JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL
Saida sukaje gda ta juya zata shiga dakinta Momy tace “bantaba tunanin hakan daga gareki ba Meenah mijinki zabinki a baya banga zafin da rayuwa tayi tsakaninki dashi ba da zaki zabi azabtar dashi Meenah koda a yanzu baki zabeshi ba cancanta aka duba aka zabanki shi kada kiyi wasa da damarki inaji a jikina Kareem zai sharenki hawaye don Allah Meenah indai da gaske kin daukeni matsayin uwa a gareki kiyima mijinki biyayya ki rintse idonki ki ninka hqrnki akan wanda kikayi a baya. Tabbas akwai qalubale cikin zamanku to Amma qaddara ta riga fata haka Allah ya shirya mana addu’a Rasheed yake buqata kawai daga gareki”
Sunkuyar da kanta tayi tana sauraron Mom harta gama fadar abinda zata fada
Ta juya ta fita ta kwanta rigingine zuciyarta na hasaso mata abubuwa da dama da suka faru a baya lkc zuwa lkc tana dauke hawaye a fuskarta itadai batasan sanda bacci ya dauketa ba wajen biyun dare ta farka tayi alwala ta tayar da nafila tana roqon Allah ya shiga lamuran Rasheed a duk inda yake ya tsareshi da tsarewarsa ya bayyana shi cikin aminci da salama bayan ta idar ta zauna tana lazumi taji wayarta tana ring takai hannu ta dauka lambar Kareem ce taja tsaki ta katse wayar ya Kuma Kira ta dauka zata kashe maganganun Mom suka rinqa dawo mata tayi qarfin halin dorawa a kunnenta
Ajiyar zuciya ya sauke lkcn da tayi masa sallama ya Amsa cikin wata irin murya me tsananin sanyi shiru taci gaba da wanzuwa wadda harta sabbaba mata tunanin kashe wayar can taji ya sake jan zuciya yace “nayiwa Mai Martaba mgn game da tariyarki yace nayi miki mgn shiyasa na kiraki a wannan lkcn me kike shiryawa meye plan dinki?” Shiru tayi kamar bazata ce komi ba shikuma yayi kasaqe Yana jiran jin cewarta alamar da yaga na ba mgnr zatayi ba yasashi cewa “ok bakida wani tsari ga dukkan alamu ni inadashi yau Litinin na baki zuwa juma’a ki gama komanki zaki tare a gdanki kici gaba da ibada kamar kowacce mace, ki duba account dinki na tura miki wasu yan canjika Basu da yawa kiyi hqr dasu idan basu isheki shirye²nki ba zanyi qoqarin qara miki insha Allahu”
Katse wayar yayi daga haka tabi wayar da kallo cikin mamaki lallai ma Kareem dinnan yana fama da kansa yana fama da bala’i shikam dama ya hqr ya barta anan inda take da yafi musu kwanciyar hankali dukkansu. Qwafa taja ta duba alerting din da akayi mata dazun ta zare ido tare da cewa “wht? Me zanyi da kudaden nan ni Aminatuh 2 millions ta meye ce?” Komawa tayi ta kwanta baccin da bata koma ba kenan washegare wayewar Litinin ta fara shiri don komawa makarata Mom na kallonta batace mata komai ba harta gama shiryawa ta dauki jakarta ta saba tace “mom zan koma school” murmushi tayi tace “da izinin wa?” Kallon Mom tayi da sauri tace “izini Kuma?” Daganta kai tayi tace “mijinki ya kirani da asuba yace kada ki koma makaranta kiyi shirye²nki juma’a zaki tare a gdanki Litinin me zuwa zaku tafi Saudi zai koma can da zama abinda yayi saura na karatunki yayiwa H.O.D na department dinku mgn zaayi bakin qoqari” zama tayi dabar a gurin gumi na karyo mata tace “ni Kuma Mom in bisa Saudi haba Mom don Allah kice masa aa inada abubuwan da sukafi binnasa muhimmaci anan Mom inason in nemi dangina su hadani da dangin mahaifiyata idan naci gaba da zama a haka akwai matsala please Mom kisa baki don girman Allah”
Murmushi Mom tayi tace “wannan duk me sauqi ne ni na daukar miki alqawarin bibiyarsu har zuwa lkcn da zaa dace kibani address nasu” sunkuyar da kanta tayi hawaye wani nabin wani itadai bataso ba taso tayi komanta da kanta miqewa tayi ta koma dakinta ta kishingida zuciyarta na zafi haka yinin ya kusan qarewa kiran duniya da yakeyi mata taqi dagawa itafa bayan zafin tsanarsa saboda mahaifiyarsa da tayi harma da ganin rashin dacewar wannan auren nasu duk da tasan ba haramci a ciki Amma wata halal din ta cancanci bari don kunya.
Da la’asar tana kwance Mom ta turo qofar ta shigo da sallamarta ita da wata mata Meenah dake kwance ta miqe suka gaisa da matar Mom tace “wannan itace nakeyi miki mgn aurenta na farko yazo a wani yanayi baayi mata komai ba so data haihu an gyarata Amma anja shekaru kusan shekara antafi biyar shine yanzun nake buqatar ki qure fasaharki wajen gyarata ko nawa ne mijinta yace zai biya” suna hirarsu wannan Hajiyan na fito da saiwoyi da magunguna tana yima mom bayani tare da turaruka itadai tabe baki kawai takeyi bata yarda abin gaske ne ba Saida taga an dauki wani qoqo an zuba wani ruwan tsumi an dauko wasu barbade barbade anyi an gwamutsa da danyan madarar shanu wai sun miqo mata tasha.
Ta dubi Mom da idanunta daya kawo ruwa zatayi mgn ta kuwa daure fuska tace “aini dama nasan ban isa dakeba Aminatuh nunamin bani na haifeki b….” Da sauri ta karbi qoqon maganin jikinta na rawa ta kafa bakinta ta shanye daqyar tana kakarin amai matar tayi murmushi tace “wannan shi kadai ma idan Tasha na kwana biyar ya wadatar bare zaa hada da wasu tun daga wannan rana Juhud ta bani ta lalace da magunguna wasu tsarki wasu Sha wasu dafawa itadai bakinta har daina tantance dandano yayi cikin kwanakin batada aikin daya wucce kuka.
Wayar ma da Kareem ke kiranta ta jefashi a blacklist ko ya Kira baya samunta hakan tasa dole ya qyaleta yasan duk inda yau takai da jimawa gobe tana tafe yanaji a jikinsa wataran wannan qiyayyar zata shude tunda da babu ita daga baya ta wanzu to watarana itanma zaa nemeta a rasa, da wannan tunanin ya tattarata ya zubanta ido akayita shirye²n tariyar tata shine da Mom da Ya’isha da Aunty Hamida suketa digiminsu dakin uwar ango da yan’uwansa Babu me ko lale da bikin hasali ma ko bangaren da ake shagalin basuyi itama amaryar haka saidai idan Mom tayi mata dole sannan take dan motsawa hakana aketa kaiwa da komowa su Ya’isha sune yan jeran amarya har zuwa lkcn Zahrah bata dawo ba aka gyarawa Juhud dayan bangaren kamar yasan zaiyi mata biyu dama tsarin mace biyu yayiwa gidansa bayan sun gama gyarawa sun zubanta duk wasu kayan alatun rayuwa suka kullo suka taho gda sunata yabawa da kudin da Kareem ya narkar a furniture dinta lallai ba qaramin so yakeyiwa Meenah ba.
Ta dauki gyaran jiki na ban mamaki abinka da farar fata har wani yellow takeyi yanda Mom ke rawar jiki a wannan bikin ko Rasheed ne ya dawo ba lallai tayi ba ko lalle da akayi mata dishi² ya kama jikinta saboda tsabar gyara hatta gyaran gashi a gda akayishi yin duniya suje gurin gyaran taqi tana maqale a daki kamar wata mara gsky ko yaushe cikin kukan rashin mijinta take da anbarta da wannan damuwar ma da tafi mata fiye da wannan da aka qara mata
Ranar juma’ar Mom taga ikon Allah yini Meenah tayi tana kuka tana kiran Rasheed duk dauriyar da Mom takeyi a wannan karon Saida ta kebe itama taci kuka ta gode Allah Mom bata qara tsinkewa da lamarin Aminah ba Saida magrib da Kareem ya turo da motocin daukar masa amarya tunda ta fice a sashin su Mom din aka nemeta aka rasa babu wanda hankalinsa bai tashi ba amarya ta bace da aka fadawa Kareem neman zaucewa yayi ya nufo gdan afujajan suka shiga nemanta lungu da saqo domin sun tabbatar da cewa tana cikin gdan kasancewar masu tsaron qofofin gdan sunce Babu wacce ta fita gabadaya sun gama karade gdan babu dalilinta sai a qarshe Mom tace aje bangaren Rasheed ko can tayi haka Kareem da Mai Martaba suka nufi part din ga mamakinsu suka tarar dashi a bude suka kalli juna babu furuci suka kutsa ciki yayi qura sosai part din haka suka rinqa dubawa can cikin wani daki suka rinqa jiyo shassheqarta har rige² sukeyi wajen shiga dakin sukaja sukayi turus dukkansu ganinta zaune gefen gado rungume da wani hoto a qirjinta sai kuka takeyi me ban tausayi.
Wani abu me nauyi ne yazo ya tokarewa Kareem maqoshi ya furzar da iska me zafi ya juya ya fice daga dakin sai Mai Martaba ne ya qarasa shiga ya kamo hannunta Babu musu ta miqe tanaci gaba da kukanta idonta lullube da alqyabba ya fito da ita harabar gdan Ya’isha ta nufosu da sauri suka sanyata a mota tana qarawa kukanta sauti tana Kiran sunan Baffa’am Sarki junior dukkan wanda yake a gurin hatta Mai Martaba Saida tasashi sharar hawaye.