AsuuBuhariLabarai

Ba Za Mu Iya Biyan Buƙatun ASUU Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan alƙawurran da Gwamnatin Tarayya ta sha yi wa Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta biya buƙatun su domin su daina yajin aiki, a yau kuma gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biya wa malaman jami’o’i buƙatun da suke nema ɗin.

Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da Gidan Talabijin na Channels ke hira da shi a ranar Alhamis.

Kafin tafiyar ASUU yajin aiki makonni biyu da suka gabata, ƙungiyar ta ce duk da alwashi da alƙawarin da gwamnatin tarayya ta ɗauka bayan masu shiga tsakani, har da shugabannin ɓangarorin addinai sun sa baki, har yau gwamnatin ba ta cika alkawari ko ɗaya ba.

Idan ba a manta ba kuma, bayan an shiga tsakani a cikin watan Janairu, ASUU ta ce “idan malaman jami’o’i su ka sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, shi ne bai cika alƙawari ba.

Babba daga cikin alƙawarin da har yau aka kasa cika wa ASUU shi ne wanda Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a rubuce (MOU) cewa za ta aiwatar (MOA), kuma ta sa hannu tun a cikin 2009.

Daga Muryaryanci

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button