NOVELSUncategorized

KWARATA 14

???? —— 14


            Saida ma na fita daga gidan nakejin wani irin bak’in ciki ya tokaremin zuciyata, wallahi dana iya mota saina taho da motar Bello, zanje gida na jira zuwan shi domin dai nasan nabar baya da k’ura babu yanda za’ayi ya barni na ci kud’in nan , murmushi nayi sannan nayi magana a bayyane cewa Allah ya kawo ka lafiya Baban kwali Baban tusa…..


       Ban tsaya wasa ba haka kuma banyi gigin biyawa gidan kowa ba na yanki santa na fara neman gidan da nake kwana….

      Tafiya mai zurfi nayi kafin na fito bakin titi, Allah kuma ya taimakeni ina fitowa na samu abin hawa ban wani b’ata lokaci ba, ko ciniki ban tsaya yi ba na afka nace muje.

      Inda zamuje ya tambayeni, ni kuma na fad’a masa yaja muka tafi, raina fes zuciyata dunk’ule da farin ciki na isa gida, ko mai napep 1k na bashi yayi ta zabgaga min godiya tare da jawo addu’o’in samun nasara a rayuwata…

     Godiya nayi masa sannan na shiga gida da sallama kamar yanda na saba bawai dan zasu amsa min ba, a , a, inayi ne dan fita hak’k’in musulinci, kai tsaye k’ofar d’akina na tsaya na ciro mukulli na bud’e na shige abuna….

      Saida na fara adana kud’ina a ma’adana mai sirri sannan na fara neman abinda zanba baba uban ba’u, { ciki } saida na d’ora girkin abinda zanci sannan na fita nayo alwallah dan ganawa da mahalicci na…

       Bayan na fito daga bayi ne naji su Saude suna fira kuma ga dukkan alamu zance Dikko ne sukeyi, da wutsiyar ido na kalli wurin, wata bak’ar cikakkiyar buduwarce na gani tsaye, amma ban tab’a ganinta ba sai yau, kallo d’aya zakayi mata ka tabbatar tanaji da hutu domin ta huta d’in, duk inda ta fito yarinyar can d’iyar wani attajiri ne…

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());      Fasa alwallar nayi na tashi na koma d’aki na kashe d’an gass d’ina na d’auko asawaki dan inaso inji inda labarin nasu zai tsaya, dawowa nayi na zauna ban kalli inda kowa yake ba kuma banyi ma kowa magana ba na tusa buta a gaba naci gaba da gogo asuwaki a bakina….

         A ` i ce ke cewa kai amma gaskiya Hafsat baki da hankali ai da ki nemi d’an mai kud’i da asiri gara ki tafi tsirara kawai ki huta, kina ganin ubanshi banza ne ? Wannan Dikkon da kike gani tun yana ciki an gama dafashi da asiri yanda Babanshi yasha wahala kafin ya samu namiji kina ganin daya sameshi da wahala zai barshi ne yai ta yawo figifigi a duniya ba tare da an bashi dafa’i ba ? Kai wallahi kimayi hak’uri ,

      Cikin muryar sakataccin “ya “ya tace no ai da ina kiranshi wani lokaci yana d’aukar wayata amma yanzu ya daina d’auka kwata kwata, da sauri na d’aga kaina na kallesu sai kuma na basar kamar ina kallon wani wuri, wato ita tana ma da number Dikko, tunani na farayi yanda wayarta zata zo hannuna na, ba ansar wayarta zaimin wahala ba yanda zan gano sunan Dikko shine wahala a wurina….

        Kawai gaba d’aya tunanina ma har ya tashi daga d’aukar number, kawai harma na hango gani nan na d’auko tsiraicin Dikko na balbad’a a social media, tabbas Dikko saina had’a shagalin partyn wulak’anta mishi rayuwa…. Tunani na ya dawo ne a lokacin da naji Saudatu na cewa aiko ki dage yarinya dan nan da shekara d’aya Dikko baya rik’uwa, tunda shi dama bai dogara da kud’in gidansu ba gaskiya Dikko yana da sa’ar rayuwa idan kika auri shi kin more rayuwa domin dai cikakken namiji ne…

        Banyi musu magana ba dai naci gaba da goge hak’ora na, wayau sukayi ma Hafsat suka amshi kud’i masu yawa a hannunta da sunan za’ayiwa Dikko asiri, ci gaba da tattaunawa sukayi amma hankalina baya wurin firarsu ya tafi wurin karatun halayyar Hafsat, tab’e bakina nayi a bayyane nace itama dai “yar mad’igon ce { Lesbian } 

      Kallona tayi nima na watsa mata mayatattun idanuwana masu sa mutum ya rikice na k’ura mata su sosai domin ina so ta yabani idan har ta shigo hannu na nice zan koya mata barikin da zata kawo min Dikko k’asan k’afaafuwana nima in rama wulak’anci da yayi min dan nayi alk’awari nima sai Dikko ya lashi k’afata kamar yanda yasa na lashi tashi…

        Shegiya ta kuwa daskare ta kasa barin kallona, kyakkyawan murmushi nayi mata tare da cewa sannu ko ? Na k’arasa maganar tare da d’an wasa da idanuwana… Murmushi tamin tare da cewa ya kike ? Ban bata amsa ba naci gaba da alwallata…

      Ina gamawa ban sake bi ta kansu ba nayi d’aki inajin tana ta magana amma na basar da ita, nadai juya ta ganni maza ma sun gani sun rikice ina ga mata mayun mata kuma ?

    Ina shiga na kunna gas ina na kabbara sallah. Bansan yanda suka k’are ba, amma nasan tabbas saita dawo saboda taga ina da irin k’addarar da suke nema…

      Bayan na gama sallah na zuba abinda zan dafa a tukunya sannan na zuba ruwa na tafi wanka, lokacin da nayi wanka na dawo har ya dahu, dan haka kashe gas ina nayi sannan na shafa mai da powder, d’aurin gaba nayi sannan na zuba abinci na naci gaba daci….

        Bayan na gama duk abinda nake na kunna kallo, sannan na saka kayan bacci na koma saman katifa na kame kamar d’iyar wani shege… Kai gaskiya inajin dad’in wannan rayuwa tawa, saida na kwanta sannan na bud’e data ta, lamba d’aya na gano bayan na ganoshi na tura mishi vidion dana d’auko , tare dayin voice note na tura mishi. Ina turawa na sauka online na kashe wayata gaba d’aya, na kashe kallo na rufe d’akina nayi kwanciyata…….

      Tashin hankali shine kalmar da Alhaji ya fad’a a lokacin da yaga vidion dana tura mishi, wata irin gagarumar zufa ta yayyafo mishi a lokacin da ya saurari voice note ina, tashi yayi tsaye cikin tsananin tashin hankali ya rasa gane a wace rayuwar yake rayuwar mutuwa ce ko ta duniya ?

      A gefe kuma wayarshi ce take ta kwarara ihu, lambar mai gida Dikko ce keta tsalle babu k’ak’k’autawa amma Alhaji yau kam bata Dikko yake ba, saida kiran ya tsinke sannan Alhaji ya sake kunna maganar Sultana yana sauraro, ga abinda take cewa….

     Ina mai farin cikin sanar dakai wannan mummunan labari, d’abi’a na ne yin albishir da farin ciki yayin fad’ar abu mai munin gaske, kuma nakanyi farin ciki yayin fad’ar abun farin ciki, wannan vidion dai dani dakai ne a ciki kuma kaga irin bad’alancin da muke aikatawa a ciki, nidai banajin komai idan wani ya gani domin ni iyayena tuni sun sallama ma duniya ni, saboda haka ni duniya itace uwata kuma itace ubana, idan na yad’a wannan vidio banajin komai tunda biye nake da mutanen cikinta ina basu, nayi tunanin maidashi faifayin filet na sidi dan in siyar na samu kud’i , sannan kuma in watsashi a yanar giza gizo dan inyi suna, kai kuma kana da dama d’aya tak data rage maka, idan har ka bani naira miliyan d’aya nayi maka alk’awari zan goge shi sai in hak’ura basai nayi suna a duniya ba…… Idan kuma baka dasu in turawa “ya “yanka ko suna da kud’in fansar ka !  Sultana, Sultana ce yarinyar mai dogon zamani, idan kuma kace zakayi gigin sako hukuma a ciki na riga dana turama k’awata nace da taji an kamani firr zakaji su sun watsu a duniya kamar saukar tsuntsaye. Ka huta lafiya habibinah muah ????

       Goge zufa Alhaji yayi tare da cewa Allah ka tsinewa yarinyar nan albarka, shegiya tsinanniya ubanta da uwarta basuyi addu’ar kwanciyar aure ba yayin da zasu kwanta Allah ya basu cikin d’ebabbar albarkar yarinyar nan, a daidai wannan lokacin kiran Dikko ya sake shigowa.

       Jiki a sanyaye Alhaji ya kalli wayar tare da cewa mai gida kayi hak’uri wannan abun kunya ina za’a dashi na watsu cikin duniya ina zina, abun bak’in ciki da d’iyar da nayi d’iya da ita, garin ciye ciye na har naje na ciwo ma kaina bala’e, kila sai ta k’arar da arzik’ina, kuma tace idan na fad’awa hukuma taba k’awarta vidion zata yad’ashi wannan shine ciwo ya riga ajali zuwa…

    Kuka Alhaji yayi tayi tare mitar ya shiga 3 ya bani ya lalace, wannan labarin abun kunyar waye ma zai fad’a mawa bare kuma yasa ran zai samu wata sahihiyar shawara, kai ya bani ya bani ya bani……..????????????‍♂????, a daren nan Alhaji baiyi bacci ba kuma baibi kiran Dikko ba, wayar Sultana kuma ya kirata yafi so adadin yawan dutsinan da ake jifar shedan dasu amma maganar dai d’aya ce cewa a kashe…….

     Da safe , tunda nayi sallar asuba na koma bacci, can cikin bacci naji ana dukan k’ofar d’akina, addu’ar tashi daga bacci d’auke a bakina bayan na gama nace waye ? Na tambaya cikin muryar bacci tare dakai idona saman agogon dake lik’e a saman bangon d’akina k’arfe 10:36am, cikin muryar murna Nana tace “yan sanda aka d’auko miki Sultana….

       Murmushi nayi tare da jawo wayata na kunna sannan nace ma Nana da Allah kije kice waye ya d’aukomin “yan sanda ? Cikin farin ciki ta koma zaure sannan ta tambayi d’an sanda waye yake k’arata ?

       Fad’a mata yayi tayo cikin gida da har yanzu tanajin dad’in k’arata da akayi, a bakin k’ofar d’aki ta tsaya sannan tace wai abokin Babanki Bello, jinjina kaina nayi tare da cewa tou ina fitowa….

      Data na bud’e na nemo lamba 2, hotunan dana d’auke shi jiya na tura mishi tare da yin voice note na antaya ma banza, ina gamawa na kashe wayata, saida nayi wanka naci gayuna na watsa turare na d’auku iyakar yanda hankali baya tunani duk wanda ya ganni saina burgeshi, fitowa nayi banma kowa magana ba na tunkari zaure, dan zuwa wurin hukuma a yanayin talauci yana jawo ma mutum raini….

        A k’ofar gida na samu d’an sandan nan ya gama shak’e b’acin rai daga gani yana jira muje can yaci uwata, a yangance na fito cikin aji na kalleshi tare da cewa “yar labai barka da aiki……

     ‘Dan sakin fuska yayi tare da cewa yawwa, gaishe shi nayi tare da ce masa nice Sultana, kallona yayi sama da k’asa sannan yace tou hajiya muna gayyatarki zuwa ofishinmu ai anyi miki bayanin mai k’ararki ko ?  murmushi nayi tare da cewa babu damuwa muje amma Allah yasa ba’a cikin motar “yan sanda zaka d’aukeni ba, murmushi yayi tare da cewa ai hajiya napep zamu shiga, ajiyar zuciya nayi cikin sigar jan hankali sannan nace tou ai har naji natsuwa.

Napep muka hau muka nufi c p s , kuma nice na biya kud’in 1k ne na bayar kuma daya anso canji nace ya rik’e yasha ruwa, tunda muka fita a napep gaba d’aya wurin saida hankalin kowa ya dawo kaina, na farko dai ga wanka ga gayu ga k’amshi uwa uba kyau Allah yayi min kyawun da mutum baya gajiya da kallona, ga gashina na tik’ashi nayi mishi wani irin parking irin na wayayyin mata, baka isa ka rainani ba ko waye kai domin sitirar dana saka ita kad’ai ta isa ka gane ni ba sa’ar wasan yaro bace ba…..

    Ofishin d c o muka nufa, a ciki na samu Bello zaune tare dashi da wasu abokan Babana, sallama nayi sannan na gaishesu dukansu cikin kyakkyawan yanayi, bayan mun gaisa nima na samu wuri na kame kamar yanda naga kowa yayi…..

       Kallona d c o yayi bayan ya gama karanta wata takarda dake gabanshi sannan yace Maryam miya had’aki da Bello ne ? Murmushi nayi tare da gyara zamana nace ranka ya dad’e ai Baba Bello abokin kasuwanci ne, halak’a ta mutunci ne a tsakani na dashi bayan wannan babu komai….

          D C O yace tou jiya ina kika had’u da Bello ne ? Ranka ya dad’e majalissar su naje gaishe su, bayan mun gaisa kuma ya tambayeni nayi aure nace masa A , a, yace yanzu ina nake zama ? Nace masa ina zama a tsohuwar anguwarmu daya sani, ya tambayeni ko ina kasuwanci ne ? Nace masa Eh yace me nake siyarwa ranka ya dade nace masa karuwanci nakeyi, tsakanin mai saye da mai siyarwa ai babu fushi anan muka daidai suka d’aukeni muka tafi wani gida, nuna yawan duka abokan Babana nayi sannan naci gaba da cewa ranka ya dad’e dukansu nan babu wanda baiyi ba kuma duk saida suka k’ara zagayawa “yar labai, kuma gasu nan ka tambayesu idan nayi musu k’arya. Kuma cikon kud’in ma har yanzu basu bani ba..

        Kowansu zaro ido yayi tare da dafa k’irji cikin yanayin mamaki yace ke mune mukayi iskanci dake ? ‘Daure fuskata nayi kamar gaske nace aini banajin kunya tunda dai banji tsoron Allah ba nayi zina wallahi banajin kunya gaban kowa in fad’a nayi, kunyi mana ko k’arya zan muku ne ? Lokacin da bakuyi ba nace kunyi ?

       Gaba d’aya wurin hayaniya ta tashi har bakajin bakin wani, d c o ya dakatar dasu tare da cewa suyi mishi shiru, bayan kowa yayi shiru ya kalleni sannan yace ke Sultana Bello yana tuhumarki kud’in shi da kika d’auka. Cikin natsuwa nace wasu iri kud’i kuma ranka ya dad’e ?

        Bayani d c o yaimin kamar yanda na sani, jinjina kai nayi tare da cewa idan sun gama k’arata nima zanyi k’ararsu saboda b’atamin suna da sukayi, ranka ya dad’e a gaban idon waye na d’auka kud’in ne ? Nifa bana sata amma ina neman maza gaskiya, duk abinda nakeyi bana jin kunyar asan inayi domin dai duk sana’a sunanta sana’a, idan ma na d’auka aka tambayeni idan nasan na sata kawai zan dawo musu da kayansu in basu hak’uri tunda karuwanci da nakeyi ai ban b’oye ba na fad’a tunda ba abun kunya bane….

      Tambayar Bello D C O yayi ko yana da wata sheda ne ? Baida ita tunda an tambayi mai gadi yace shidai bai ganni cikin mota ba, duk iyakar binciken da akayi dan asamu wata sheda babu ita, dan haka aka rubuta takarda cewa an janye k’ara, bayan an gama rubutu aka bani na saka hannu da larabci nayi sigining ina, an mik’e za’a tafi nace ma d c o naga fa sunamin wani kallon hadarin kaji sufa fita ido na, d c o yace ai duk an rubuta, nace to ranka ya dad’e cikon kud’ina kuma sai yaushe zasu bani ?

    Hak’uri  d c o ya bani tare da nunamin tunda anyi masa sata inyi hak’uri inma barshi da ramuwar biyan kud’in mutane, babu kunya ba komai nace kenan ni yanzu ranka ya dad’e sunci banza ? Duk wanda ke cikin office in saida ya kalloni, nace ranka ya dad’e kafa duba lamarin nan gaskiya ni ba’amin adalci ba, shiru wurin yayi wutar kowa ta d’auke, murmushi nayi tunda basu da amsa nace nawa ake yankar sammaci ? Sammaci ma ake cewa abin ko miye ?

      A kotu ake yankar sammaci d c o ya bani amsa tare da fad’amin abinda ake kiran nasu da turanci, oho dai da yake kan baya ganewa kasa maimaitawa nayi saidai kawai nace nawa ne ? Kud’in aka fad’amin na bud’e jakata na bada sannan nacewa d c o ga wanda nake k’ara nan Bello ina tuhumarshi akan b’atar mahaifina daya tafi babu wanda yasan ina yaje……….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button