FARHATAL-QALBNOVELS

FARHATAL-QALB CHAPTER 4

FARHATAL-QALB
(FARIN CIKIN ZUCIYAH)
                     ????
NA

NANA HAFSATU
(MX)

AREWABOOKS:MISSXOXO
WATTPAD: MISSXOXO00

ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS

FREE PG:4
××××××

Marka ta ‘daga kai sheqeqe ta dubi Najan isubu hade da jan tsaki ta kaikaice kanta gefe.

Domin Marka tana cikin jerin tsofaffin nan masifaffu wanda basa ganin kowa da gashi.

Don kaf cikin sansanin su na manya tsofaffin unguwar shurah ta kere su a rashin mutunci da rashin ganin daraja. Haka takan taka duk wanda ya nemi ya kawo mata wargi. Duk girman shekarun ta wata rana sai an shigaa rabiyar fadañ su da tsofaffi kawayen ta .

“Marka magana nake miki ….” Najan Isubu ta sake cewa da marka. Cikin muryar ban lallashi da neman afuwa.

“Yo ai shiru nayi ki tsara yadda komai zai kasance tunda jikar ki ce. Ai sai yadda kika ce.”

Najan Isubu ta dan kakaro yake kawai. Ta juya ta kalli umma hadiza da ke tsugunne daga gefen wata kwalla .

“Haba ni na isa? Ni din gaba da shirme, Ai abunda kika yanke dole abi shi Marka… Kawai dai so nake ki duba zancen Na’Ateeku a mizanin tunani. Sam Na’Ateeku ba tsaran auren Waheedah ba ne marka.”

“Sannu. Nace sannu zabiya mai dalilin aure. Ita din wacece da har zaki ce Na’Ateeku ba tsaran aurenta bane iyye? Fin karfin sa tayi? Ko kuwa usuli ta fi sa. Allah na tuba astagfirullah Na’Ateeku kaf unguwar shurah akwai wanda ya ko kamo dan yatsan sa ne a usili? Mutimi dan mutunci da dangi masu dattako. Kar ki manta kakan sa da ya haifi gyatumin sa shine mai unguwar shurah. Sannan mahaifiyar uwa ta sa kakanta kani ne ga dagacin fandau., Sannan kanin sa da suka fito ciki daya chiyaman ne ke kanki kinsani. Sharbacecen kwaltar data miqe sambal ai shi yayi mana. Ya kuma kawo tuqa tuqa (borehole) Da haqa rijiyoyi. Bacin nan shi kansa mai rufin asiri ne. Shago shaqe da kaya na kayan masarufi. Sannan ke kanki kinsan yanada shagon chajin wayoyi da sayar da kati. Ki gayamun tsakanin shi da ita wanene ya kere wani? Na’Ateeku duk yar daya tsayar a unguwar nan yace yana so wallahi auren sa zatayi. Iyayenta Kuma su zuba ruwa a kasa su sha dan farin ciki , Aikin kawai.”

Marka ta karasa fada hade da hambale taliyar da ke cikin hannun ta . Najan Isubu ta sauke katuwar ajiyar zuciya. Ta juyar da kanta ta hango Waheedah dake tsaye a bakin kofa hawaye daya na bin daya . Tausayinta ya sake dabaibaye zuciar Naja. Cikin sanyin jiki da muryar roko ta sake cewa da marka,

“Duk abunda kika fada hakan yake Marka, Ban musa ki ba. Na kuma san kauna ce tasa kikeson ki hada auren nasu. Sai dai abunda nakeson cewa shine, Na’Ateeku yayiwa Waheedah girma Marka. Wallahi zaa cuceta idan har aka aura mata shi. Dansa na biyu Hashimu fa satin baya ya kara aure. Mata ta 3. “

“Sai akayi ya ya? Ai dan arziki shi yasan abun arziki. Yadda matan sukayi yawa ai dama kamata yayi maza su ringa aure su , Su cike gurbi. “

Najan Isubu ta sake gyada kai kafin ta zauna daga gefen Marka.

“Marka…. Rayuwar auren daa da yanzu ba daya bane. Tamkar yadda kukayi rayuwar auren ku da tamu wallahi ba daya bane. Hakama yanzu wannan zamanin ba a irin auren nan Marka. Zamani yazo da sauyi.”

“Ni fa ban gane abunda kike nufi ba Najaatu. Gwara ma ki dena ‘babaatu. Ahto!” Ta karasa hade da nanawa cinyarta duka.

“Abun nufi yanzu zamani ya kara wayar da mu. Ciwukan yanzu a baya baa yi su ba. “

“Uhmm Hu’uhm…” Marka ta numfasa tana gatsine gatsine.

“Allah Marka. Na’Ateeku bakiga yana da yara hudu ba marasa lapia shima.?”

“Bangane ba.. Yo sai me? Ba Allah ne ya doran su ba. Ina ruwan auren su da wahidin ya hadu da gamayyar rashin lapiar yaran sa?.”

“Ina nufin Na’Ateeku a dauke zancen ya haifeta da sauran su. Abunda nakeson ce miki shine. Shi ma Na’Ateekun yana dauke da kwayoyin cutar sikila. Kamar dai yadda su Kamalu da Najeeb ke fama da ita.”

Marka taja dogon tsaki data saurari karshen zancen Najaatu. Cikin takaici tace,

“Banji ba, Ban kuma gani ba. Karki manta da sherri dan aike ne, Dik inda yaje zai dawowa mai shi… Sannan ni me sunan Malam (Na lado) Bayada wata cuta.. Domin idan da yana da ita da yaran wajen sa’adatu ba sa yi lapia ba. Ita kuwa uhm uhm Hadiza, Da cutar ta tayi guzuri. Aka liqa masa ita ya aure. Ashe lullube maganar cutar jikinta sukayi. .”

“Kayya Marka ki dena cewa haka dan Allah .. Banda ishasshen ilimin da zan buda miki komai yadda yake. Amman Allah ya kai mu sati na sama. Wata kungiyar wayar da kan jamaa kan hanyar da zaa kula kar a fada halin qaqanikayi na ciwon sikila zasuyi taro. Da yardar Allah kuma dukkanin mu zamuje. Saboda har gwajin jini za’a yi ko kanada cutar duk zaa sanar maka. Hakama idan baka da ita.”

“Kingama?”

“Kiyi hakuri Marka.”

“Baki gama ba kenan. To kici gaba idan kin gama se ki tashi ki koma inda kika fito.”

“Kiyi hakuri Marka. Ni kawai so nake ki janye zancen ki…”

“Aure babu fashi…”

“Nalado ka sa baki dan Allah. ” Najaatu ta dubi nalado dake gefe yana katsar ruwan dake kasan tukunya na taliya.

“Me zance Naja..?” Ya amsa ta hadi da lashe bayan hannun sa.

“Yanzu ba zaka tausashi zuciyar marka ba ta janye zancen nan? Haba dan Allah.”

Malam Nalado yayi shiru bai ce komai ba.

“Aure babu fashi. Yace dama inde zuciyar sa ta aminta da ita. To fa ko kayan daki yace shi zai yi. Ita kadai za a wanke akai. Saboda Allah meya fi wannan karamci? Na’Ateeku kyakkyawa da shi , Sambalele jazur da shi . Kina ganin matansa kowacce da kayanta maya maya. Sunyi ‘bundun da su.. wallahi ance ba yunwa agidan sa. Duk sallah sai ya dinkawa matan sa turame maya maya. “

Waheedah dake labe tana sauraron komai. Kasa jurewa tayi. Dan kukan da take rikewa ne ya kufce mata ya shigaa sharara a idanunta. Cikin rawar jiki da baki ta fita tsakar gidan. Ta sukwane agaban Marka tana faman rokonta.

“Dan Allah Marka kiyi hakuri. Ki barni na cigaba da karatu na. So nake na zama ma’aikaciyar lapia Marka. So nake na bawa harkar lapia gudunmawa Marka. Dan Allah kar ki mun aure ki bari na cika burina. ” Ta karasa hade da riko kafafun Marka. Hawaye sai dalala yake daga idanunta.

“Matsa kafin na hamb’are ki. Me sunan Malam kana jin maganganun da tsageriyar yarinyar nan take faada….?”

“Laàa. Ke yanzu Waheedah Markan kike gayawa haka?Uhm tab. Lalle. Kokari.” Cewar Inna Sa’adatu matar Nalado ta biyu, Mahaifiyar su Zainab da su ke uba d’aya da su waheedah…..

FARHATAL QALB

FARIN CIKIN ZUCIYA

ZAFAFABIYAR2022

❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????

ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA

Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?

Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane

????????????????????????????

YA KUKAJI SALON MASU KARATU?

YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button