NOVELSUncategorized

KWARATA 10

???? —— 10

             Lallai idan nayi shiru da maganar nan ban fad’awa mahaifin Dikko ba nan gaba ya gano wani abu lallai zan fuskanci baraza na dagani har mahaifina, kila ma ya kora mu, ya zama wajibi naje na fad’a masa halin da Dikko yake ciki, in yaso zaiyi bincike abinda ya had’ashi da ita yarinyar, Umar yake magana duk abin yazo ya dameshi yana mamakin abinda ya had’a Dikko da mace har take fad’ar zata gauraya dashi…..


      Dikko mai zafi akan mata, ya akayi ya koma mai sanyi ? Wuta ne mai tsananin k’unar gaske ga duk macen data matse masa, babu abinda ya tsana duniya irin mata, amma wai shine yake godiya akan mace… Wace ce ita ? Miye tsakanin su ne…. ? Kayi shaye sheyenka ne Umar shi yasa ka manta wace ce Sultana…..

         Tsohuwar anguwarmu ta farko na koma, inda Dikko yayi ta siye siyen gidanjen da muke kamawa haya, gida mai sauk’in kud’i na samu na kama d’aki d’aya, bayan na biya kud’in d’aki na tafi kasuwa dan siyo d’an abinda ba’a rasa ba na amfanin yau da kullum.

        Na dad’e sosai a kasuwa, saboda duk abinda nasan zan nema saida na tabbatar na siya saboda ni rayuwata ta duniya babu abinda na tsana irin aro, bana san na takura shi yasa zanyi k’ok’ori na bada k’addarata dan na samu kud’i…….

        Umar durk’ushe a gaban mahaifin Dikko, hada wani hawayen munafirci kanshi a k’asa kamar sabuwar amarya a daren farko, Dady kuwa gaba d’aya yanayin fuskashi ya sauya zuwa damuwa bayan ya gama jin duk maganar da Umar yazo da ita, shi baya hana Dikko yayi magana da mata bane ko wani abu a , a shi baya so dai ya shiga damuwa har wani abu yazo ya sameshi, kuma idan yayi ma Dikko maganar aure sai yace shi yaro ne a bari saiya k’ara girma, ga Umar kuma yazo ya fad’i k’arya da gaskiya dandai kawai a bashi wani abu, wannan fada ce ko kuwa maulace ? Kallon Umar Dady yayi sosai sannan yace kirawo min shi….

       Umar ya kira Dikko yafi so a irga amma bai d’auki wayarshi ba, ganin haka yasa Dady ya fara kiran Dikkon da kanshi, shima bai d’auka ba, jinjina kai Dady yayi tare da turawa Dikko sak’o kamar haka….


        Babana idan ka gama abinda kakeyi ka kirani.

      Umar kuwa yana tashi daga wurin Dady ciki ya wuce inda iyayenshi suke, a gidan su Dikko Umar da iyayenshi suke zama, suna a k’ark’arshin su Dikko ne, kuma Umar shine mutumin da yayowa Bello jagoranci aka kawoni wurin Dikko, ni da dare na ganshi amma Allah yasa na ganeshi duk da jakanci na, amma shi ya kasa ganeni kwata kwata….

      Umar bai dad’e da tashi ba kiran Dikko ya shigo cikin wayar Dady….. Da farin ciki Dady ya d’auki wayar tare da cewa ina ka shige ne ? Ko kana tunanin surukata ne ? Ya fad’i maganar cikin sigar zaulaya, d’an gyaran murya Dikko yayi tare da cewa barka da yini, ya gaishe da Dady dan kauda waccan maganar…..

      Ansawa Dady yayi suka gaisa cikin farin ciki da soyayya irin na d`a da mahaifi. Bayan gaisuwa Dady ya tambayi Dikko labarin yarinya da Umar yazo mishi da ita, miye tsakaninsu kuma miye gaskiya labarin …? Dady ya k’ara da cewa banso soyayya tayi min wasa da rayuwata, domin duk abinda ya tab’a hanci ido ruwa yake, tou duk abinda ya tab’oka ni ya shafa.

    Me ya had’aku har take zaginka ? Gyara zama Dikko yayi sannan yace ba komai, kuma ma ai bata zageni ba Dady, duba Babana yaushe ka fara b’oyemin abinda ya shafeka ? Ni zaka juyawa baya ? Me zaka b’oyemi bayan kasan ni bana b’oye maka komai ? Fad’amin abinda ya dameka muyi damuwar tare…..

       Shiru Dikko yayi na wasu mintoci yak’i yayi magana, Dady yace kai nake saurare Babana kaji tsoron Allah ka fad’amin abinda yake damunka idan har kana so nayi bacci a daren yau…..

       Har yanzu Dikko baiyi magana ba kuma bai kashe wayar ba, Dady ya k’ara cewa ka daiji tsoron Allah ka fad’amin gaskiya k’arya ba halinka bane kuma masu sunan manya basa fad’ar abinda ba gaskiya ne ba, gaskiyar mahaifina da amana irin tashi yasa na saka maka sunanshi saboda kwad’ayin kaima ka zama mai gaskiya da amana kamarshi,  kuma ina fatan ka zama mai adalci ko bayan bana duniyar nan….. Ina so ka zama jigo ga “yan uwanka ka tausaya musu ka karb’i damuwarsu ka sakasu farin ciki karka barsu suyi kukan rashin mahaifi, inaji a jikina bazan dad’e duniya ba, nayi kuka kuma na shiga damuwa rashin samun d`a namiji, sai kuma nayi farin ciki a lokacin da Allah ya azurtani dakai…

      Idan kaga na damu da nasan abinda yake damunka saboda in d’oraka hanya idan naga zaka sauka daga saman layin gaskiya, ina fad’a maka tawa damuwar ne dan ka gane abinda duniya take ciki.

Me ya had’aka da yarinyar mutane take zaginka ne Babana ? Cikin kame kame yace Dady nifa ba zagina tayi ba, kuma ma yake maganar cewa tana min rashin kunya a ina akayi haka ? Ni ba ruwana da ita sab’ani ne kawai muka samu kuma ma ai abun ya wuce….

        Saidai inayin mafarkinta idan ina bacci, inajin damuwa ne idan na tuno da ita, sai kuma inji kamar tana kiran suna na wani lokaci, kuma sai inji kamar tana tare dani, inajin kamar numfashinta a jikina sai kuma shashshekar kukanta tana dai zuwa min sosai a ranaku da dama, shi yasa ma nake d’an tunani, amma bayan haka banda wani damuwa da ita.

      Tou soyayya kakeyi da ita ne ? Dady ya tambayeshi, no ba soyayya kawai dai rashin kunya tamin sai nayi maganin bakin tsiwa, kamar ya dady ya sake tambayar Dikko, shiru Dikko ya sakeyi ya kuma rasa abin cewa.

    Kai nake saurare, Dady ya fad’a, kwashe komai Dikko yayi ya fad’awa dady amma bai fad’a masa labarin wani abu ya shiga tsakaninshi da Sultana ba, kawai dai yace ya sissiye gidajen da suke haya ne, a haka aka tsaya ba maganar yayi wani abu da ita.

      Nasiha Dady yayi ma Dikko kamar yanda ya saba, yace yayi ta addu’a, kuma zasu tayashi har Allah yasa ya manta da labarin Sultana a rayuwarshi, godiya Dikko yayi ma Dady sukayi sallama.

      Haka kuwa akayi domin dai Dady ya mik’e tsaye yasa ayiwa Dikko rok’on Allah dan shi a tunaninshi Sultana aljana ce, ko kuma mayu ce ko tanawa d`ansa asiri ne, dan haka Dady ya tsaya akan k’afafuwanshi saida ya tabbatar Dikko ya manta da labarin Sultana a rayuwarshi sannan hankalinshi ya kwanta………..

        Wannan kenan………..


     *

           { kalu bale gareku matan aure………. }


        Gidan da na kama haya gaba d’aya gidan matan aure ne babu zawara ko d’aya haka babu budurwa idan bani ba……..

        Kowa da mijinta daban babu wacce ta had’a miji da wata, abinda na fuskanta da rayuwar mazauna gidan kowa yanayi ma d’an uwansa kallon hadarin kaji ne, babu wanda yake san kowa sai zazzafar bak’in ciki da jin zafi da gasa da kowa yake nunawa abokin zamanshi ido biyu kunne tsaye babu kunya bare kawaici.

        Gidan babu katsari kuma bashi da saiti kowa yaga dama shigowa yakeyi, sai a tara dandazon taron mata ayita maganganun sakarci da rashin kamun kai, shi yasa zawarun anguwar da “yan mata wanda suka bushe fitilarsu suka maida gidan dandalin sauke lalatarsu.

     Suna da wata d’abi’a d’aya dana lura da ita ta wasan banza, kuma basajin kunyar nuna tsiraici wa junansu, ma’ana kamar irin cire riga da bra a lokacin fira, irin wancan tace amma wance gaskiya kinfi wacce nono, basajin kunya sakin maganganu na sakarci da fallasa sirin mazajensu.

       Duk da ni yarinya ce mai k’aranci shekaru a cikinsu na raina musu wayau gaskiya, kuma na d’aukesu wawaye idan naga dama zan basu shawara kuma idan suka d’auka zata musu amfani, amma gaskiya banga dama ba, haggu zanyi amfani da ita dan ni yanzu ba shiriya nake so ba lalacewa itace na zab’a kuma duk wanda naga zai lalace saina kama mishi ya lalace, dan nayi alk’awari saina kafa tarihi a garin katsina, ina so in zama cikakkiyar karuwar da sai suna na ya shiga cikin sahun “yan iska a duniya, dan bazan yadda nayi karuwanci wahala ba.

      Kujerata na d’auka na nufi k’ark’ashin bishiyar da ake zaman majalisar, ina k’ok’arin kafa kujerata zan zauna wata zawara tace ke Sultana tashi nan ba wurin zaman yara bane ba kinji…..

         Gaba d’aya suka shek’e da dariya tare dayin gud’a, { ayyuri yuri yuriiiiik…. } aka kashe, murmushi nayi tare da ajiye kujerata na zauna, ba tare dana kalleta ba nace dan anyi ciwo an warke ai ba’a ba mutuwa haushi ba, abinda kike takamar an baki nima naci irinshi, tou me za’a b’oyewa ruwa bayan babu inda bai shiga, ansha kuma anyi wanka dashi aikuwa kinga farin wata ba bak’on dare bane ba.

       Duk macen dake wurin saida ta kalleni, murmushi nayi irin na “yan duniya tare da d’aga girare na duka nace muci gaba da zance ai abokin cin mushe ba’a b’oye mishi wuk’a.

         Sama sama dai akayi firar wannan rana babu wani labarin ci gaba da guda guda kowa ya sab’e duk wanda ba gidan yake ba yayi tafiyarshi aka barmu iyakarmu “yan gidan…..

      Bayan sun fashe ne kowa ta tashi ta fara aikin gabanta tunda masu labarin iskancin sun tafi, dan haka sukeyi idan dai ana wannan firar jarabar babu macen dake motsawa, idan kuwa d’anta zaiyi kukan mutuwa bata kulashi.

      Maganar sallah kuwa saidai a mik’ata a jimlace, wai sai an gama zance duniya za’aje ayi alwalla lokacin za’ayi azahar la’asar magrib isha’i, wata ma idan ta makara bata tashi sallah asubahi ba, har gari ya waye tou duk wacce ta fito ta samu an fara fira tou wannan sallah sai anjima za’ayi ta, nan mace zata jibge kamar asara ayita kiraye kirayen “ya “yan dan ubanki baza ki kawomin kaza ba,

     Saida kowa ya tashi sannan nima na d’auki kujerata nayi d’akina, buta na d’auko nazo nayi alwallah magrib na shige tare da rufe k’ofata ba kuma zan sake fita ba sai Allah ya kaimu gobe lafiya…..

       Dan babu abinda banda shi a cikin d’akina na masarufi, ina da indomie ina da kayan tea kuma ko wane lokaci flarks ina cike yake da ruwan zafi, saida nayi sallah isha’i tare da addu’o’in samun d’aukaka kamar yanda na saba a duk lokacin da nayi sallah.

    Bana buk’atar komai domin banajin yunwa, a inda na gama sallata a wurin nayi kwanciyata, ban dad’e da kwanciya ba bacci yayi gaba dani…..

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());        Can cikin bacci naji hayani wanda tak’i k’arewa muryar Nana sama sai zabgaga ashariya takeyi tare da cewa auren ka ko auren wahala, auren cida kai niba ga gidan gayu ba na bige ga zaman haya, har kunya nakeji k’awayena su san inda nake dan darajata da nasabata ta wuce in aureka haka nan Allah ya had’ani da wannan auren k’addarar da k’aranci shekaruna duk kabi ka bigar dani na koma wata abun tausayi, tou wallahi idan kaga yau na kwana dakai saika biyani duk bashin daka san inabinka….

       Ajiyar zuciya na sauke tare da kallon “yar agogon dana mak’ala a jikin bangon d’akina 11:45pm, maida kallona nayi wurin da Nana da mijinta dake rik’e da wandonshi yana mata magana amma bana iya jiyosu….

         Zazzaga Nana tayi tare da cewa wallahi ka mutun ba abinda ya dameni idan ma ka mutu ko ka sakeni ai dubunka suna can suna jirana, magana ya sakeyi still banji abinda yace ba, Nana kuwa ta sake d’aga murya cewa bazan koma d’akin ba, kamata yayi da kokowa yana k’ok’arin turata cikin d’aki, d’an gajeran tsoki nayi tare da tirr da Allah wadai da wannan hali….

     Bansan yanda suka k’are ba na koma nayi kwanciyata naci gaba da bacci na. Tunda na kwanta ban sake farkawa ba saida aka fara kiraye kirayen sallah asuba……

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button