HALIN GIRMA 17

Gaishe ta Iman take amma ta tsura mata ido ta kasa amsawa, tsabar bakin ciki ta kasa boye shi, mamakin yadda yarinyar ta sauya take, Ashe haka take da kyau bata sani ba? Ko Kuma dai yanzu ne kyawun ya fito. Kayan jikin ta kawai ta kalla tasan an kashe kudi, idon ta ya sauka akan sarkar wuyan ta, tana ta sheki da kyalli kana gani zaka gane zallar gold ne. Tari ne taji kamr zai sarke ta, duk suna lura da ita da suka ga kamar bata hayyacin ta sai kawai suka tashi suka koma in da aka sauke su.
Lokaci lokaci Iman na kallon wayar ta, ta matsu suyi magana ta san halin da ake ciki, ba zata kirashi ba dan tasan yana cikin hayaniya amma taso ko yaya ne ya kirata.
Daidai lokacin da aka saka na daurin auren yayi, ta kwanta kawai lamo tana jin faduwar gaba, wani iri kamar tace ta fasa, ba’a gidan ake daura auren ba, a babban masallacin Kano ne da yake kusa da gidan sarki shiyasa basu san abinda yake faruwa ba.
Ji tayi gidan yayi tsit, kamar babu mutane, ta dinga jin wani tsoro tsoro yana shigar ta, Mamma ce ta taba ta, tayi mata murmushi tace
“Kowacce mace ta kan ji irin haka idan za’a daura mata aure, kiyi addu’a kinji yata?”
Da kai ta amsawa Mamman, ta soma karanta hasbunallahu wa ni’imal wakil, a hankali taji nutsuwa na saukar mata. A daidai lokacin suka ji karar tsayawar motoci, kafin gidan ya kaure da wata irin guda me karfin gaske.
Wani maroki ne me muryar tsiya, ya shiga kirari cikin muryar sa da ta shiga har kwakwalwarta, ta tsaya chak da tunanin abinda kunnen ta yaji
“Alhamdulillah, Allah mun gode maka, an daura auren Yarima Muhammad da amaryar sa Gmbiya Fatima, dan sarki jikan sarki, kuma sarkin gobe idan Allah ya kaimu.”
Farin ciki ne ya kama su Mamma suka hau murna, bata fuskantar komai, a daidai lokacin sakon sa ya shigo wayar ta,
“Duba whatsapp dinki amarya tah.”
Da sauri ta shiga whatsapp din har ta mantawa bata kunna data ba ,kunnawa tayi messages din suka shigo tayi saurin bud’e nasa. Hotuna ne masu yawa, ta hau bud’e su tana kura idon ta, hoton farko ya saka numfashin ta tsayawa na dan sakanni
“Capt Muhammad Ahmad Santuraki.”
Yayi captioning hoton, yana sanye da nadi irin na sarauta, da kunnuwan sa guda biyu a sama da yake nuna yadda tsarin sarautar take, gaba daya gani tayi an sauya mata shi,shine sai wasu abubuwan da yawa da suka dauke ta zuwa wani tunani na baya tana kokarin alakanta abubuwan da tayi ta shakku akan sa. Kwanciyar fatar sa, da yadda yake magana yana bata mamaki matuka.
Sauran hotunan ta shiga bubbudewa, duk akwai shi aciki tare da manyan k’asar da ma ketare, hoton sa da Takawa da yadda Takawan ya rik’e shi says alot. Ji tayi gaba daya ya goge mata hadda, ya bar kanta blank bata ma san wanne irin tunani zatayi ba.
Wasu mata ne suka dinga shigowa, wanda kana ganin su zaka san su din hadimai ne daga gidan sarauta, duk suka taru waje daya cikin girmamawa suka hau gabatar da kansu.
Kayan hannun su Mamma ta saka suka ajiye a gefe sannan ta aika wata bangaren Gaji akan wasu suzo a cikin dangin Abban, hakan ya bawa Iman damar sulalewa ta shige dakin Umma, sannan ta kira Ya Maryam ya waya tace dan Allah tazo dakin Umma. Sai gata tazo har da saurin ta, murna fal fuskar ta dan suma ba karamin mamaki suka shiga ba.
Hotunan ta soma nuna mata, sannan ta hau mita kamar zatayi kuka, katse ta Ya Maryam tayi,
“Yarinya kad’an ma kika gani, sai kin ga uban lefen da aka kawo miki, wallahi Iman Allah ya baki miji, miji na kere sa’a me sonki tsakani da Allah, kinyi sa’a, halin ki ne ya jawo miki amma.”
“Amma me yasa zai rufe ni?”
“Haka tasa salon soyayyar yake, kin ganshi kuwa? Salo,aji kyau ga kudi.”
Turo baki Iman tayi, ta rasa me ma zatayi, Itace zata shiga gidan sarauta? Sarauta ma babba irin ta Kano? Katse mata tunani yayi da wani sakon nasa
“Meet me a seat room din Abba, na matsu na ganki, I want to feel you right close to me.”
Da sauri ta kife wayar,. Maryam da taga komai ta kyalkyale da dariya
“Su Iman an shiga sahun manya, jeki dan Allah yaji duminki, halal dinsa ce ke yanzu ehe.”
Duka ta kai wa Maryam din ta manta ma basa yar haka da ita, ta sake kwanshewa da dariya tana tsokanar ta
“Saura kije ki dinga wannan nuku nukun naki, tashi ki sake gyara jikin ki, bari naje na karasa jin drammer da ake a gidanku, Zeenat na chan ta tada aljanu wai ba ta yarda ba, kinsan an riga an daura itama.”
“Kamar ya?” Tace cikin mamaki
“Jeki ke dai wajen aikin Allah, bari zan baki labari in details.”
Ta juya da sauri ta fice bayan ta sanarwa da Mamma cewa Iman zata je yarima na seat room suyi hotunan tarihi.
Rano????????
#Note edited
*_ZAFAFA BIYAR 2022????_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*????????????
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*????????
09134848107
[ad_2]