Labarai

Gudaji Kazaure ya taro babban yaki da Masu Yiwa arzikin Nigeria ta’addanci – Datti Assalafy

Gudaji Kazaure ya taro babban yaki da Masu Yiwa arzikin Nigeria ta’addanci – Datti Assalafy

Tun bayan da Hon Gudaje Kazaure ya sanar da bayanin mummunan cin amanar kasa da aka tafka a babban Bankin Nigeria hankalin azzalumai barayi ya tashi

A halin yanzu, barayin da suke da hannu a cikin lamarin, sun hana Gudaji Kazaure ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari sun fitar da makudan kudade, sun sayi jaridu da kudi mai tsada domin a lalata tasirin rahoton Hon Gudaje Kazaure

Ba sabon al’amari bane a Nigeria, tsinannu azzalumai maciya amana suna saye jaridu domin su yi musu aiki irin wannan da ake yiwa Hon. Gudaje Kazaure

Shugaba Buhari ne ya shinshino an yi cin amana a babban Bankin Nigeria, kuma shi da kansa ya nada Hon. Gudaji Kazaure domin ya jagoranci bincike ya kawo masa rahoto kai tsaye ba tare da shamaki ba

Hon. Gudaji Kazaure da kwamitin bincikensa sun gano an saci kudi kimanin Naira Tiriliyon tamanin da tara (N89,100,000,000,000) a babban Bankin Nigeria, ya dauko rahoto zai kawo wa Shugaba Buhari an hanashi ganin Buharin, wannan ne dalilin da yasa ya fito ya shaida wa duniya

A maganganun da Gudaje Kazaure yayi, yace binciken da suka gudanar akan wannan kudi yana daya daga cikin dalilan da yasa Babban Bankin Nigeria ya yanke shawaran sauya fasalin kudin Nigeria domin su samu damar cinye kudin cikin ruwan sanyi

CBN Governor shi kadai ba zai yi wannan satar ba sai da hadin bakin wasu manyan mukarraban Gwamnatin Buhari, yanzu da Hon. Gudaje Kazaure yake son ya tona musu asiri zasu yakeshi, sun fara yakarsa ta hanyar saye jaridu domin su karyata rahoton Gudaje Kazaure

Mu sani cewa Hon Kazaure ya taro babban yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nigeria ta’addanci, yana bukatar agajin addu’ah daga garemu sosai

Muna rokon Allah Ya kareshi, Ya bashi nasara akansu

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button