JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata biyu abubuwa suka zama tarihi akaci gaba da cudawa kamar yanda aka saba kowa yasa abinda yake gabansa a gaba Rasheed ya koma aikinsa gabadaya sun ajeshi guri guda a Lagos inda kullum tunaninsa zuciyarsa da ruhinsa yake Mali gashi tun a farkon da abubuwa suka lalace da Meenah ta rinqa kiransa yayi block na numberta itama tayi block nasa koya nemeta baya samunta wannan tasa dole ya nemi sabon layi dal saboda zuciyarsa taqi sabawa da rashin sauraro da jin abinda zuciyarsa take muradi saidai rashin saar da yayi daya Kira sai yaji layukan dukka a kashe girman kansa na masifa ya hanashi tambayar wani cikin yan’uwansa layinta yabari akan cewa idan ya koma yasan yanda zaiyi ya sata a wayar Mom.
Hakan kuwa akayi bai iya hqrn wata biyun da yayi niyyar yi a Lagos ba ya dauko hanya ya taho Daura bayan ya huta da dare suna hira da Mom a dakinta tanayi masa fadan zamansa haka yayi murmushi yace “mom kamar akanki nake duk kinbi kin damu nayi aure” jinjina kai tayi tace “to ai Rasheed nidai naga cikar kamalar mutum shine hade kansa da iyalansa guri guda kai Kuma na rasa inda kanka yake kunqi ku daidaita da yar’uwarka Meenah Kuma ka kasa samo madadi jiya ma Baffanmu yakirani yake tambayata akan lamarinka da Meenah ance mata aure tace karatu ance ta dawo hannunka tace har abada kaima ya tuntubeka kayi masa shiru wai meye yake faruwa ne”

Goge gumi yayi ya gyara zamansa yace “ni bawai Meenah ce bazan dawo da ita cikin rayuwata ba aa Mom abubuwa ne sun kasa gogewa a mind dina Kuma na fahimci kamar itama ba nine a gabanta ba yanzun” murmushi Mom tayi tace “hakane bakai ba aure ne ma bakidaya bashi gabanta so Amma idan kaje zaku iya daidaita kanku” shiru yayi yana nazartar kalaman Mom tace “zanji dadi idan hakan ta faru Rasheed Meenah tanasonka kanason Meenah ga yaranku guda biyu baikamata ku Bari shaidan ya raba kanku ba babu wanda ya isa cikinku ya canza wannan qaddarar kama godewa Allah da rabon Muneefah bai kasheka ba Rasheed rabon ya mace zafi gareshi shiyasa kullum yanada kyau karinqa yima kanka addu’ar Allah ya rabaka da auren mace me yayan wani a cikinta duk son da kake mata idan rabon nan ya yunquro to sai dayan biyun ta faru kodai a rabu ko Kuma a mutu”
Jinjina kai yayi jikinsa ya qara sanyi abinda Kareem yayita qoqarin fahimtar dashi kenan ya kasa fahimta yau kam ya gane Kuma ya fahimta wayar Mom ya dauka ya fice daga dakin nata ya shiga mota ya nufi gidansa ya shiga ciki Saida ya dangana da dakin baccinsa ya cire kayansa ya fada bathroom yayi wanka ya dawo ya kwanta gabadaya dakin manyan hotunansa ne shida Meenah saina yaransa Sarki da Muneefah ya zubawa hotunan idanu a fili yace “lkc yayi da yakamata da dawo da farin cikina” wayarsa ya dauka ya Kira Abokinsa Kamil suka gaisa yace masa “cikin satinnan kana free ne?” Amsawa yayi da “eh” yace “ok zamuje Mali ne jibi” bai boye masa komai ba khamil yayi dariya sosai yace “tsohuwar zuma kishin ya gushe kenan?” Ya lura tsiya ya shirya yi masa don haka ya kashe wayar ya dauki ta Mom yanabin contact din ya lalubo number ya danna kira lkcn tana sallar Isha Muneefah ce tana wasa da wayar ta danna tana gwarancinta yayi murmushi yace “daughter bakin yazo kenan?” Nan sukayita shirmensu da yarinyar bayan ta idar ta karbi wayar tunaninta ko Muntaz ne ko Urwat tace “surutu ke gareta Mamana bata rabo da rigima” ajiyar zuciya yaja a hankali taji ya sauke numfashi yace “hakan yanada kyau ba lallai tayi kamar na Mom dinta ba” qamewa tayi a gurin jin muryar da batayi zato ba nandanan ta rinqajin zuciya na ayyana mata ta kashe wayar tana Shirin gimtse layin taji yace “ranar juma’a idan Allah ya amince zan shigo qasar ki fara Shirin zama amarya domin bazan kwana a garin nan ba saidake matsayin matata kamar yanda yake rubuce a allon qudura duk wanda yayi karambanin shiga wannan gonar ma saiya fice da kansa ko Kuma dole ta fitar dashi”

Murmushi tayi tace “tunaninka ne yake baka hakan nikuma inajin a raina qaddarata tayiwa taka nisa Ya Rasheed so don Allah kada mu wahalar da shari’a kayi zamanka a inda Allah ya ajeka idanma matsuwa akayi nayi auren naji zan fitar da miji tsakanin yau da gobe Amma kaikam nagama aurenka” murmushi yayi yace “au haba da gaske Kuma kikeyi? To ai kin manta da Abu daya ni idan nayi niyyar aiwatarwa yuwuwa yakeyi Meenah badon kanki da kaina ba don rayuwar yaranmu nayi niyyar abinda na furta saboda haka kada ki manta gyarane kawai Amma kedin matata ce domin da igiyar aurena uku akanki aka jingine aka dauranki wani…. Oh God banaso nake tunawa fah ki share kawai sainazo”…….
Daga haka ya gimtse wayarsa yabarta da sakin lebe lallai wannan yazo da izala mara gemu dole ta takansa birki don bataji a ranta wannan tatsunniyar zata yuwu ba.

Ranar kwana tayi tana jujjuya kalamansa da safe kuwa bata sanar da kowa ba ta shirya nata ya nata ta gudu gidansa Aunty Kharimatu batare da kowa yasan inda ta tafi ba Kumbo Hami ta riga tasan me ta gudarwa saboda sunyi waya da Mom a haukan ma da takeyi tuni magana taje ga kakanta ya Kuma amsa har anyi duk abinda zaayi an wucce gurin da sahalewar Mai Martaba.
Tana zuwa gdan Aunty Kharimatu suka lalace da hira har dare tayi kwanciyarta dake mijinta matafiyi ne washegari ma sukaci gaba da harkokinsu har magrib batada niyyar tafiya suna falo suna cin dambum nama sukaji sallamar Jabir gabanta ya Fadi ya shigo yanayi mata dariya yace “girman kujera aunty babba kinada baqi a waje fah” harara ta zabga masa tace “munafuki suwa kak debomin?…..” Bata gama rufe bakinta ba sukayi sallama suka shigo idanunsa na kanta ta kuwa hadiye fara’arta ta hade rai ta miqe ta nufi wani daki suka dubi juna shida Khamil sukayi murmushi suka zauna Aunty Kharimatu nata zolayarsa fadi takeyi lallai ango kasha qamshi ashe da gaske kana tafe”
Shafa sumarsa yayi Yana cire hularsa yace “wlh Ina tafe nazo na dauke matata mu tafi nagaji da zaman gwaurontaka” harararsa tayi tace “aa kuwa baka isaba wannan abu Babu shiri nifa sai dazun Kumbo ke fadamin Shirin da akayi nace halan ma waccan uwar taurin kan bata sani ba don ko dazun Saida tace batada muradin wani aure” numfashi ya sauke yace “tasan komai ai dama barinta nayi ta huta saboda rayuwar batada tsayi Amma an fuskanci qalubale da suke buqatar dogon hutun brain”………..

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta baney ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/27, 9:03 PM] Oum Hairan: Dariya Aunty Kharimatu tayi tace “ah lallai to ubangiji ya kade fitina ya daidaitaku sai aje ayita hqr koda yake tsohuwar zuma ce Babu wani qalubale qalaunku zaku zauna wuyarta ku daidaita kanku……” Aunty Kharimatu bata gama rufe bakinta ba Juhud ta fito dauke da Muneefah da niyyar ficewa daga gdan Muneefah na ganin Rasheed ta fara zamewa a jikinta tana Kiran Dad sweet Dad biscuits….” Murmushin gefen baki yayi ya miqe ya nufi Meenah da takai bakin qofa yasa hannu zai karbe yarinyar ta juyo a fusace cikin bala’i tace “inada tabbacin bakada wata alaqa data wucce wan mahaifi gurin Muneefah domin kuwa qaddararta me qarfi ce itane ta sanya abubuwa da yawa suka faru a qarshe dai nida Kareem muka Samar da Muneefah saboda haka ikona ce”
Sakin yarinyar yayi yayi baya jikinsa na daukar sanyi yanajin saukar kalamanta na dukan zuciyarsa, batare da wata damuwa ba ta fice ta jefa yarinyar da keta kuka a mota ta shiga ta figi motar a mugun guje ta fice a harabar gdan tabarshi tsaye kamar dashe Yana qara maimata kalamanta, Khamil ne ya dafashi yace “nifa Ina mamakin yanda dangantaka tayi tsami haka tsakaninka da Meenah meye ya farune mutumin bakada dama ne fah qila Kaine ka tabo zuciyarta” janye hannunsa yayi yace “koma mene ban cancanci wadannan munanan kalaman akan yar qanina ba Amma zan gwada mata haihuwa ce tata nafita qarfin iko” Yana fadin haka ya fice Yana huci ran maza ya baci Jabir ne yazo yajasu suka nufi gda ganin motar da ta hau ta fito yasashi tabbatar da gidan ta dawo, bai shiga cikin ba ya nufi sashin baqin ya cire kayansa ya zauna yana fitar da iska me zafi zuciya na raya masa meye zaiyi ya rama wannan wulaqancin da Meenah tayi masa?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button