BidiyoLabarai

Bidiyon Wata ‘Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe ‘Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3 Suna Tare

Wata ‘yar Najeriya ta dauki ‘yar aiki mace wacce ta kwashe watanni uku tana yi mata hidima, sai daga baya ta gano abinda ya firgita ta akan ta.

Matar ta sha mamaki bayan gano ashe katon namiji ne ‘yar aikin nata inda ta yi masa bidiyo tare da fallasa shi a idon duniya don kowa ya sani.

Nan da nan mutanen da suka ga faruwar lamarin ta hanyar duba bidiyon ‘yar aikin suka dinga tsokaci iri-iri kowa da nasa ra ayin.

Ki kwatanta daukar ‘yar aiki kawai sai ki gano cewa ta daban ce da wacce ta bayyana miki a zahiri, to irin haka ne ya faru da wata ‘yar Najeriya.

Matar wacce sunanta bai bayyana ba ta gano cewa wacce ta dauka aiki daban da wacce take yi mata aiki, don namiji ne ba mace ba.

ourtalkroom ta wallafa bidiyon yadda matar ta kunyatar da mai aikin inda tace sai da ta kwashe watanni uku tana yi mata aiki sannan ta gano gaskiya.

Ya kunyata matuka a bidiyon Ya sha kunya a bidiyon, inda ka ga yadda dan aikin yake zaune a kasa sanye da rigar mama da wani wandon jins.

Ya sanya hular gashi kuma. Daga bisani aka sanya hadimin a cikin abin hawa wanda alamu suna nuna kamar ofishin ‘yan sanda aka zarce da shi.

Abin ban mamakin shi ne yadda dan aikin ya kwashe watanni uku yana aiki ba tare da asirin sa ya tonu ko kuma ya yi kuskuren da zai sa a gano shi ba.

Ga bidiyon a kasa:

Daga Hausa Legit

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button