DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[7/29, 9:18 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI ✈️

PAID BOOK

Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200

Account number

0255526235

Fauziyya Tasi’u Umar

GTB

Ko katin waya MTN ta wannan number

09013718241

Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi  daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria.

Episode 30

END OF THE PART ONE

Ta jima a kwance tana tufkawa da warwarewa kafin ta miqe ta dauro alwala tayi nafila raka’a biyu ta me neman gafarar ubangijinta a bisa laifukanta da suke bibiyar rayuwarta.
Wannan dare bata kwanta ba sai bayan sallar asuba ta koma ta kwanta tanajin zuciyarta tanayi Mata zafi tashin hankalinta shine batasan inda zata nufa ba babu inda tasani a cikin garin gombe balle tace zataje, tananan kwance har azahar tanata juyi wayarta da take charge ta qara bugawa tayi qarfin halin miqewa daqyar ta dauko wayar tayi murmushin yaqe tace “Ibrahim Ina cikin aminci kayi hqr kaji don Allah duk ranar da Addah ta sauko ta yafemin ta yarda da qaddarata a matsayin tata ka fadamin kaji…”

Ta qarasa maganar cikin shassheqa numfashi Taheer ya furzar yace “yanzu kina ina?” Saurin sauke wayar tayi saboda ko muryarsa bata qaunar ji shine sanadin faruwar komai, tsorone ya kamashi.
Itakuma ta manna wayar a qirjinta ta koma ta kwanta tana sauke numfashi wannan rana azumin dole tayi kiran duniya Taheer yayi mata taqi dauka sai bincike suka shiga Allah yasa dan Napep din daya daukota na gidane shine yayi masa Jagora har hotel din ya bashi kyauta me kauri ya shiga ciki Koda aka kirata aka sanar da ita mijinta yazo cewa tayi batada appointment dashi.

Saida ya tashi hankalinsu sannan suka rakashi dakin nata yayi knowking bugu biyu ta taso tunaninta  abinci aka kawo mata da hijjabinta qato har qasa ta bude, ja tayi da bsya da sauri tana danna qofar ya riqeta da sauri ya danna ya shiga ya mayar ya rufe yana kallonta cikin tsananin qaunarta da tausayin kansu ya matsa gabanta ta janye tace “don Allah ka tafi Taheer wlh banason ganinka banaso Taheer kaje kawa….”
Cafkarta yayi ya hada bakinsa da nata tanata qoqarin qwacewa shikuma yana qara shigewa jikinta har suka zube a gadon ya janye da sauri yace “ohhhh meye yasa zakiyimin haka habeey zuciyata tana gurinki ke kuma kina qoqarin turamin takaici da wanne zanji ne ya kikeso nayi”

Janyewa ta sakeyi tace “nikuma banason ganinka na tsaneka ya zanyi na cireka cikin qaddarata tunda na hadu dakai qaddarorina suka qara tsanani Taheer nasan badon shegen cikin nan nakaba da mahaifiyata bazata qyamaceni hakaba shikenan itama ka dasa Mata tsanata a kunnena akan idona Addah take cemin ta tsaneni na fice Mata daga gdanta inba hakabs ta tsinemin Taheer nikam nashiga ukuna waye zai soni waye zaiji tausayina…”
Matsawa yayi sosai numfashinsu na bugun juna yace “duk duniya nafi kowa sonki wlh har mahaifiyarki nafita sonki habeey bazan taba gudunki a cikin hayyacina ba kiyi hqr nasan nine silar faruwar komai nima a cikin qaddarata kike”

Shiru yayi na wani dogon lkc kukanta na dukar masa zuciya ya janyota jikinsa ya sanya hannunsa ya shafa cikinta yace “bakici abinci ba kin barmin baby da yunwa ko?” Numfashi taja ta miqe ta diro daga gadon yayi murmushi da yawan Mata ciki muni yake sanyasu itakuwa gwanarsa wani sihirtaccen kyau ta qara, wayarsa ya dauka ya fita ya jima yana waya da Hajiya Dije kakarsu ta wajen uba bai boye mata komai ba yana kuka ya zayyane mata komai itama cikin tausayin kanta da jikokinta tace.
“Kowanne bawa baya wucce qaddararsa Taheer ka kawomin ita har zuwa lkcn da zuciyar mahaifiyarta zatayi sanyi haqiqa yarinyar tana buqatar kulawa idan aka qyaleta ta qara fantsama duniya bazataji kira ba saboda zata cigaba da daukar bata da wani me tausayinta a duniya”

Yaji dadi sosai na yarda kakar tasa ta fahimceshi yanzu ne hankalinsa zai kwanta yakuma ji da rikicin cikin gdansu, abinci ya nema Mata ya dawo ya tararta ta fito a wanka tana tsane jikinta da towel saida numfashinsa ya dauke saboda wani yanayi daya shiga yayi saurin juyawa ya fice saboda baison sake sanyata cikin damuwa yanzu nutsuwa tafi buqata.
Saida ya daidaici ta gama sannan ya dawo ya tarar da ita a saman sallaya ta idar da sallar La’asar ta dago sukayi ido hudu yayi mata murmushi yace “kinfi kyau kina murmushi Hurul ainiy” qasa tayi da kanta ya matsa ya zauna yace “kiyi marnege da wannan Grandny tanacan tana shirya Miki tuwon alkama miyar danyan kuka nasan baby na zaiso tunda shi babansa yakeso”

Kallonsa takeyi har ya bude abincin ya debo a cokali yakai bakinsa ya tauna sannan ya matsa gabanta ya kamo kanta ya dagota ya juye mata a bakinta ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya.
Murmushi yayi ya hada mata tea tanacin abincin tanashan tea din tana kallonsa saida ta qoshi ya qyaleta ya miqe ya fara hade mata kayanta yana zubawa a akwatinta babban ta matsa gabansa tace “ina zamu Taheer nayiwa addahta alqawarin bazan qara zina ba a rayuwata don Allah kada kace zaka mayar dani gdanka ka massheni kamar matarka”

Dagowa yayi ya kalleta yace “nima nayi alqawarin bazan sake tursasaki kiyi abinda bakiso ba a yanzu nutsuwarki nafi buqata Habeey azare zan kaiki gdan kakata wacce ta haifi babana nasan Zaki samu rayuwa me dadi anan har zuwa lkcn da Zaki haihu sai muyi aure mu raini babynmu cikin kulawa da soyayya nasan Granny zata soki saboda ta taba ganin hotonki a wayata ta qare miki kallo tace kina mata yanayi da wani data sani koda yake tace da yayan Abbanmu Sahabi kike mata kama”
Zama tayi tana kallonsa har ya dauki kayan ya fita ya sake dawowa ya kamo hannunta yace muje ko?”

Batayi masa musu ba suka fita ya bude mata suka shiga suka dauki hanya lkc zuwa lkc yana kallon yanda tayi tagumi hannu biyu tana sharar hawaye, basu isa Azare ba sai bayan isha sosai yabi wata hanya.
Itadai gabanta sai faduwa yakeyi saboda tunanin me zataje ta tarar acan din, parking yayi a gaban wani gda babba gaban get din gidan cike da almajirai sunata karbar abinci, yayi horn masu gadi suka bude masa ya shiga Granny tana tsaye a saman bene ta hangosu yana fito da kayan itakuma ta koma gefe ta zauna a saman wani dutse tanata sharar hawaye gabanta naci gaba da faduwa.
Tsugunnawa yayi a gabanta yace “inada tabbacin bazaki taba samun matsala anan ba My Habeey shiyasa na kawoki ki saki ranki kiyi rayuwa me dadi, kamota taji anyi ana cewa “yo karma ta saki ran nata mana basai na qwanqwashi kanta ba” dariya yayi itakuma ta kwantar da kanta a kafadar Granny tanajin gabanta na tsananta faduwa itama Granny faduwa gabanta yakeyi ta shafa kanta tace “ki kwantar da hankalinki kinji Habibatullah insha Allahu zakiyi farin ciki zakiji dadin rayuwarki a gaba farko rayuwarki qunci qarshenta walwala da farin ciki dawwamamme” a haka suka shiga ciki Granny tana cewa“Taheer yanzu babarka ta kirani take fadamin kana neman bijirewa auren Saudat……..”

Tashin hankali kunji fah wata sabuwa Taheer zaiyi aure, wacece Saudat da zai aura? Meye ya San gaban Granny da Habeey ya fadi lkcn da sukayi arba da juna? Shin wai Taheer ma zaiyi biyayya kuwa wa zabin iyayensa? Wannan amsoshin sai a DUBAI PART TWO.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button