Labarai

Bada Izinina Aka Wallafa Allah Wadai Ga Masu Kisan Deborah Ba – Atiku

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku, ya ce dole ne duk wani sakon Twitter da ke shafinsa ya samu amincewarsa kafin a yada shi a duniya.

A baya an wallafa Atiku Abubakar ya mayar da martani game da kisan Deborah Samuel da aka zarga da aikata mummunar dabi’ar batanci ga Annabi SAW a Jihar Sokoto.

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin goge sakon ne a lokacin da ya kai ziyarar neman goyon baya ga Gwamna Godwin Obaseki na Edo a gidan gwamnati da ke Benin.

“Kowane rubutun Twitter ko facebook da sauran kafafen sadarwa na zamani dole ne sa samu amincewa ta amma wannan bai samu ba don haka na nemi su sauke shi.

“Na tsaya tsayin daka game da shari’ar Musulunci, aka zage ni, aka jefe ni da duwatsu, amma har yaushe hakan ya kare? Duk da haka, ban canza matsayina a kan hakan ba. Ba na jin tsoron tsayawa kan batutuwa masu mahimmanci.”

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button