HALIN GIRMA 17

” Dan Allah nidai kayi hakuri ka yafe mana,dan Allah ka taimaka.”
” Wallahi Hajara babu abinda zan iya akai, kinji ma na rantse, ki barni dan Allah.”
Zama tayi dabas a k’asa, sai kuma ta tashi da sauri ta fice ta nufi shashen Gaji, ta same su a falon yan uwa ana ta shewa, ta wuce su zuwa ciki kamar wadda ta zare. A k’asa ta tsuguna ta gaida Gaji wanda rabon da tayi haka an dade.
” Dan Allah ki taimaka ki saka baki Dr ya fasa auren nan, wallahi idan akayi auren komai zai iya faruwa, nasan ke kadai yake jin magana dan Allah.”
” Yana ina?”
” Yana gida, dan Allah ki taimaka min.”
” Kije kice idan ya gama ina neman sa, Allah ya kyauta ya rufa asiri, sai a hakura kawai.”
Tashi tayi da sauri, ta manta ko godiya bata yi ba, ta fice kowa ya bita da kallon mamaki cike da jin haushi. Ko da ta fadawa Abban be ce mata komai ba, da ya fito ya shiga wajen Gajin bata yi masa maganar ba, ya gaisa da kowa sannan yayi breakfast da masa ya wuce wajen yan uwan sa.
***Daren ranar Moh be runtsa ba, duk wasu bakin da zasu iso sun gama isowa a lokacin kowa an sama masa masauki na alfarma. Abokan sa da sukayi karatu tare suke kuma aiki tare sai dai kowa wajen da take daban ne suka sauka a cikin gidan a bangaren Moh din, kafin a daura auren su wuce adamawa sannan su sake dawowa Kanon saboda events din da za’a yi a Kanon.
Raba dare sukayi ana hira, anan suke fad’a masa suma fa sun shirya masa kayataccen bikin sword crossing amma a abuja saboda suna so manyan su na wajen aiki su ma su zama sun samu halarta. Abubuwan sun so suyi ma Moh yawa saboda shi dai tsakanin sa da Allah zai fi so ace da an daura auren kawai su yi tafiyar su shi da ita,amma kowa kokari yake ya shirya wani abu da zai sake rik’e su, shi dai kawai dan kar ya fito fili yace baya so ne, amma har ga Allah da kowa ya hakura.
Da suka tashi da safe ma wasu suka dora da hirar in da Musaddik da wasu ciki suka tafi karasa abubuwan da basu samu gamawa ba, duk da sai bayan sallar juma’a za’a daura auren kuma komai da ya kamata su yi an ma riga an gama amma suma zasuyi nasu kokarin ko yaya ne.
Tun wajen sha biyu Takawa ya saka aka kira masa Muhammad, ya same shi da manyan mutane har da Mr President sai Bubu da tasa jama’ar. Aji dan tsoho ma ba’a barshi a baya, yaji dadin ganin su musamman Aji da be saka ran zuwan nasa ba. Bin su yayi daya bayan daya ya gaishe su dukka, kowa ya kawo kyautar bangirma ya damka masa, harda masu blank cheque duk dan a birge Takawa.
Godiya yayi musu dukka ya koma wajen jama’ar sa, suka dauki duk abinda zasu dauka suka wuce gidan Moh din dake Lamido Crescent yadda zasu fi yin komai a tsare.
***Wanka na wajen uku kenan idan tayi ta gama da wannan hadin ruwan sai Mamma ta sake bata wani, gaba daya wani irin sulbi fatar jikin ta take yi, tayi wani irin haske me kyau fatar ta sai glowing take kamar fuskar ta taji labari.
Tun da aka soma mata gyaran jiki ta tabbatar da komai nata ya sauya, hatta lallen da aka yi mata da gyaran gashi na daban ne, bata kara tabbatar da gatan da take dashi ba sai a event din da aka yi jiya taga tarin mutanen da suka zo domin ita, kowa don ya ganta kawai. Tasha kyaututtuka daga kawayen Mummy da yan uwa kowa burin sa ya yi mata abinda zai burge mummy din.
Sosai kuwa Mummy taji dadi ba kad’an ba, duk kuwa da miskilancin ta amma sai da yanayin ta ya sauya sosai.
Bayan an yi taron an gama ne da daddare take bawa Iman din labarin yadda akayi suka rabu da mahaifin ta.
“Kinsan aure rai ne dashi, idan lokaci yayi sai an rabu, amma har gobe ina son mahaifin ki, kaddara ce kawai ta raba mu, a lokacin alhajin mu yayi fushi sosai akan auren da mukayi ba da sanin kowa ba. Alhajinmu me kudi ne sosai kuma dan siyasa ne, yana matakin senate president a lokacin, hakan ya saka dole Ibrahim ya sake ni akan kar abinda mukayi ya shafi mutuncin sa, dan wasu ba zasu taba yarda da cewa munyi aure ba, ko bayan an haife ki nan ma yace a dole dole sai ya karbi yarsa, ya rik’e ta dan baya son ko kad’an mutuncin sa ya tabu. Hakan ya saka Ibrahim yin fushi, ya karbe ki ya kuma yi alkawarin ba zai bani ke ba, nasha kuka nayi ta rokon sa ina masa magiya karshe yayi min alkawarin idan da rai da lafiya zai kawo ki idan kin isa aure.”
” Amma fa ko bayan nan Alhaji yazo daga baya yayi regretting abinda yayi har ya nemi Ibrahim din da kansa ya kuma roke shi ya bashi ke, dan a lokacin girma yazo gashi yana son gyara, Mamma ce babbar mu gashi har lokacin Allah be bata haihuwa ba ,amma sai Abban naki yaki yace yayi hakuri ba zai iya ba.”
” Ni banga laifin shi ba dan nasan shi da Zuciya idan har aka taba shi,karshe dai nima nayi aure bayan na kammala wani course da nake na auri wani dan siyasa Babba, na dade sosai a gidan kafin karshe Allah ya bamu haihuwa daya, na haifi yan biyu Amaan da Amaani, daga nan kuma sai muka rabu.”
Shiru Iman tayi tana harhada maganganun.
“So kinga kowanne bawa baya wuce kaddarar sa, ni dake haka kaddarar mu take, dole ne kuma mu karbe ta hannu bibiyu mu gode wa Allah.”
“Haka ne mummy, wallahi na zata so Amaan yaran Mamma ne.”
Murmushi tayi
“Yaranta ne kam, tunda dai ni ban wani san komai akan su ba, Itace komai dinsu, Allah be bata haihuwa ba shiyasa ta dauki son duniya ta dora akan su.”
“Hajiya fa?”
“Step Mom dimu ce,itace ta haifi Zayd.”
“Allah sarki tana da kirki.”
” Sosai, kirkin ta yayi yawan da karyar mutum ya shigo gidan nan yace ba ita ce ta haife mu ba, ita ta kula da koman mu, Itace kuma a matsayin mahaifiyar mu har gobe.”
” Ashe akwai step moms masu kirki?”
” Akwai su da yawa Iman, ba dukka aka taru aka zama daya ba, wasu kuma zaki ga yaran ne basu da kirki sam, sun takura mata sun hana ta sakat, komai dai da kika gani akwai good side dinsa akwai bad side haka rayuwar take.”
” Haka ne.” Tace tana tuna Mama da Zeenat
Shirya ta aka yi cikin wasu yan ubansu kaya, kayan da ta tabbatar ba kananun kudi aka kashe wajen samar dasu ba, komai na jikin ta unique ne, me kyau da ya dace da ita. Sarkar gold din da Mummy ta siya mata Mamma ta saka mata, sannan ta zaunar da ita a gefen gado ta dauko mata abinci, ta zauna da kanta ta taimaka mata ta ci dan ta tabbata idan suka tafi babu batun cin wani abinci a wajen amarya. Ci tayi sosai sannan ta dauko wayar ta tana duba misscalls ko ya kirata, be kira ba, ajiye wayar tayi akan cinyar ta har lokacin tafiyar su yayi, text message ta tura masa ta saka wayar a jaka suka fito gaba daya, wajen Hajiya aka kaita tayi mata nasiha sosai kafin su nufi airport da su Ya Mubarak da sauran jama’ar da zasu halarci daurin auren, sai kuma su Amaani, Mamma da yan uwan su da zasu je a karasa bikin da su a matsayin dangin Mamanta.
Mintuna kad’an suka isa dasu Kanon, dan ma basu taho da wuri ba, Abba ne ya saka aka je aka taho dasu daga airport din, aka sauke su a bangaren Abba babba, ita kuma Iman aka wuce da ita ta gaida Gaji sannan suka shiga wajen Mama.
Gabanta ya fadi tun shigowar su, ko wanka bata yi ba, duk da ta dan samu nutswa bayan ta samu Gaji, tana da yakinin zata hana Abban kuma ya hanu, amma kuma jikin ta duk yayi sanyi tana dai zaune ne tana kallon kowa, masu kaya-kaya ma a cikin yan uwan ta haushin su take ji, gani take ai kamata yayi su tayata alhini. Kawayen ta kuwa da sun kirata take dagawa tace an daga bikin zata neme su, abinda bata sani ba zance ya gama zagaya ko ina wasu ma da gayya suke kiran dan su tabbatar.