HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 26-30


2/2/22, 18:35 – Buhainat: Halin Girma

      26

 

******* �

 

Sai da ya gama komai sannan ya biyo ta dakin ya yaye abinda ta
rufan yana shigewa jikinta

“Kinyi bacci?” Yace yana leka ta kin motsi tayi a dole
tayi bacci, fuskar sa ya matsar jikin ta ta, ya taba saman idon ta, motsi yaji
idon nayi yayi dariya yana cewa

 

“Stop pretending ki tashi, nasan ba bacci kike ba.”

 

“Uhum…”

 

“Yawwa, hira zamuyi, zaki iya tambaya ta koma menene akai
na, zan sanar dake.”

 

_”Farko  dai sunana Muhammad Ahmad Santuraki, kamar
yadda kika gani, mahaifi na shine sarkin Adamawa, sannan Mahaifin Ammi shine
sarkin Kano, na taso tsakanin Kano da adamawa in da zama na yafi yawa a Kano
saboda yadda Maimartaba ya kwallafa rai a akai na. Nayi karatu na both na
addini dana boko har na kai matakin captain a yanzu a bangaren aikin soja. Ni
kadai Ammi da Bubu suka haifa,bani ne dansu na farko ba, kuma bani ne na karshe
ba amma ni kadai ne Allah ya raya musu. Aji shine Mahaifin Bubu da sauran yan
uwansa su hudu, shine na biyu akwai babban wansa wanda Allah yayi masa rasuwa,
shine Mahaifin Laila da Kamal, bayan rasuwar sa ne Bubu ya auri matar wan nasa
wadda ake kira da Kilishi,a lokacin kuma rikon su ya dawo hannun Bubu tunda
dama chan gida daya muke baki daya. Daga nan ne kuma Aji ya sauka ya nada Bubu
domin ya huta shima. Tun farkon dawowar Kilishi gidan mu, daidai da sakan daya
bata taba kauna ta ba, infact idan za’a bata wuka ace wa zata kashe toh tabbas
ni zata kashe, bata kaunata ko kad’an duk akan sarautar da take ganin Kamal
dinta ne yafi dacewa ya karbi kujerar tunda Mahaifin su shine gaba da Bubu. Tun
da na taso bani da ra’ayin sarauta ko kad’an, mutane da yawa na min kallon
wanda be san abinda yake ba,. abubuwa da yawa sun faru wanda ni kadai na san
su, wanda suka kara taimakawa sosai wajen ganin ban karbi tayin bubu ba, tsawon
lokaci ya dauka yana bibiyata da maganar amma sam ban taba nuna masa zan iya
ba, illa iyaka sai ma na nisanta kaina da duk wani abu da ya shafi gidan da
sarautar baki daya. Wannan dalilin shine ya saka ni zama lafiya har wannan
lokacin. Akwai abubuwa da yawa na ban mamaki a gida irin na sarauta, wanda sai
wanda yake cikin ta ne kawai zai iya ganewa, babban kalubale shine tsantsar
makirci da nake kyautata zaton dashi ake haifar da yawa yawan yayan sarauta.
Amma duk da haka akwai mutane na gari a ciki wanda basu da matsala ko kad’an
sai abinda ba za’a rasa ba.”

 

Shiru yayi kamar me nazari, kafin daga bisani yace

 

” Laila ta jima tana so na, tun bayan da ta taso ta san
menene soyayya ta kwallafa rai akaina, sai dai nayi ma kaina alkawarin ba zan
auri jinin saurata ba, sannan ba zan iya auren mace me irin halin Laila na
rashin sanin darajar hatta mahaifiyar da ta kawo ta duniya, a sangarce ta tashi
ganin duk wani abu na duniya ta same shi, kyau kudi mulki sannan uwa uba gata,
sai ya zama na bata san komai ba sai kanta, bata son talaka da duk wani da zai
rabe ta, she’s very selfish, mutum ce ita da zata iya komai dan ganin ta samu
muradin ranta. Mafiya yawan lokuta takan aika min da sakonni, na kyaututtuka ko
wani abu, amma ban taba nuna na gane me take nufi ba, har tazo ta tarkata ta
bar k’asar don karatun ta na Masters, hakan ya saka ni samun sauki, sai gashi
ta dawo a lokacin da maganar auren na ta kai mata, bansan da wanne shiri ta
dawo ba, amma nasan ba zata hakura ba.”

 

” Humm…”

 

Taja numfashi tana jin shi, kanta a saman chest dinshi yana wasa
da gashin kanta, dagota yayi, suka kalli juna,

 

“Nayi alkawari zan kula dake da dukkan karfina, gatan da
kika rasa zaki same shi yanzu har sai kin ce na gaji Muhammad dina.”

 

Ya karashe cikin kwaikwayon muryarta, dariya tayi tana dora
fuskar ta a saman tasa.

 

“Baka fad’a min dalilin da ya saka ka boye identity dinka
ba.”

 

“Saboda step mom dinki ne, na samu labarin komai ta wajen
Sadeeq abokin yayanki Habib, shiyasa na zo a haka dan na tabbata ba zata taba
hutawa ba har sai ta tabbatar da auren mu, wanda na tabbata da nazo a ainihin
identity dina da ba lallai ta bari ba.”

 

” Haka ne.” Tace a sanyaye cikin son kauda tunanin
Maman da zaman da sukayi.

 

” Na tambaye ki…”

 

” Ummm.” Ta daga mishi Kai

 

” Did you love me?”

 

Da sauri ta kalle shi

 

” I’m serious, inaso na sani, ko tausayi na baki kika
taimaka min kika aure ni!”

 

” Inji wa?”

 

” In jini, haka nake gani, tunda ni banga wata alama ba,
baki taba furta min ba, ni kadai nake kida na nake rawata.”

 

Sauka tayi daga jikin shi, ta kwanta tana juya bayanta.

 

” Ni dai goodnight bacci yazo.”

 

Da sauri ya jiyota

 

” Ai baki isa ba, sai kin fad’a min.”

 

Sake juyawa tayi tana jan duvet ta rufe kanta, ya shiga ja tana
ja, ganin zata bashi wahala ya saka shi dagata gaba daya, ya mike da ita a
jikin shi zuwa doguwar sofa din dake chan gefe a dakin, zaunar da ita yayi akan
cinyar sa ya warware duvet din daga jikin ta, yunkurawa tayi zata gudu ya riko
waist dinta ya dawo da ita.

 

“Sai kin fad’a min, ko kuma na miki irin abun jiya.”

 

“Na shiga uku.”

 

Danne dariyar sa yayi ganin yadda ta firgice

 

“Allah kuwa da gaske, tell me you love me or else…”
Ya rad’a mata a kunne

 

“Me zance toh?”

 

“Abinda nayi ta ce miki, I love you Zahraah, Iman, Fatima,
Baby, sweetheart duk dai.”

 

“Ni dai… Ni bansan me.zance na.”

 

“Kice I love you baby, ki hada da hot kiss a nan.” Ya
turo bakin sa gaba, hannun ta tasa akan bakin ya dan cije ta, tayi saurin janye
hannun ya maida shi baya.

 

“Oya ina jinki, say it, inaso naji muryar ki tana fad’a

 

Shiru tayi kunya na kamata, kunyar sa take ji sosai ta yaya zata
fara furta masa wani I love you right in front of him, ai da kunya tunda ba
sabawa tayi ba, gashi har da wani hot kiss shi ko kunyar nan ma babu. Rufe
idonsa yayi ya sake turo mata fuskar tasa

 

” I’m all ears.”

 

Minti kad’an yaji shiru ya bud’e idon, lokacin har sun sauya
zuwa wani abu daban, saurin dauke kanta tayi tana turo baki. Kamar daga sama
taji hannun sa a cikin rigarta, ta juyo da sauri tana rik’e hannun

 

” Dan Allah tsaya zan fada, wallahi zan fad’a.”

 

” Oya ina ji, don’t waste my time.”

 

” I lo…ve… You.” Tace a rarrabe

 

” Ban yarda ba, ki fad’a kai tsaye daga chan k’asan zuciyar
ki, in a romantic way., Kice I love you Muhammad. “

 

” I love you Muhammad. “

 

Tace da sauri kamar wadda tayi gudu ko tsere.  Murmushi
yayi mata ganin yadda ta fitar da maganar, yana son komai nata, har kunyar ma,
ya san in dai suna tare toh har wanka ma sai ta yi masa wataran, zai koya mata
komai, yadda yasan yana so rayuwar auren su ta kasance.

  Zaka rantse wani babban laifin ta aikata ganin yadda
take jujjuyar da fuskar ta gefe, zaunar da ita yayi ya fita, tashi tayi da
sauri ta haye gadon ta kwanta, shigowa yayi dauke da cups akan tray da vacuum
flasks dake dauke da black tea, dorawa yayi akan table ya zuba ya mika mata,
sannan ya zauna a gaban table din ya shiga kurbar nasa da zafin sa. First time
na shan black tea dinta kenan amma sai taji yayi mata dadi sosai, sai dai bata
shanye ba ta ajiye a gefen nasa ta dawo ta sake zama, sai kuma ta tashi ta nufi
toilet din ta daurayo bakin ta, ta fito ta haye gadon ta kwanta. Kallon ta yake
har ta gama ta rufe idon ta, sai da ya gama shan tea din tas, ya wanko bakin sa
sannan ya kashe hasken dakin ya barshi k’asa k’asa, ya kwanta rigingine yana
kallon sama, yana tunanin yadda zai bulowa al’amarin Lailah don baya son a samu
matsala, gashi har lokacin bashi da wata hujja da zai kare kansa. Ganin zai
cigaba da bata lokaci wajen tunanin abinda bashi da iko akai yaga gwanda kawai
yayi abinda zai karu ya kuma samu dumbin lada, duk da yasan duk gudun sa take
amma ba zai iya hakura ba.

  Ji tayi an matso ta sosai, tsoron ta ya karu zuwa sanda
taji yana jujjuyata, kuka ta saka masa bil hakki da gaskiya dan tayi masifar
tsorata da abinda ya faru,

 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button