Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar dakataccen shugaban hukumar amsa korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Rimin-Gado, ranar Laraba ya shigar da Ganduje kotun ma’aikata kan korarsa da akayi daga bakin aiki.
Daga cikin wadanda ya shigar karar akwai Antoni Janar na jihar Kano, majalisar dokokin jihar Kano, Akawunta janar na jihar Kano, shugaban hukumar, Mahmud Balarabe, da kwamishanan yan sandan jihar.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa Alkali mai shari’a Oyejoju Oyewumi ya saurari karar da tsohon shugaban hukumar ya shigar.
Lauyan Rimin-Gado, Muhammad Tola, ya bayyanawa kotu cewa an sanar da dukkan wadanda aka shigar kotu amma basu amsa ba. Amma lauyan Gwamna Ganduje, Abdulsalam Saleh, ya sanarwa kotu cewa tuni sun nemi uzuri kan hakan.
Ya kara da cewa sun nemi izinin a dawo da zaman jihar Kano tunda duka wadanda aka shigar kara na Kano.
Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 7 ga Maris don tabbatar da an sanar da kowa.
[ad_2]