DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

Episode 23

Wannan kalma ta matsiyaciya tanayimin ciwo musamman idan Pappa ya dangantata da Addana, wannan rana ban iya hassala komai ba saboda damuwa da tashin hankalin da nake ciki.
Idan na tuna Addana tanacan babu lfy Kuma babu kudin da zaa siya Mata magani sai naji hawaye yana shararomin qannena da ya kasance Addah ce kawai gatansu suna fadomin kukana yana qara tsananta.
Qarfin hali nayi na tashi naje gurin madam dita na tsugunna Ina kuka ta kalleni tare da tambayata matsalata, yanda tayimin mgnr ya sanyaya zuciyata na karkace na zayyane Mata damuwata ta nuna alhininta sosai.

Nan na dada Mata alfarmar da nake nema ta albashina na wata uku zan tura a nemawa mahaifiyar tawa magani, jummm tayi na dan lkc sannan ta dago ta fara yimin dogon larabci wanda bashi nake buqata ba sannan tacemin ita yanzu bazata iya bani kudi ba saboda Nigery sun damfareta da yawa.
Haka na miqe jikina babu qwari na koma daki na dasa sabon kuka ganin kukan bazaikai min ba na tuna shawarar da Addah take bani kullum idan na fada Mata cewa banason zaman qasashen nan matsayin bauta.
Miqewa nayi nayi alwala nayi sallah raka’a biyu na dauki qur’ani Ina karantawa inajin wani sanyi yana zagaya zuciyata a hankali na miqe na dauko wayata da taketa ring.

Nandanan annurin fuskata na halitta ya dauke na danna wayar na kara a kunne na baiko amsa sallamata ba yace “sunce nanda awa goma sha shida zata iya mutuwa kudin ma ya qaru daga dari biyu da ashirin ya koma dari uku da hamsin saboda harda aikin tsiron mahaifa zaayi Mata”
Qitt ya yanke wayarsa na zubd saman carpet din Ina furta innanillahi wa Innah ilaihirraji’un hawayen ma ya tsaya ya daina zuba a idanuna sai tafasar zuci kawai wani tuquqi yana tasomin daga qasan maqoshina wanda nakejin kamar zai fito da raina.
Inanan zaune cikin tunanin rashin makoma wayata ta soma Ring kamar bazan dagaba nadaiyi qarfin halin tashi zaune na dauko wayar number Aysher ce na sauke ajiyar zuciya tare da karawa nace “Aysher Ina cikin matsala”

Salati tayi tace “badai fyade Nazan yayi miki ba ko?” Numfashi na sauke nace “wlh da zaiyimin ya bani abinda nake buqata yanzu da zan bashi Aysher Addana zata mutu saboda rashin kulawar Pappa duk kudin da nake turawa ya cinye yanzu kudin magani ya gagaremu”
Ajiyar zuciya Aysher tayi tace “kema kinada matsala Habeey kinada hanyar da zaki samu duk abinda kike buqata amma kin matse abu a cikin cinya yanzu dai ba wannan ba kizo muje Beachwood Jabir ne yayi baqo dan governor Usman Waziri ne na Bauchi Amininsa yazo shine zamuje taronsa”

Numfashi na sauke nace “nidai inajin tsoro Aysher….” Katseni tayi da cewa wannan itace kawai mafitarki kiyi ki shirya ki fito yanzun zamuzo”
Kashe wayar mukayi a tare na sake zaman dirshan har zuwa wani dogon lkc wayata ta qara dokawa na daga tace “na dauka zamu tarar dake a waje” miqewa nayi na dauki doguwar rigata na saka na fito a salube na dauki wayata da jakata da wasu cikin kayana.
Da nasan inaso saboda na riga na zabi duk abinda qaddara tazomin dashi yau duk abinda zai faru saidai ya faru amma nima na gama zaman gdan aiki zaman hantara da gyara da wulaqanci, a wannan rana na haqiqancewa kaina cewa a yau duk wanda ya nemi wani abu a gurina saina bashi indai Addata zata tashi taci gaba da rayuwa a doron duniya.

Madam dita tana sama na fito naci karo da Nazan yana saukowa yana ganina ya nufoni da sauri yana fadin “Habeebaty Ina zaki?” Bai samu ko kallon tsiya a gurina ba balle na arziqi na qetareshi na wucce na fito harabar gidan Ina fitowa na hango wata zundumemiyar mota me numfashi a gabana na.
Isa nayi gaban motar Aysher ta budemin na kalleta tayimin murmushi tare da rungumeni tace “wow! Habeey ke kadara ce me tsada” yaqe nayi na shiga bayan motar saurayin Aysher Jabir sai kallona yakeyi nace masa “sannu” daqyar ya iya amsawa idonsa na kaina Aysher tace “ya kaga babyn na fada maka babban kayane ba matar talaka bace”

Ajiyar numfashi yayi yace “muje dai tukunna inajin tsoron jizgin Taheer duk yanda kike tunanin mutum me izza Taheer ya wucce nan sannan shi a tsarinsa baya bare budurwa fah.
Gabana dokawa yakeyi saboda jin hirar tasu da nakeyi duk akaina ne, haka har muka isa airport sunata hirarsu duk akan abokin nasa nidai bana sanya musu baki saboda ni ba ma’abociyar shiga abinda babu ruwana bace.
Mun dan jima a airport din kafin fasinjan su fara fitowa na zuba musu ido Ina kallonsu har suka kusa qarewa sannan naga wani matashin Saurayi me cikar zatin halitta Gant kyakkyawa wankan tarwada ya fara saukowa riqe da yar qaramar akwatu a hannunsa, zuba masa ido nayi Ina kallonsa shima idonsa akaina yake duk da bana fahimtar hakan saboda baqin glass din idanunsa.

Jabir naga ya nufeshi da sauri sun rungume juna tare dayin kissing kuncin junansu sukayiwa juna murmushi Aysher ta miqa hannu domin karbar jakar hannunsa amma saiya janye tare da daga mata hannu alamar jinjina ya miqawa Jabir ya karba sannan suka iso gurin motar nidai inata kallonsu cike da sha’awa da Kuma faduwar gaban dana rasa dalilinta.
Bude masa gaban motar Jabir yayi ya shiga sannan shima ya shiga Aysher ta tabani nayi firgigit daga duniyar tunanin dana lula daidai lkcn da wayata ta dauki ruri muka shiga motar lkc daya da Aysher sannan na dannan pick na fara mgn da cewa “Pappa meye kuma ya faru?” Katseni yayi da cewa “saura awa shidda uwarki ta karci qasa bisa sakacinki idan ta mutu kece da asara sannan tace na sanar dake indai baki samo kudin da kika ceto rayuwarta ba cikin sa’o’innan da suka rage nononta da kikasha bata yafe miki ba………..

UMMUH HAIRAN CE…✍️
[7/26, 10:47 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️

PAID BOOK

HAƘƘIN MALLAKAR
              ????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
(UMMUH HAIRAN)

Don Allah idan kinsan baki biya ba kada ki karanta VIP 600 single 300

Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin

Account number
             ????????
     0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar

GTB

Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp
          ????????
09013718241

Saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number
           ????????
09013718241

Episode 24

Wani mugun shock naji tare da zuba sun fara ketomin a hankali nake furta Allahummah la sahla….” Har zuwa qarshenta ni kadai nasan irin zugin zucin da nake fuskanta a daidai wannan lkcn.
Rintse idona nayi na dora kaina saman bayan kujerar inajin wani zazzabi me dafa qashi yana saukomin bansan ina muka nufaba Saida aka tsaya suka fita gabadayansu wannan baqon ya cire glass din idonsa ya sauke qananun lumsassun idanunsa akaina kamar me nazarin wani abu game dani.
Aysher ce ta janyoni tace “tashi muje muci abinci mu wucce gda naga kamar na takura miki ko?” Hadiye wani Abu nayi me nauyi sannan na zuro kyakkyawar qafata qasa na sauketa na miqe baqon ya bini da kallo tun daga sama har qasa.

Ya girgiza kai kawai yayi gaba Jabir yabi bayansa muma muka rufa musu baya sun danyi gaishe gaishensu nidai ko kalma daya bata shiga tsakaninmu dashi ba har muka isa gurin cin abincin.
Sukayo order kowa ya zabi abinda yakeso ni kuwa lkcn da aka miqomin menu din girgiza kai nayi kawai na kalli Aysher hawayen da naketa qoqarin shanyewa suka zubomin karaf idanuna ya fada cikin na baqon ya lumshe idonsa tare da sake budewa a kaina muka sake hada ido.
Qasa nayi da kaina saboda wani yanayi da nakeji game da baqon, Aysher ce tayimin teak na abincin da zanci aka kawomin kowa yanacin abincinsa nikam juya cokali kawai nakeyi lkc zuwa lkc ina share hawayen idona da banason a fahimta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button