GURBIN IDONOVELS

GURBIN IDO CHAPTER 1

“Na’am inna”

“Muguwa!……saboda bana nan ne shine kika barmana dabbobi su wulaqanta……seto me wanna nima ɓerde(sai na bata miki rai),ki kamasu ki kallaceminsu” daga haka ta sanya kai zuwa shiyyar da dakunansu suke ganin ruwan na sake qarfi.

Abinda ya daga hankalin maimunatu kenan,ta riga data saddaqar yau din mawuyacine ta samu barci matuqar ruwan yaci gaba da taba jikinta,wani irin jiki Allah yayi mata da baya qaunar ruwan sama,indai zai tabata to lallai zata kwana da zazzafan zazzabi,amma sai gashi innar ta wuce abinta ko a jikinta,nata burin dai kawai ta tattala mata dukiyarta.

Duk da yadda ruwan yake dukanta hakata dinga kamasu tana killacewa,ta daure wata saniya tana laluben danta da aka haifa wancan satin,santsin tabon dake wajen ya debeta,ta tafi suuuuu idanunta a rufe tana jiran ta jita a qasa,amma sai taji wani abu ya cake gaban qafafunta,abinda ya hanata faduwa kenan,ya kuma sanyata bude idanunta d asauri wanda tun kan ta bude din haske ya cika idanun nata.

Tarwai ta bude manyan idanun nata da ruwa ya jiqe gashin idanun nata,kamar yadda ya jiqe na girarta da kanta yasa suka hade gaba daya,fuskarta ta sake haske ta kumayi tarwai da wani irin kyau.

Idan har idanunta dai dai suka nuna mata mutum ne tsaye a gabanta,matashin saurayi dauke da lema da kuma fitilar torch light mai tsananin haske.

Da sauri taja da baya cike da tsananin tsoro,saboda tunda take kaf kafin rugarsu bata taba sanin wannan fuskar ba,abune kuma mawuyaci indai kaidin haifaffen rugarne ka tashi bakasan dan wani gidan ba”tsaya mana” ya fadi da dan qarfin murya amma a tausashe,abinda ya dan bata nutsuwar tsaiwar,yadda take dubansa ya tabbatar masa data gamsu dashi ba,don haka yace

“Me kike a ruwa a daidai wanna lokacin a haggo?” Qas tayi da kanta saboda wadatuwar hasken da walqiya ta bayar a lokacin ya haska mata fuskarshi sosai,ta kuma so ta ganeshi

“Ina daure dabbobi ne” kamar xaiyi magana sai kuma taji baice komai ba,ya ajjiye lemar kansa gefe,ha saqale fitilar a jikinsa,ya fara kama mata dabbobin yana tayata dauresu.

Tsai tayi tana dubansa,sai kuma ta taka a hankali itama ta fara kama wadanda zaa daure din tana tayashi sunayi tare,lokaci lokaci tana satar kallonsa,kamar yadda shima yake satar kallon nata lokaci bayan lokaci,ta gaza gasgata idanunta,wani yau a rugar yasa hannunsa yana taimakonta?,abinda ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya faru ba,rashin sabo da ganin hakan ya sanyata dari dari dashi,har zuwa sanda suka gama tas,ya qarasa wajen lemar ya dauketa yana rufeta,saboda bata da wani sauran amfani a wajensa,saboda abinda zatayi masa rigakafi dashi ya riga daya faru.

ZAFAFA BIYAR

Kundi kuma dausayin zaqaqa kuma da d’ad’an litattafan hausa masu cike da nishadi soyayya darasin rayuwa dana zamantakewa,tsantsar ilimantarwa da kuma fadakarwa

Wannan karon ma gasu tafe da wasu taskirar tsararrun litattafan guda biyar

SANADIN LABARINA
Hafsat rano

BABU SO
Billyn abdul

GURBIN IDO
Huguma

FARHATUL K’ALB
Miss Xoxo

INAYAH
Mamuhghee

Dukka guda biyar din akan

1k

Guda hudu:::700
Guda uku:::500
Guda biyu:::400
Guda daya:::300

Garzaya ki biya naki a fara a kan idanunki ta wannan account din

Hafsat Kabir Umar
2270637070
Zenith bank

Saiki tura shaidar biyanki
07040727902

MASU KATIN WAYA ZASU TURAWA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYA

09134848107

KARKU MANTA…..HAR KULLUM,SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA NE

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button