HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

2/17/22, 09:45 – Buhainat: Halin Girma

36

 

*******�

Cikin wani yanayi taji kamar bacci yana fuzgarta, ta sake
gyarawa sosai Ummimi ta matsa mata sosai ta

kwanta a bayan, nan take kuwa bacci
ya dauke ta. A tunanin Ummimi tsabar gajiya da wahala ce ta saka ta baccin, dan
tun safe suka fito kuma tana lura bata saka komai a cikin ta ba sai ruwa, ita
dai ta bata kudi taje cafeteria ta siya abinci taci, amma ita kuwa bata ci
komai ba, dole ne ko ba karatu kake ba, ka jigata balle. Tausayin ta taji,
musamman da ta gama fuskantar halin kirkin da, bama ita kadai ba duk ma’aikatan
gidan na murna da samun ta a matsayin uwargijiyar su, babu hantara balle
tsangwama, gaba dayan su son ta suke da gaske.

   Tafiya suke tayi babu alamun zasu tsaya, har duhu
ya fara mamaye sararin samaniya, kallon ta Ummimi tayi taga har lokacin bacci
take da gaske, shiru kake ji a motar babu wanda yake magana a cikin su, a
tunanin da za’a samu ko yar karamar hira ce tsakanin driver da na gaban amma
babu wani wanda yayi magana a ciki, jakar dake kusa da Iman din ce ta fadi
kasa, Ummimi ta sunkuya da nufin dauka, abinda ta hango a hannun shi ya saka
hantar cikin ta kadawa, a firgice ta dago tana dunkule jakar a hannun ta,
juyowa yayi ya dube ta, ya sake dago mata hannun nasa da kyau dan ta gani
sosai, bindigar ce kuwa, tsoro ne ya kamata,

“Idan kika sake kika bud’e bakin ki a wajen nan, sai na
fasa kanki da alburushi.”

Da sauri ta rufe bakin ta da hannun ta, juyawa yayi kan driver
yace

 

” Idan ka kai karshen titin zaka gangara haggu.”

 

Da ka ya amsa, daga gani a tsoroce yake, rashin sani ya hanasu
ganewa tun shigowar su motar. Kallon Iman take ganin da gaske bacci take, bacci
me nauyi da ya hanata jin duk abinda ya faru, mamaki ne ya kama Ummimi, dama ta
saba irin bacci haka ko kuma dai akwai matsala, da sauri ta dan taba ta, sai
taga ta motsa kad’an tamma kuma bata tashi ba, ajiyar zuciya ta sauke, hawayen
da take ta makale shi ya gangaro zuwa fuskarta, me yasa mutane suka lalace
haka? Labarin da suke ji a gidan radio yau shine ya faru dasu? Idan har masu
sarauta da masu hannu da shuni basu da tsaro toh waye kai kuwa talaka? Anya
rayuwar zata tafi a haka?

   Cikin tsananin fargaba take har suka karaso wani
gida, karami a cikin gungurmin jeji, babu gida gaba babu baya, ba zaka taba
tunanin halitta irin ta mutum zata rayu a wajen ba, tana jin yadda suka dinga
shiga kan tudu da kwari alamun sam hanyar bata mota bace, ko tace mota bata
taba bi ba. Murfin motar ya bud’e yana nunawa driver bindiga, suka fito a tare
ya zagayo wajen sa ya rik’e kugunsa. Fito yayi da bakin sa, sai ga wasu kartin
maza su biyu sun fito, tare da wata mace a bayan su, tafawa sukayi da daya daga
ciki sannan yace

 

“Kayi babban aiki, aikin da zai firgita ilahirin k’asar har
ma da ketare, tana ina?”

 

Bayan motar ya nuna masa, ya tafi zuwa wajen ya bud’e yana leka
ciki

 

“Baccin ne be sake ta ba har yanzu?”

 

“Eh!”

 

“Tasha ruwan kenan!” Yayi murmushi yana rufe kofar

 

“Tasha sanda ta shigo motar.”

 

“Kayi kokari sosai… Kudos!”

 

“Thank you sir.”

 

“This is a shame to the Nigerian Armies, The royalties,
government, gaba daya ma, duk sunyi failing, ta yaya kake tunanin mutane zasu
sake yarda dasu? Bayan sun damka hakkin kulawa rayuwar su garesu, sai ya zama
sun k’asa tsare kan su?”

 

Sai ya kwashe da dariya

 

” Yaron nan a bayan mu yazo, yaron nan ta dalilin sa na
rasa komai, ciki harda aikin da na kwallafa rai, saboda shine shafaffai da mai?
Saboda shi din dan gata ne, shiyasa aka fifita shi akan kowannen mu, me yafi
mu? Mulki?”

 

“Oga!”

 

” Haka ne mana!” Ya fad’a da karfi

 

“Haka ne. Kullum cikin favoring dinsa ake, kullum cikin
yabon sa ake, na kai mataki Babba amma yaron nan, ta dalilin sa komai ya baci,
ya kake tunanin zan iya hakura?”

 

“Kunsan shekarun da na dauka ina gina rayuwata har na kawo
wannan lokacin?”

 

“A ah.” Suka girgiza kai dukka

 

” Shekara goma sha daya, amma cikin sakan da be wuce goma
ba, ya kwace komai, khaki na, rank dina, mutunci na a idon duniya, na muzanta,
na zama abin gudu da k’yama.”

 

Duk sun yi shiru kowa na sauraren sa, shirun shima yayi dan
bashi da abin fad’a kuma

 

” Ku shigar dasu ciki, idan princess ta tashi a fad’a
min.”

 

Sai ya juya ciki ransa fari tas, ya tabbatar saura kiris bomb ya
tashi, bomb din da zai tarwatsa duk wani farin cikin Muhammad Ahmad Santuraki
da duk wani makusancin sa, shekara biyar kenan yana bibiyar sa, ya kuma samu
nasarar samun duk abinda ya samu a yanzu, wanda yake tabbatar da su kadai sun
isa su tarwatsa duk wani farin cikin sa. Matsala daya da ya samu, bashi kadai ne
yake son ganin bayan sa ba, nasa kawai yafi zafi ne, sai ya hada guiwa dasu,
yayi amfani dasu wajen samun abinda ya samu akan sa, ya kuma tabbatar da babu
wata alaka da zata sake hada su a nan gaba, ya datse duk wata hanya da zasu
neme shi.

   Ta jima tana bacci sosai, Ummimi dake durkushe a
gabanta tana kuka sosai taga ta motsa, ta cigaba da motsawa tana yamutsa fuska
kafin ta bud’e idon ta da kad’an kad’an da sukayi mata matukar nauyi, saman
dakin ta fara kalla, sai kuma ta shiga jujjuya idanunta tana son gano a in da
take, da sauri ta yunkura zata mike, Ummimi ta taimaka mata tana rik’e ta

 

“Karki tashi da sauri jiri zai iya daukar ki, ina tunanin
sun zuba miki magani ne.”. Ta fad’a cikin muryar kuka

 

“Ina ne nan? Me muke anan Ummi?”

 

“Ni ma ban sani ba, wanda kukayi magana dashi, shi ya kawo
mu nan, sun sato mu!”

 

“Musaddik?”

 

“Eh.”

 

“Innalillah wa inna ilaihi rajiun.” Ta furta a
hankali, kanta da yake jujjuyawa ta saka hannu ta dafe, amai ne taji yana taso
mata, ta yunkura da nufin tashi amma kafin ta kai kofar har ta soma aman, wanda
babu komai a cikin sa sai zallar ruwa, tun tana yi har ta koma kakari
kasancewar babu abinda yake cikin ta tun safe, rik’e ta Ummimi tayi tana kuka,
tana jera mata sannu, sai da taga ya lafa sannan ta taimaka mata ta maida ita
gefen tabarmar da ta tashi,

 

“Bari na samo miki ruwa, sannu.”

 

Ta tashi ta fito, su biyu ne a zaune suna karta, suna ganin ta
suka tashi

 

” Ruwa take so dan Allah. “

 

Da Ido sukayi wa juna signal, kafin daya daga ciki ya shiga wani
daki, ya dawo da ruwa ya mik’a mata, ta karba ta juya ciki, ta tarar da ita
tana ta juyejuye akan tabarmar, ta rik’e cikin ta da yake murda mata kamar zata
amayar da kayan cikin ta. Dagota tayi, ta bata ruwan ta kuskure bakin ta,
sannan ta sha, ta koma ta kwanta tana sake rik’e cikin ta.

 

   ***Kwanan Zeenat biy babu Bashir babu alamar sa,
Abba kuma ya zuba musu Ido be sake cewa komai ba, ko Mama be sake mata maganar
ba, shirun nasa yayi masifar bata tsoro, dan bata san me yake shiryawa ba,
ranar suna zaune Zeenat din na cin wainar fulawa, ba wani dadin ta take ji ba
amma itace kadai take mata dadin ci, sai nama da tuwo idan ta same su kamar
wata tsohuwar mayya, jigum jigum suke kowa da abinda yake damun sa. Kofar falon
ce ta bud’e duk suka kalli kofar a tare, Abba ne ya shigo, ya wuce dakin sa,
k’asa k’asa Zeenat din tayi masa sannu da zuwa be ma ji ba, ya shige jimawa
kadan ya fito, ya dubi Mama da tayi tsam tana kallon sa yace

 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button