HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Jin tace sai ta kammala girkin Rana Kuma a yau zata dawo Kuma itama hutawa zatayi yasa tace ta je amnan Kar ta Kai dare , ta jeho Mata kud’i d ta fito dashi daga Aljihun bayan jakar ta ,tace tayi kud’in mota dashi 2k ne, ko tsaya sauraron godiyar indon batayi ba ta yi gaba ..
.

Indo bin kud’in tayi d kalo Tana Mai Jin zafin jeho Mata kud’in da tayi ba Abin tayi fushi dashi ba , ko kayan miya ta saima Inna zai amfane ta sanan ta tsuguna ta kwashi kudin ‘yan dubu guda 2 tace Allah y shiryemu baki d’aya a fill Dan takaici Dan kowa Yana neman Shirin ubangiji …

Bayan Indo t gama komai ta Adana musu ,ko sallama batama momyn su Noor ba ta fice Tama Mai gadi sallama zataje gdn Inna ya Mata adawo lpy ta fice d haushi da takaicin NAWAL …

Nera hamsin ce ta kaita kasuwa ta siyo ma inna kayan miya da dankali Mai Zaki na hausawa da d’anyan rogo tasan Inna d son rogo d gyada d’anya d aya kwano kwano tasai Mata d ledar k’ullin gyada d ayar sanan ta nufi gidan inna cike d murna

Ko da tayi sallama ,tuni Inna ta cefe muryar ta Tana Mata oyoyo ,jikin Inna t fad’o Tana cemata sannu” Inna tace inkinka karyani Naga me d’aura Ni agarin Nan , indo tace Ni zan d’aura ki …

Nan Indo ta gaishe ta ,ta Bata kayan d ta siyo Mata harda su ayar ….

Inna tace har anyi Albashi NE ?

Indo tace aa mmn su Noor ce ta bani dubu biyu shine nasiyo Miki har su Aya nasan kina kukulawa yara suna zuwa siya gama kayan miya Kya kwana biyu baki siya ba ..

Inna tayita samata Albarka har mmn su Noor din ma kamar Tana Jin ta ….

Indo Ce ta mik’e ,tace Inna zani shagon dumbulun in siyo filawa Dan kwad’ayin wainar filawa nakeyi wlh , kinada yaji Mai dad’i ko Inna?

Inna tace aa kinsan ba cin yaji nakeyi sosai ba tun Wanda Kika dakamin d’inan d y kare ko neman shi ban k’ara yi ba , Kune masu bakin cin yaji ki siyo harshi sai n daka Miki ke Kuma ki fara tuyar wainar d sauri t fita zuwa shagon Tana to Inna ta …

Bayan t siyo tare suka shigo da k’awar ta nawara , ta ba inna yajin d d’ata d suka siyo Mata ,ta karba Tana shi musu Albarka …

Nan d Nan suka had’a gawayi suka Fara tuyar “nawwaran na tuya Indo na daka yaji sukace Inna t huta tanata cin datar ta Tana gyara ayar ta d gyad’a Dan yanzu zata soye su ta kukula Abin ta dama Tata ta kusa k’arewa …

Suka Toya wainar su sukaci sukayi kat har inama sanan suka tafi gdn su nawara ….

Nawara kawar Indo Ce Basu Jima d had’uwa ba ,ita nawara CE take son Indo d kawance tun Indo Bata kulata sai d Inna ta Mata fada sanan take kulata har suka Fara Shirin yanzu …

Iyayen nawwara sunada Hali ba laifi sunfi karfin komai ..

 

*Maman shaheed*????
[12/28, 7:04 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`
I

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na shatakwas_

Iyayen nawwara nada Hali ba laifi sunfi karfin komai a gidan su ,sunada rufin Asiri ..

Koda sukaje gdn d Indo ,yaune shigan Indo gidan na farko ,suka gaishe da ummah su nawwara ,ta karbi Indo cikin sakin fuska d fara’a Indo ma nata girmamata ,daga Nan d’akin nawwara suka shiga sunata Hira ,yau Dadi y kasheta gata ga Indo acikin gidan su …

Sunata Hira kamar sun shekara ,har nawwara take cemata Indo sunanki fa Aisha Amman kike amsa Indo …

Indo tayi dariya tace wlh Nima dai yanzu bana son sunan innace t ke kirana dashi shikenan ‘yan gari suka Kama …

Nawwara tace to wlh daga yau Aishatu zandinga ce Miki ,Indo tasa dariya …

Sunata Hira ganin yadda nawwara take bala’en son ta yasa ta Bata tarihin Rayuwar ta d Wanda tasani d wayon ta d Wanda inna ta sanar Mata kaf ..

Nawwara har kuka Tama Indo ,tace Kuma ta Dena Aiki a gidan su Noor ,Indo tace Sam dashi take taimaka ma Inna ..

Nawara ba yadda batayi ba har tace zata dinga koya Mata d’inki sai ta dingayi Dan ta rike kanta ,Indo tace zata koyi dinki Dan tanaso dama can Amman ba yanzu ba ..
Itako dama telace dinkuna takeyi na garari .

Haka nawwara ta hak’ura , har indon tace zata tafi , nawwaran ta rakata har gidan Inna …

Nawara tafi Indo sanin wasu abubuwa na rayuwa zata d’an girmi Indo kad’an sanan ta fita wayo da sanin duniya me take cikin Dan kanta awaye yake bakamar Indo ba itama ba irin wayewar Nan ta ‘yan duniya bane ,aa ta sanin darasin tafiya da zamani Dan tanada Nutsuwa d hankali g ilimi Dan ta gama secondary school d’in ta tanason cigaba Amman saurayin ta yace sai dai ta Bari in sukayi Aure sai taci gaba a gidan sa …

Bayan Indo t dawo gdn Inna ,yamma tayi lis ,Inna tace tazo ta tafi kartayi dare a hanya tunda da d’an tafiya tsakanin su Dan sai an hau mota ..

Cikin kewar inna ta Mata inna sallama t mik’a Mata ragowan kud’in hannun ta ,Inna nata shi Mata Albarka na mota kawai ta Bari ta d’ebo gyada d Aya zata tafima d Noor d Haneef har d’atar da tasaimusu dazu t d’auko Tama Inna sallama ta tafi …

Tana zuwa bakin layin su ta Sami 3cycle sai gidan su Noor …

Koda ta shiga , Tama Mai gadi sannu d gida , y amsa ta wuce parlour .

Tana sallama Noor da Haneef d gudu suka taso suka Mata oyoyo suna tambayar ta Ina taje sunata nemanta …

Momyn su ko baki sake take kallon su har dadyn su d be Jima d shigowa gidan ba, da gani Dan ko takalmi be cire ba …

Momyn su cewa tayi wani sabon salo ! Tayi mamakin Dan Bata Saba ganin haka ba …

Noor ce tace wlh aunty Indo d bakya Nan gidan ba dad’i ……dadyn sune y bi momyn su d wani irin kallo Mai cike d tuni d nuni agareta Dan duk sunji Abin da Noor ta fad’a ..

Jin haushin kalon d ya Mata yasa ,tace dan uwarki da kin sani da binta kikayi kuka tafi marakunyar yarinya maga naniya …itako Noor ta turo baki alamun taji haushin zagin d uwar ta Mata Dan basa zagi a gidan Kuma Indo tace musu Mai zagi za a k’onashi a wuta ……Aiko ganin ta turo Mata baki momyn su ta taso d sauri t d’aga hannu zata mareta ……..safwan y Kama hannu y wugar gefe yace ko kusa ko Alama karki sake ko a bayan idona ki dakesu akan rashin dalilin komai …yarinya Kuma gaskia ta fad’a ai …..

Cikin mamaki NAWAL tace , kana ganin Tana turo min baki ? Ka hanani hukunta ta ka nuna Mata rashin kunya abunyi ne?

 

Yace to meye acikin turo baki? Nawa ke Kika min a ‘yan kwanakin Nan? Kuma me Kika koya Mata zagi yanzu fa ? Ko kinmata zagin d Kika Mata Alhalin kinsan basa zagi na hanesu dashi? Kike karya min doka…

Kuma karki Kara cema yarana marasa kunya ,Kar ki k’ara zagin su bazan yadda d haka ba ,kema halin zagin d Kika aro kiyi gagawan mayarma duk Wanda y baki Dan be Sami karbuwa ba ,yarana basa zagi bantaba ji ba sakamakon Basu Sami training d’in shi ba a gidan Nan kema Kuma ba halin ki bane shiyisa nace aro shi kikayi ,Dan haka ki kiyaye ,in ba haka ba zamu samu sabani nida ke for d first time acikin Rayuwar Auren mu..

Gargad’in ya shigeta Dan haka ,a hassale tazo ta bangaje Indo saida suka kusa fad’awa jikin safwan d’in Indo d Noor d suke manne da junan su ..

Safwan d’in nne y kamo kafad’an indon kafin ta gama fad’a Mai badan ya Ankara ba ,da jikin shi zasu fad’o gaba d’aya , Yana Ankara yayi saurin sake indon , tare d ta’auwizi (A’uzubillahi minashaid’anu la’enun rajim) k’irjin shi na bugawa da sauri da sauri ,a hankali yake sauke numfashin shi …

Ganin Abin ba sauk’i d’akin shi ya wuce Dan samun nutsuwa Mai inganci atare d illahirin jikin shi ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button