DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

Rufe mata baki Bushirah tayi tace “don Allah kada ki rantse Mom matar mutum kabarinsa bakisan abinda Allah yake nufi da hakan ba idan kika cika matsawa komai zai iya faruwa haba Mom kifa tsaya ki duba na tsanaki cikin lamarin nan tunda kike da Ya Taheer banajin ya taba cemiki yanason wata mace sai akan Habibatullah…”
Angajeta tayi ta fada jikin Taheer daya dafe kansa ysnajin kamar zai tarwatse tace “kajini da yan iskan yara to kuyimin nasiha tunda kunfini sanin abinda ya dace” fuuuuuu ta shige daki ta dauko mayafinta da Jakarta tace “kayi sauri yau qafata qafarka kaida Dubai kuwa zaka dade dan ubanka shashasha shi ko tsoron ciwukan zamanin nan bayayi”

Saida taje bakin qofar ta juyo tagsnshi a zaune inda tabarshi ta juyo a fusace ta daukeshi da mari sannan ya dawo hayyacinsa ya miqe ya shiga dakinsa ya hado kayansa har ya juya zai fita ya koma ya bude inda kayanta suke ya zauki rigar baccin data kwana da ita kwananta na qarshe a gidan ya rungume a jikinsa yana shinshinawa.
Saida yaji Mom na qwala masa Kira sannan ya fito a gajiye rungume da rigar a jikinsa ya shiga motar driven yaja suka nausa airport, da sukazo hanyar unguwar su Habeey har leqowa yakeyi wai ko zaiganta amma Bai ganta ba, ya furzar da iska tare da gyara zamansa ya dora rigar a qirjinsa yanajin kamar Habeey ya rungume.

___________Biyar jirginsu ya sauka kasancewar lahadi ce governor waziri dakansa yaje dauko iyalansa tun daga fitowar Taheer a jirgi yaga yanda yake layi yasan ba qalau ba har ya iso gareshi ya fada jikinsa ya rungumeshi yace “Dad don Allah kada ka bari Mom ta rabani da Habibatullah itace rayuwata Dad bantaba son wata ya mace ba sai akanta, kaji Dad don Allah wlh Itama bason wannan qazamar rayuwar takeyi ba kawai dan babu yanda zatayi ne Dad har yanzu Habeey tsoron maza takeyi saboda bata sababa…”
Rufe masa baki yayi yace “could down My Son kayi addu’a kawai ita mace allurar ruwa ce me rabo ke dauka balle irin wadannan matan, Son banayi maka sha’awar auren karuwa nafison ka auri kamilar mace  manzon Allah yace mu zabawa yayayenmu uwa ta gari wacce zasuyi alfahari da ita”

Share qwallarsa yayi yace “itama ta garice nine na fara batata nine ma bana gari ba saboda son zuciya da kwadayi yasa na wulaqanta mata rayuwa Dad nifa koma ya take inasonta kawai ka nemamin aurenta”
Jikin Dad yayi sanyi sosai amma zuciyarsa bata amince da ya nemawa Dan nasa auren Habeey ba musamman da suka shiga mota Mom tarinqa famfashi tana fada masa qarya da gaskiya, shima ya hau ya zauna tare da cigaba da lalllashin dannasa.
Ganin bashida alamun cinmma nasara yasashi sharesu yaci gaba ta qulla me yuwuwa a zuciyarsa, Abu na farko dole ne duk yanda zaiyi yayi ya kasance tare da Habeey Koda aure ko babu aure saboda barinta gidan magajiya Adama matsalace babba itadin ster of women’s ce duk namijin da ya kalleta sai yaso dandana daga gareta shikuma abinda baya fata kenan yafiso ya kasance shi kadai ne yake mu’amala da ita.

Da wannan tunanin suka shiga government house din motar tayi parking a wata qatuwar rumfar aje motoci Taheer ya riga kowa bude motar ya fice a fusace yanaji Dad na kiransa ya daga masa hannu batare daya juya ba yace “me zakacemin Dad bayan wannan matar” ya nuna Mom yace “ta zigeka har sharri ma tayiwa Babena saboda kawai batasonta to nidai babu ruwana ko ku auramin ita ta zama matata ko kada ku auramin ita bazan fasa hutawa da ita ba saboda babu macen da take certified dina kamarta kunga kenan sai ku shirya daukar jikoki course bazan qara yi Mata amfani da maganin hana daukar ciki ba gara mu samu zuri’a mum….”

Wani mugun mari Alh Wazir ya dauke dannasa mafi soyuwa a ransa dashi yace “ashe bakada hankali dan ubanka Taheer, ni zaka kunyata ka tozarta a idon duniya? Ok na gane inda ka dosa kaje Taheer kaje kayi abinda kaga dama aurene kaida yarinyar nan har abada dan ubanka idan mune muka haifeka zamu gani idan kuma Kaine ka haifemu nan ma zamu gani sakarai kawai da baisan ciwon kansa ba”
Marin ya bashi mamaki kuma ya shigeshi tunda yake da iyayensa musamman Dad baitaba daga hannu ya dakeshi ba sai akan Habeey hakama Mom, “Habeey! Habeey!! Habeey!!!” Baisan sanda bakinsa ke furta wannan kalmar ba sai jiyayi Mom tace “ba Habeey ba inma habibu ne saidai zuciyarka ta tarwatse amma bazaka kawo mana baragurbi cikin ahlinmu ba”

Dagowa yayi ya kallesu kawai yayi wani murmushi dashi kadai yasan me yake nufi ya juya da sauri ya shige part dinsa ya datso qofar da qarfi Mom da Dad suka kalli juna cikin dan firgici Kubrah ta tabe baki tare da nufar nasu bangaren ita kuwa Bushirah kawai hawaye take zubarwa as Imaging tana jin da ace itace a halin da Habeey take ciki haka itama iyayenta zasuyi mata kenan?”
Saurin kada kai tayi tare da nufar bangaren nasu da sauri tana kuka, nan fah Dad yabita da kallo yace “au ita kuma wannan fah?”
Tabe baki Mom tayi tace “yar abi yarima asha kida ce ita kasan duk abinda wancan shashashan yakeso itama shi takeso dazu har wani wa’azi takeyimin fa” shidai Dad baice komai ba ya nufi part dinsa Mom ma ta nufi nata.

___________Cikin satin da Taheer ya tafi Habeey tasha wahala sosai don Saida ta sake kwanciya a asibiti gashi Pappa ya matsa mata ta turo masa da kudi, hakanan a batada lfyr ta samu ta tura masa kudin da Taheer ya bata kusan million of nairas tace ya siya mata gida anan Gombe.
Aikuwa rufeta yayi da fada wai me zatayi da wani gda a Gombe har yana cewa shifa baya fatan ta sake dawowa Gombe tayi zamanta a Dubai kawai tana turo masa kudi yanashan giya yana caca.
Lkcn da aka sallameta daga asibitin suka koma gidan nan ma ba wani sauqi ta samu ba har yanzu tanajin ciwon ciki da bayan dake damunta saidai ba kamar na kwanakin baya ba.

Wayarta da ta dade da mutuwa saboda Kira ta dauka ta jorner a charge ta kunna tana duba Miss calls din sunfi dari biyu, kusan dari da hamsin duk na Taheer ne hakanan tayi murmushi saboda itama zuciyarta tana azabtuwa da rashinsa zuwa yanzu ta fara sabawa da halinsa duk da yanada gundura idan kana tare dashi amma yanada shiga rai.
Bangaren saqonni ta shiga nan ma duk shine ta sauke ajiyar zuciya tare da rafsa tagumi maganganun Mom sunayi mata yawo a kwanyarta, tana shirin tashi wani Kiran ya shigo takai hannunta ta dauka wayar tana dubawa taga shine taja huci tare da kwanciya ta danna pick ta kara a kunnenta tare dayin sallama cikin siririyar muryarta me sanya masa kasala.

Ajiyar zuciya ya jera tafi guda bakwai sannan yace “inata kiranki baki dagawa hankalina ya tashi na dauka fushi kikayi dani sai daga baya Aysher take cemin ashe jikinki ne yaqi dadi har takaiki ga sake kwanciya a asibiti, sannu ya jikin naki?”
Numfashi ta sauke tace “naji sauqi sosai sai ciwon ciki da baya da yaqi barina” da sauri yace “wht? Amma shine kuka dawo gida?” Iska ta fesar tace “to zamuyita zama a asibiti ne Taheer, inasa ran shima zai tafi” qwafa yayi yace “ok Allah yasa ya kk ya kewata ko bakiyi?” Shiru tayi masa, yace “kice wani abu mana hearty koda kince bakyayi bazanji haushinki ba kamar yanda bazanyi mamaki ba saboda nasani baki sona nine kadai na jarabtu nake azabtuwa da soyayyarki take neman aikani lahira”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button