KUSKURE Complete Hausa Novel

Gudu gudu taje ta fesa wanka tayi kwaliya ta saka wata mayar atamfa Mai yellow d orange d’inkin doguwar Riga d’inkin ponix yayi Mata kyau ta kashe d’aurin “in kin Isa kena kiyi” Bata cika fuskar ta d kwaliya ba Amman tayi kyau sosai …
Ta yi sallah ta zauna zaman jiransu Dan ko Abinci Taki ci wai sai sunzo ..
,Bayan minti 57 sai Taji Ana taba k’ofa ,atunanin ta safwan NE ta kwasa d gudu sai d’akin ta ,shiru bataji anshigo ba anata nowking sai ta tuna d su Noor d sauri ta tafi tace waye?
Haneef yace ,mune Aunty Aishatu!
Gudu gudu ta bud’e k’ofan , Tana oyoyo my Haneef nd Noor !
Tana budewa hassana d ussaina suka sakar Mata murmushi Mai kayatarwa ta mayar mu d sannun ku da karasowa ,ku shigo, Noor Haneef ,Janna tuni sun rufeta da Runguma da kyar suka saketa ta mik’e suka shigo …
Duk a falo Kan 4seater suka zube ussaina na wash!
Hassana tace dubeta sai kace a kafa mukazo !
Aishatu tace aunty Ussaina kin gaji NE? Ussaina tace eh wlh a napep pa mukazo Tana kalon hassana !
Aishatu tace sannun ku to , suka gaisa tanata tmby Ina Ammy d Alhaji?
Sukace suna lpy suna gaishe kima ,tace Tana amsawa …
Bayan ,su Noor sun gaishe ta ,ta janyo su,tanata ce musu tayi missing dinsu har Janna ,suko yau murna kamar suyi hauka Dan Dadi …
Aishatu tace ga Abinci ya Kamala fa ,ku yake jira kawai !
Hassana tace ,to su Janna ga food can ,Haneef d gudu y nufi dining…
Ussana ta bisu ta zuzuba musu ,komai sunata murna sunaci suna Santi ,hassana ma ta mik’e Aishatu ma ta nufi wajen kowa y zuba iya cin shi ,ussaina nacewa nifa sai na Kara yaushe Gamo ?
Sukaci sukayi Kat , juice din ma b Wanda yasha ,Bayan sun gama ci ,suka dawo kujera kowa na Mike ciki …
Sunata kalo ,Baki baya motsawa ,Aishatu ta tashi ta nufi kitchen ta d’auko musu iloka dama tayi ta ajiye Dan su Noor ,ta ajiye kowa y d’iba Ana Sha Ana Santi har ussaina ta nemi akoya Mata , Aishatu ta koya Mata kuwa anata dariya…
Suna cikin badalin ilokar ,safwan y Kira hassana a waya ,yake tmby sun karaso?
Tace mai eh gasu ga Aunty Aishatu su Noor se murna suke ta kashe mu da kayan Dadi ….
Yaji dadin maganar hassana ,yace abashi Aishatu , hassana ta Mika Mata waya ,jiki ba kwari ta karba ….
Hello dadyn su Noor!
Yaji dadin sunan y lumshe Ido ,yace naam ,Ashe bakin ki sun gama so ?
Tace eh ,gamunan muna tare abin mu !
Yace yayi ,kyau shine Kika musu hidima d zan fita Baki tmby komai ba?
Tace ai Akwai duk wani Abu d zan bukatane acikin gidan ,
Yace yayi kyau , nagode ,yace Ina Noor ,taba Noor waya ,Tana karba ta Fara bashi lbr sunzo gidan Aunty Aishatu Kuma ita bazata koma gidan Ammy ba ,dadyn su yanata Mata dariya ,akaba Haneef shima y Fara nashi surutun harda lisafa Abin d sukaci ,daga baya akaba Janna ta dinga ma su Noor dariya ,tanacewa sai sun koma gidan Ammy tare ,daga karshe hassana t karbi wayar sukayi sallama d shi ….
Ana gama wayar ,saurayin ussaina y kirata ta d’auka t gudu d’akin Indo inda t kwana Tana soyewar ta d saurayin ta ,su Hassana d Aishatu nata Mata dariya ….
Suko su Noor anata tsale tsale Ana wasa hankalin su kwance …..
*********
Nawara tanason magana d kawarta Amman Abu y Gaga ,gashi tanason zuwa hydar yace t Bari ko sati suyi Mana kafin ,shine ta hakura ,Amman suna gogar amarcin su son ransu babu mishkila …..
Inna ma tanata ,Alhinin jijar ta ,sai yanzu take karajin gidan shiru ,Amman Aure y gaji haka ba yadda zatayi sede su bita d Addu’a …
Gidan Safwan ko anata hirar zumunci tsakanin su Hassana d Amaryar yayan su ,b nuna tsana ko kyama hankalin su kwance suke Hira b irin yadda sukeyi d NAWAL da can baya ba ,sukaji Aishatu tafi birgesu t ko ina …
Safwan ne yace
Ne,yace su Bari d yamma zezo y kaisu gida …
Around 5:30 sun gama shiryawa yadawo gidan …
Aishatu b gudu yau tunda Tana cikin jama’a Yana shigowa Noor,Janna ,Haneef suka cacimeshi suna mishi oyoyo ,y dinga dagasu Yana Basu kiss a kumatu da kyar suka barshi y zauna ….
Ga gajiya y d’ebo ga yunwa ,Dan haka ,kowa yamai sannu d zuwa Aishatu ce ta karshe ,kamar jira yake ya amsa yace dafatan su Noor sunbar Mai ragowar Abincin su ?
Ta yi murmushi tace akwar ragowa ,nayi nayi d su twins su Bari n doramana girkin dare ma sunki ,wai Ammy tace su koma d wuri …
Yace gaskia ne Kam badan na Mata waya bama d basukai yanzu ba ,barin ci nataso mu kaisu ko Haneef ,yace eh Amman mu dawowa zamuyi ko?
Ussaina tace dakai zamu koma gidan Ammy !
Y kebe Baki shi bazashi ba Yana wajen Aunty Aishatu !Noor ma tace haka suna ganin kamar wayo za a musu !
Bayan y Kamala y shiga y watsa ruwa y sauka shiga zuwa blach jeans and red t_shirt Mai d’auke d tambarin polo yayi matuk’ar kyau yace sun shirya?
Janna itama tanata murna zata wajen ammyn ta ,su Hassana suka saka gyale suka d’auki jakar su sukayi hanyar fita daga falon …
Haneef d Noor na makale jikin Aishatu ,yace Haneef bazaku raka su auntie’s din naku ba?
Noor tace Kar Amana wayo abarmu a gidan Ammy !
Suka yi dariya ,yace bame barin ku acan Baga kayanku can antaho d shi ba ,Noor tace ai Akwai wani acan saidai idan d aunty Aishatu zamu…
Safwan y kaleta ,yace kinji rigimamun naki ko sai ku taso mu kaisu base mun shigaba ma sai mu dawo yamma nayi …
Bata d zabi g idon su ussaina a kansu ,ta shiga t d’auko gyalen macht d kayan suka nufi mota …
Hassana ussaina Janna d Noor duk sukayi baya ,Haneef n rike d hannun Aishatu,gudun Kar y Mata magana duk tagabe so suke ta shiga gaban ,Dan haka ta shiga t zaunar d haneef gefen dadyn shi y Cinna hancin motar gate ,sai titi. …
Basu tsaya ko Ina ba sai kofar gidan ammy ,anfara Kiran magriba Dan haka gudu gudu yace ai gaida Ammy zasuzo ,Janna Tama su Noor bye_bye ta shige d gudu Don yima Ammyn ta oyoyo….
Bayan sun tafi ,seda suka tsaya wajen Mai seda fruits suka siya sanan yayi gida dasu ,suna shiga Ana d’auke wuta ,Dan haka y tashi gen,sukayi ciki domin yin sallah Dan har an idar d sallah a masalaci ….
Kowa seda Aishatu ta umarce shi d yin sallah ,Bayan sun idar tashiga kitchen ta Dora musu joluf din taliya d makaroni Wanda yaji kayan lambu d kifi bushahe ,Dan shi zefi Mata sauki …
Ba a jimaba y Kamala ta zubo musu ita d su Noor ,suna cikin ci dadyn su y fito daga shi sai vest d short niker ,jikin Aishatu ne y fara wani iri ganin shi d yafito a haka tun d ta kale shi so1 Bata Kara kalon shi ba …
Kamshin girkin nata bugan Mai makoshi ,se daga baya y Kali shigar shi shida kanshi yaji wani iri ,be sake gaskatawa ba seda yaga Aishatu ta takure sosai ko magana su Noor suka Mata a dakile take Basu amsa ,gudun Kar y koteta y takurasu d yaranshi y tashi y koma y sako jalabiya a Kai ,y dawo shine tad’an saki jiki kadan ,har take cewa Ashe kasan abinda kayi wani kato dakai zaka fitomana tumbir kawai Tana mita cikin zuciyar ta..
Ba left ganin su Noor tad’an saki jiki ,shima hakan yamai Dadi ,har y umarci d in Akwai Abincin t zubo mai kadan in sun gama Amman tace to!
Bayan sun gama ,ta karana su Noor ,ta zubo mai shima ta Mika Mai …
Bayan duk sun kamala ta gyara wajen dasu Noor suka Bata ….
Taje jakar d aka kawo musu ta duba taga Akwai komai d zasu bukata Dan tafiya school gobe ta shirya musu su a guri daya ,ta d’auko musu kayan canji t canja musu ,suna zaune sunata kalo …
Shidai goga time to time Yana latsa wayar sa ,ba wata Hira bace tsakanin shi d ita Amman Noor d haneef sukan hadasu cikin magana suyi hirar Dole …..