuka ya fara dinke raunikan
dake gadon bayansarki sailur cikin razana da
dimauta yana ta fama rusa kuka domin a lokacin
ma
gani yake kamar tuni sarki ya dade da
mutuwa.Bayan ya gama dinke masa raunikan ne
yaga har a sannan jini bai daina zuba daga cikin
raunikan,al’amarin daya dugunzuma hankalinsa
kenan ya ruga da gudu izuwa cikin daji ya samo
wadansu saiwoyin bishiyoyi yazo ya dakesu ya
shafe
raunin dasu.A sannan ne jinin ya daina zuba,har
izuwa wannan lokaci Ruhaisu bai daina kuka ba
saboda ko kadan babu alamar numfashi akan
kirjin
sarki Sailur,kuma babu inda yake motsi a
jikinsa.A
daidai wannan lokaci ne Ruhaisu ya fara sakar
zuci
wata zuciyar tace dashi menene amfanin
rayuwarka
a duniya tunda ka rasa wannan BABBAN MASOYI
wanda baka da kamarsa a duniya.Ai gwara kaima
ka
kashe kanka tunda idan ma ka dauki gawarsa ka
kaita cikin gari babu yadda za’ayi ka tsira daga
zargin cewa kaine ka kasheshi.Koda gama aiyana
hakan sai Ruhaisu ya sake fashewa da
matsanancin
kuka na bakin ciki har izuwa lokaci mai dan
tsawo.Daga can kuma saiya daga takobinsa
sama
da nufin ya cakata a cikinsa ya kashe
kansa.Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga
sarki
sailur yayi wuf ya taso zaune ya rike hannunsa
kuma
ya budi baki da kyar cikin matukar karfin hali
yace,dakai ka mutu gwara ni na mutu kai ka rayu
saboda indai ban samu haihuwa ba kai nakeso ka
gajeni.Har yau har gobe wannan shine babban
BURIN ZUCIYATA.Koda sarki Sailur yazo nan a
zancensa sai Ruhaisu ya rungumeshi cikin
tsananin
farin ciki bisa ganin cewa bai mutu ba.Kafin sarki
Sailur ya sake budar baki yace da Ruhaisu wani
abu
sai Ruhaisu yayi wuf ya goyashi a bayansa ya
falfala
da azababben gudu izuwa hanyar dazata kaisu
cikin
gari.Nanfa ya rinka yin wani irin gudu na ban
al’ajabi
yana gifta bishiyoyi tamkar giftawar tauraruwa
mai
wutsiya.Cikin kankanin lokaci suka iso cikin gari
suka karasa fada,tun a kofar gidan sarautar
Ruhaisu
ya kwallawa likitan sarki Sailur kira don haka
kafin
su karasa turakar sarki sailur tuni anje an kirawo
likitan ya karaso da gudu izuwa cikin
turakar.Nandai
Likitan ya shiga aikinsa ya baiwa sarki sailur
wadansu magunguna wajen kala uku yasha kuma
ya
shafa wani maganin akan rauninsa.Faruwar
hakan
keda wuya sai barci ya sace sarki.Saida sarki
Sailur
ya shafe sati uku a kwance yana jinyar wannan
rauni
na gadon bayansa sannan ya warke
sumul,tamkar
bai taba samun wani rauni ba ma.Sa’ar dayayi
itace
saran da akayi masa bai taba kashi ba,tsokar
nama
ce kawai ta dare.Wannan shine takaitaccen
tarihin
Barde Ruhaisu.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
BAYAN SARKI SAILUR da Barde Ruhaisu sun dan
jima a tsaye rungume da junansu suna kuka sai
sarki sailur ya janye jikinsa daga cikin na Ruhaisu
ya
dubeshi a nutse yace,yakai dana kayi sani cewa
ba
komai nake so kayi mini ba face ka yiwa
surukata
Yazarina rakiya izuwa tafiya neman mijinta
dan’uwanka Yarima Lubainu.Ka sani cewa tuni
mun
gama shirya komai ni da mahaifinta Abu Yazarina
saboda haka a cikin wannan dare nake so kayi
wannan tafiya kuma zan hada ka da wadansu
amintattun zakwakuran dakaru nawa kamar
mutum
dari kacal wadanda zasu taimaka maka.Ina son
kuyi
bad-da-kama a cikin daren yau zaku bar garin
nan
domin a samu cikakken sirri.Koda Sarki Sailur
yazo
nan a zancensa sai farinciki ya lullube barde
Ruhaisu ya dubi sarki sailur fuskarsa cike da
annuri
yace,yakai Abbana kayi sani cewa a iya tsawon
rayuwata ban taba jin farin ciki ba a raina irin na
yau
saboda yaune ranar farko daka taba neman wata
alfarma a wajena.Tun daga kuruciyata kawo
izuwa
girmana bantaba saka maka ba da abin alherin
daka
ke yi mini tsawon shekaru,amma yau gashi ka
bani
damar dazan iya kwatantawa.Na rantse da
darajar
kauna da soyayyar dake tsakaninmu dakai zan
sallama rayuwata don kare ta surukarka,kuma
duk
inda dan’uwa na Yarima Lubainu yake a cikin
duniya
sai na damka Yazarina a hannunsa cikin koshin
lafiya kuma a raye.Koda jin wannan batu sai farin
ciki ya sake baibaye sarki sailur ya rungume
barde
Ruhaisu a karo na biyu yace,ina alfahari dakai
yakai
yayan Lubainu,kuma nasan cewa saika cika
wannan
aiki dana baka bisa amana.Ni yanzu babbar
masifar
dazan fuskanta itace ta kewarka a yayin daka yi
wannan tafiya.Ka tuna cewa tun daga ranar dana
daukoka a gidan sarautar Birnin Darnis kawo
izuwa
yau bamu taba rabuwa daidai da rana daya
ba,yanzu
gashi zakayi wannan tafiya mai mugun hadari
wacce
bansan ranar dawowarka ba.Koda sarki sailur
yazo
nan a zancensa sai ya sake kankame barde
Ruhaisu
a kirjinsa ya fashe da matsanancin
kuka.Al’amarin
daya karya zuciyar barde Ruhaisu kenan,shima ya
fara yin sabon kukan.Tabbas irin son da sarki
Sailur
yake yiwa Barde Ruhaisu har yafi wanda yake
yiwa
Yarima Lubainu duk da ya san cewa barde
Ruhaisu
ba dansa bane na cikinsa,’da ne na TSUNTUWA
wanda ma baisan asalinsa ba.Tsananun tausayin
barde Ruhaisu da yakeyi be yasa yake kaunarsa
fiye
da Yarima Lubainu.Sarki Sailur bai taba fifitashi
ba
kan Ruhaisu,kuma kowanne taro sarki zai tura
wakilci bai taba tura Yarima Lubainu ba saidai ya
tura barde Ruhaisu.Kai saida takai cewa Yarima
Lubainu ya fara
nuna kishinsa a fili akan Barde Ruhaisu saboda
ganin yadda sarki ke fifitashi akansa.Daga ranar
da
sarki sailur ya baiwa Yarima Lubainu labarin
haduwarsu tun yana dan shekara goma kawo
izuwa
girmansa shike nan sai Yarima Lubainu ya
kaunaci
barde Ruhaisu fiye da yadda ma sarki ke
sonsa,kuma suka zamo manyan abokai yan’uwa
kuma aminan da basa son rabuwa.A ranar da
Yarima Lubainu zaiyi wannan tafiya saida suka
shafe
rabin sa’a cif a tsaye rungume da junansu suna
kuka na bakin cikin rabuwa,da kyar suka saki
juna
Yarima Lubainu ya tafi,domin a cikin zukatansu ji
suke kamar dama can sun kasance yan’uwan
juna
na jini.Bayan bardw Ruhaisu da sarki Sailur sun
dan
sake jimawa a kankame da juna sai Ruhaisu ya
janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna
yana mai share hawayensa yace,yakai Abbana
kayi
sani cewa akwai bukatar naje na kammala
dukkan
shirye shiryena yanzu tunda bani da isasshen
lokaci
kuma nayi bankwana da matata.Sarki sailur ya
gyada kai a lokacin da hawaye ya subuto masa
yace
wannan gaskiya ne,kuma ka nema mini gafara a
wajen surukata matar taka tunda na rabata dakai
a
lokacin datafi koyaushe kewarka.Na sani cewa
bata
da burin dayafi ta haihu kana nan ku raini abinda
kuka haifa tare domin babu takaicin dayafi na
rabuwa da IYAYE tun mutum yana karami.Gashi
kai
ka rabu da iyayenka a lokacin ma baka sansu
ba,amma na sani kuma naji a jikina cewa tarihi
bazai maimaita kansa akanka ba,lallai kai zaka
dawo
gida a raye cikin koshin lafiya tun kafin ‘danka ko
‘yarka tayi wayo.Koda jin haka sai fuskar Barde
Ruhaisu ta fadada da murmushi ya yiwa sarki
Sailur
godiya sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin
turakar ba tare daya yarda ya sake waigowa
ba.Take
Barde Ruhaisu ya nufi izuwa gidansa.
2 mins · PublicALLON SIHIRI
Littafi na Hudu (4)
Part D
DA ISAR BARDE RUHAISU gidansa sai ya iske
matarsa ZASMIN tsaye a falo dauke da tsohon
juna
biyu tana kai kawo cikin alamun damuwa.koda ta
hango shigowar Barde Ruhaisu sai ta taho
gareshi
fuskarsa cike da annuri suka rungume,amma
yayin
data janye jikinta daga nasa taga idanunsa sunyi
jajir alamar cewa yasha kuka sai zuciyarta ta
buga
da karfi ta dubeshi cikin alamun tsananin tashi
hankali tace,gaya min gaskiya yakai mijina yau
kuma menene ya faru a fada?Lallai ba ka taba
dawowa gida a cikin irin wannan yanayin ba.Shin
wani makusancinka ne ya mutu ko kuwa wani
abu
ne ya sami sarki?Tabbas yadda na sanka da
DAKAKKIYAR ZUCIYA in ba wadannan abubuwa
ba
babu abinda zai saka kuka.Koda jin wannan
tambaya
sai Barde Ruhaisu ya suri Zasmin ya dagata
sama
yana mai rungumeta a kirjinsa yayi juyi da ita don
haka bata san sa’adda ta kama kyalkyala dariya
ba.A hankali Ruhaisu yaje ya shimfide Zasmin
akan
gado ya kama wasa da gashin kanta suna kallon
juna cikin murmushi.A sannan ne ya kwashe
labarin
dukkan abinda ya faru tsakaninsa da sarki Sailur
ya
zayyane mata.Koda gama bata wannan labari sai
yaga ta kyalkyale da dariya,amma kuma hawaye
na
zuba a cikin idanunta.Al’amarin dayai matukar
bashi
mamaki kenan kuma ya kadu,cikin mamaki
yace,yake matata ina dalilin wannan dariya taki
gami
da kuka a lokaci guda.?Sa’adda Zasmin taji
wannan
tambaya sai ta nutsu ta dubeshi da kyau tace,ya
kai
mijina abin begena dare da rana,kayi sani cewa
ba
komai ne ya sakani wannan kuka ba face yau ne
ranar farko da zan fara rabuwa dakai tun daga
lokacin aurenmu.Alhinin rabuwar tamu ne kawai
ya
sakani kuka,amma ina ji a jikina cewa tabbas
zaka
dawo gareni.Abinda ya sani nake yin wannan
dariya
kuwa ba komai bane face tsananin tayaka
farincikin
samun damar dazaka iya sakawa sarki kadan
daga
cikin irin abubuwan alherin dayayi maka.Kash!In
badon ina dauke da wannan TSOHON CIKI ba da
lallai tare dani za’ayi wannan tafiya,sabida inason
na
haife maka danka a lokacin da kake cikin
GWAGWARMAYA ko shima dan naka ya sami
tabarraki irin naka.Koda Zasmin tazo nan a
jawabinta sai farin ciki ya lullube Ruhaisu ya
rungumeta ya kama sumbatarta yana sa mata
albarka.Nan take Zasmin ta mike tsaye da kanta
ta
fara debo kayan Ruhaisu tana zuba su cikin jakar
guzuri don kammala shirye shiryen
tafiya.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button