HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 41-45

   

   _Halin Girma_            *41*

***Ruwa ta fara ambata sanda ta farka, da sauri Mamma tayi wajenta itace take tsaye dama, Mummy na kan sallaya tana lazimi ta mike da sauri cikin tsananin farin ciki.

“Alhamdulillah.” Ta furta tana karasa kusa da Mamma da take jera mata sannu, da ido kawai take bin su tana son tuna abinda ya faru karshe. Murmushi tayi cikin dauriya tace 

“Mamma.”

“Na’am Iman, sannu kinji?.”

” Alhamdulillah mun auna arziki. ” Ta juya tana fadawa Mummy da ta kasa boye farin cikin ta

“Fatima. ”

“Mummy. ”

” Sannu kinji, akwai abinda yake Miki ciwo? ”

Da hannu ta nuna cikin ta, taba cikin Mummy tayi kila saboda wankin cikin da akayi mata ne, 

” Bari nayi musu magana tunda ta farka. ”

” Bari naje. ” 

Mummy tace tana yin gaba, ta bar su da mamma tana tambayar ta. Tare suka shigo da nurses su biyu, mamma ta matsa suka duba ta, sukayi mata tambayoyi sannan suka ce a bata ruwa tasha da abinci sannan suka fita daya ta sauki file din ta daya kuma ta tafi kawo mata magunguna daga pharmacy. 

   Taimaka mata mamma tayi tunda an cire drip din ta kai ta toilet, ta gasa mata jikin ta, ta taimaka mata tayi wanka da brush kafin ta fito Mummy ta hada mata tea me kauri da kidney pepper soup da aka kawo daga fada.

  Daure da alwala ta fito bayan ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga mara nauyi ta saka Hijab ta zauna a gadon ta biya bashin sallolin da suke kanta, sai da ta idar sannan ta dan ci abincin kad’an ta koma ta kwanta lamo tana jin jikinta babu kwari ko kad’an.

   Abba ne ya shigo tare da wasu  mutane masu rawani, suka dubata sukayi mata ya jiki sannan suka tafi, Abba ya rakasu ya dawo ya zauna yana sake dubata. Tsam Mummy ta bar dakin ta koma waje ta bar Mamma a ciki suna magana da Abban, ya dan jima a ciki sai da yaga alamar ba zata dawo dakin ba bayan kuma ita ta kirashi da Iman din ta farka sai ya tashi kawai yayi sallama ya tafi akan zai dawo anjima.

   A waje suka hadu da Mummy din, ya sameta har wajen da take zaunen yayi mata magana, ta amsa masa sama sama kamar tana jin haushin sa ko wani abu, be gane dalilin ta ba, ganin a waje ne ga kuma Moh da ya nufo su ya saka shi kyale ta ya tafi, suka gaisa fuskar sa fayau alamun ya samu labarin farkawar Iman din. Komawa yayi ya raka Abban har mota sannan ya dawo, ya tarar da mummy da Mamma din duk a waje, kila Mummy din ce ta sanar mata da zuwan sa shiyasa suka fito ba sai ya shiga su hau fita ba, gaishe su yayi da tambayar ya mai jiki sannan ya danyi jim a wajen sai da Mamma tace ya shiga sannan ya tashi ya nufi dakin da daukin ganin ta. 

   Ko sallama ya maita yayi sai da ya tura kofar ya shiga sannan ya tuna yayi sallama ta dago daga kwanciyar da tayi ta kalle shi. Da sassarfa ya karasa kuwa, ya haye saman gadon ya tattaro ta zuwa jikin sa, ya rungume ta tsam damuwar da yake ciki na raguwa. Luf tayi a jikin nasa tana jin nutsuwar da ta rasa tsawon kwanaki, bata san haka tayi kewar sa ba, sai yanzu da suke tare, kuka ta saka masa ya sake rungume ta yana jin shima kamar ya rushe da kukan. Sai da yaga kukan nata na neman zarcewa sannan ya dakatar da ita ta hanya shafa bayan ta ya shiga magana a kunnen ta

“Shssh… Karki karawa kanki wani ciwon please, you are safe now. Babu wani abu da zai sake faruwa, I will protect you with my life.”

Shiru tayi tana jan numfashi, ya cigaba da shafa bayanta har sai da yaji tayi shiru gaba daya, sannan ya dago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta, murmushin ya sakar mata ta maida masa itama.

” Me yake miki ciwo yanzu? ”

” Kai na.. ” Tace a hankali

” Sannu zai daina a hankali, komai zai wuce, ba zan sake tafiya ba barki ba nayi miki alkawari nan.”

Maida kanta tayi jikin sa ta kwantar ya gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi, ya saka hannu yana mata tausa a hankali.

  Sun dade a haka har sai da akayi knocking a kofar, ya zameta ta kwanta sosai akan gadon ya sauka sannan yace

” Bismillah a shigo.”

Bataliyar yan gidan su ce, tun daga kan su Ya Maryam da matan gidan hadda Dadah da wasu ma da be san su ba, a gurguje ya gaisa dasu ya bar musu dakin dan dakin ma yayi musu kad’an.

   Dakin da Musaddik yake ya wuce, ya sameshi a zaune ya gama cin abinci, yayi fes dashi jikinsa kuma yayi kyau, kanin sa ne yake kula dashi suka gaisa da Moh din sannan ya basu waje dama yana so yaje ya siyo abu a shop sai yayi amfani da damar ya tafi.

“Jikin ka yayi kyau sosai friend.”

“Wallahi Alhamdulillah, mun gode Allah, ya jikin Madam din?”

“Itama Alhamdulillah wallahi, ta samu sauki.”

“Masha ALLAH. Allah ya kara mana lafiya baki daya. ”

“Amin, ka tabbata kana cikin abokai na gari, Allah ya hada mu tare a inuwar al’arshi, bansan da wanne baki zan gode maka ba, ban kuma san da wanne ido zan kalle ka na gode maka ba, ta ya akayi na kasa ganewa? Na kasa banbance ka da wani daban? How long ka zauna a wajen sa.? ”

” Mu daina tunawa dan Allah, tunda ya shigo hannu shikenan nasan dole zai girbi abinda ya shuka. ”

” Still dai inaso nasan komai… ”

” Ka bari mu koma gida, zan baka labarin komai, for now kayi fucusing akan case din cikin gida, yau saura kwana uku su juya komai, kana bukatar gabatar da evidence din nan.”

” Haka ne, kuma abinda ya faru yanzu ya saka na kara jin kowanne abu akwai good side da bad side dinsa, abinda na tsana nake ganin shine kawai matsalar ta, har naki bin umarnin Bubu akai,shi zan yi facing yanzu, zan karbi abinda ya zama mallaki na, zan farantawa mahaifi na kamar yadda ya dade yana burin ganin ranar. ”

” Da gaske kake? ” 

” Da gaske nake. ”

” Kai masha ALLAH, Bubu zai fi kowa murna shi da Aji. Dama a komai alkhairi ake nema ba son zuciya ba,nayi murna sosai aboki na, Allah ya baka sa’a. ”

” Amin. ” Yace yana daukar ledojin maganin sa

” Kana shan magungunan nan kuwa?”

” Ina sha. ”

” Good, da baka sha da sai na saka ka… ”

” Frog jump. ” Ya karasa masa suka kwashe da dariya suka tafa

” Wallahi ka raina ni, Capt guda, Capt Muhammad Ahmad Santuraki, babu wani respect ko? ”

” Ayi hakuri tsohon Capt! ”

Duka ya kai masa a kafadarsa, ya goce suka sake kyalkyalewa da dariya.

***Baki daya ta rasa abinda yake mata dadi, ta rasa in da zata tsoma ranta taji sanyi, cikin jikinta yayi masifar takura mata, babu abinda take so take kulafuci sai mijinta Bashir, takanas ta aika aka samo mata irin turaren da yake amfani dashi amma duk a banza, watarana sai ta shiga daki tayi kuka gashi Abba yayi shiru da maganar, ko dan abinda ya faru a kwanakin ne? Babu irin kiran da batayi wa Bashir amma sai yace mata ta kara jira zaizo,. Takanas ta samu Mama a daki da ita ma kanta ta gaji da zaman Zeenat din ta kuma damu da shirun da Abban yayi dama Bashir din. Da kallo ta bita har ta zauna a kusa da ita, tun ma kafin tayi magana ta riga tasan me ya kawo ta

“Yau zan samu Abban ku da maganar, ni kaina hankali na ba akwance yake ba, kema kuma duk alamu sun nuna dakin mijinki kike so, ki tattara ki koma Allah ya baku zaman lafiya, me afkuwa ta riga ta afku shiyasa yayi biris damu shima Bashir din yasan ya gama damu, sai ki koma kawai ya zamuyi?”

“Nima dama maganar da nazo muyi kenan.”

“Ai na sani, oh Zeenatu ana son miji. ”

Da sauri ta rufe idon ta, ta tashi ta bar dakin a kunyace, ita kanta bata san menene ya hau kanta ba, yadda take ji idan bata koma ba, komai zai iya furuwa da ita. Ga wani masifaffen son cikin jikin ta da take ba zata so ya taso ba tare da mahaifin sa ba, ta taba karanta wani littafi da yarinyar ciki tayi gangancin kashe aurenta ashe akwai ciki, karshe haka ta haife dan a gida kuma ta cigaba da rainon sa a cikin bakar wahala, gashi duk wanda yazo auren ta sai yace ba zai rik’e mata da ba.

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button