DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

Baya Pappa yayi sai yanzu ya fahimci cikin dake jikinta yace “heeee Anitah aure kika daura a Dubai bansani ba munafukar uwarki ta daure miki gindi kikayi aure batare da ansanar Dani ba to wlh yau shari’a ce zata rabamu da ita tunda ta munafurceni”
Tsoro ne ya kama Habeey ta zame daga jikin Taheer tace “Pappa Ina Ibrahim da Idris?” Tabe baki yayi yace “yana gurin munafukar uwarku ba har kudi kika turo mata ta siyi gda ba?” Lamarin duk ya daure Mata kai ta koma ta maqale a bayan Taheer daya zubawa Pappa ido sai hauka yakeyi wai sai yayi qarar Hajar da Taheer tunda suka zuga masa ya ta dawo 9ja bayan bai gama gininsa ba”

Zuciyar Taheer takai wuya yana qara second talatin bai fice a gdan ba zai iya rufe Pappa da duka figar hannun Habeey yayi suka fice daga gdan ya jefata a mota cike da tunani ya samu wani matashin yaro yayi masa yan tambayoyi tana kallon yaron yanayi masa kwatance ya juyo ya shigs motar ya kalleta yaci gaba da tuqinsa suka fice a unguwar suka nufi wata sabuwar unguwa ya kuma fita yayi tambaya sai gashi da wani yaro, Habeey ta zubawa yaron ido yana zuwa sai taga ashe autansu ne Idris yana ganinta yace “lahhh Aunty Habbatullah kece dama dama tun jiya Addah take kuka tana cewa baqin cikinku ne zai kasheta”

Dago jajayen idanunta tayi tace “addah kuma Idris wacce Addan?” Kallonta yakeyi da mamaki yace “munada wata Addah ne bayan mahaifiyarmu…” Rungumeshi tayi ta saki wata ajiyar zuciya tare da kuka a tare tace “dama Ibrahim qarya yayimin yace Addah ta mutu ya tashi hankalina ashe meye yasa yayimin wasa da rayuwar uwata?”
Parking sukayi a wani matsakaicin gida Idris ya fita da gudu ya shiga gdan ya qyarawa Addah da Ibrahim cewa ga Yaya Habbatullah nan ita da wani” miqewa Addah tayi da sauri ta shige wani daki ta kulle suka shigo suka tarar da Ibrahim yanayi mata magiyar ta bude Amma fir taqi matsawa tayi kusa da Ibrahim din tace “nice batason gani ko qanina? Addah ki bude ni inason ganinki inason na tabbatar da lfyrki Addah kada kiyi fushi dani da qaddarata wlh nayi iyakar qoqarina na ganin na tsare mutumcina amma na kasa”

Tun tana magiyar ita kadai har saida Taheer yasa baki amma Addah ta qeqashe tace itafa batason ganin Habbatullah ta fice mata daga gda kafin ta zama ajalinta, Taheer da baqar zuciya ya matsa gabanta yace “ke kowa ma gudunki yakeyi da qaddararki uwar data haifeki ms tana gudunki saboda qaddarar da itace sanadin faruwarta Habeey ni bazan taba gudunki ba kizo mu koma ki haifamin baby na sai muyi aure duniya ai fadine da ita…”
Daga masa hannu tayi cikin kukan nadama da danasani mara amfani tace “dakatamin malam sanda taka uwar tazo tacimin mutunci banji haushi ba nasan sonka takeyi saboda haka bazaka rabani da tawa ba Ina ruwanka inma kasheni zatayi, ka fice Taheer ka fita banason ganinka kaine Taheer Kaine qaddarata kaine ummul aba’isin faruwar komai don Allah ka fita a rayuwata wlh daga tunda nake bantabajin sonka ba balle naji zan iya barin uwata saboda kai”

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[7/28, 8:20 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI ✈️

PAID BOOK

Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200

Account number

0255526235

Fauziyya Tasi’u Umar

GTB

Ko katin waya MTN ta wannan number

09013718241

Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria.

Episode 28

Tsayawa yayi sororo sake da baki yana kallonta ganin yanda take kukan tana yiwa Addah magiya yasashi juyawa ya fice daga gdan ya nufi hanyar da zata mayar dashi garinsu zuciyarsa cunkushe da abubuwa da yawa shidai baisan meye yasa duk abinda ya shafi Habeey take tsaya masa a zuciyarsa ba.
Kai tsaye gda ya nufa saida jami’an tsaron gdan gwamnatin suka tabbatar da shine sannan suka bude masa get ya shiga yayi parking a harabar ajiye motocin ya fito fuskarsa a cunkushe ya nufi cikin gdan parlourn Mom ya shiga ya tarar da ita hakimce ita da yanmatanta biyu Kubrah da Bushirah sai wata da baisan wayece ba.

Suna ganinsa suka miqe suka rungumeshi suna murna shidai ya kasa boye damuwar da yake ciki yaqe kawai yakeyi yana dauke kai saboda kada Mom ta fahimci wani abu, sakinsa sukayi ya matsa ya zauna kusa da Mom ya kama hannunta yace “mom i hope kina lfy?”
Janye hannunta tayi tace “ance tun jiya ka dawo meye ya hanaka isowa gda?” Shafa kansa yayi yace “shigowar dare mukayi kuma tare muke da Babe so banson na barta ita kadai nasan idan nace zan kawota gdannan Zaki iya fada mata mgnr da zata sanya ciwonta tashi…” Katseshi tayi da cewa “wato dana rabaka da yar iskar yarinyar nan baka rabu da itaba ko Taheer wai kaikam wanne irin yarone da bakajin mgn wlh kaji na rantse baka isa ka gurbatamin zuri’a da wannan karuwar yarinyar ba wacce iskancinta ya riqa ya tatura har ta tsallake qasarta ta tafi uwa ba kwaba take sheqe ayarta ba”

Qasa yayi da kansa ya zubawa Mom idanunsa daya kada yayi jajir yace “amma Mom kinsan dai cewa komai yana tafiyane bisa rubutun qaddarar bawa meye yasa kullum baki yiwa yayan wasu fatan alkhairi itama fa yace qaddarorinta ne sukazo Mata a baibai kuma suka hado dani yanzu Mom idan Bushirah ce ko Kubrah suka samu kansu a wannan halin ashe gudunsu kema zakiyi kamar yanda mahaifiyar Habeey ta kasa tsayawa ta dubi yarta me qaunarta da idanun rahma bayan duk abinda ya sameta sanadin uwar tatane, ta sadaukarmin da abu mafi daraja a gurin kowacce ya mace a lkcn da tafi buqatarsa kawai saboda ta ceci rayuwar mahaifiyarta ashe uwarma butulci zatayi mata”

Miqewa yayi yana huci yana hada hanya har ya kusa qofar da zata kaishi bangarensa ya juyo yace “wlh indai irinku ne iyaye masu fifita son zuciyarsa fiye da farin cikin yayansu nikam dama baa halicceni ba Mom meyesa kikeso watsawa muradai na qasane? Hmmm babu komai albishir daya zanyi miki ki shirya daukan jika nanda watanni biyu Habeey da kika tsana tana dauke da cikina watanni bakwai….”
Wata zabura sukayi duka parlourn harda baquwar da baisan wacece ba suka miqe ya kallesu yayi murmushin gidan boss ya shige bangarensa da sauri yanaji Mom ta biyosa amma ya shareta ya shige part dinsa ya kulle ya fada bathroom ya cire kayansa ya fara wankansa yanaji tanata buga qofar ya shareta saboda shi ya qaddara Mom dinsa a matsayin ciwon kansa ya lura duk cikin ysyanta tafi sanya masa ido.

Kwatan abinda takeyi masa bata yiwa Muheed ta takura masa tasa mawa duk wani motsinsa ido, yana gama wankan ya fito ya fara shafa mansa bayan ya gama yasa doguwar rigarsa ya kwanta ya fara kiran wayar Habeey amma bata dagaba, dama baiyi tunanin dagawar tataba ya bude hotunansu da sukayi tare yanata kallo yanajin sanyi a ransa ya rasa irin son da yakewa Habeey komanta birgeshi yakeyi.
Cikinta ya zubawa ido yanajin nutsuwa tana saukar masa shima ya kusa zama daddy yayi ajiyar zuciya tare da kiran wayar kukun gdan ya fada masa abubuwan da yake buqata ya kawo masa ya zauna yana tsakurar abincin hankalinsa gabadaya yana gurin zuciyarsa, yinin ranar bai iya hassalawa kansa komai ba har zuwa dare da yaji ana buga qofarsa ya share duk tunaninsa Mom ce wayarsa ce tayi ring ya dauka sai yaga number Dad dinsa ya kara a kunnensa Dad yace “ance ka dawo ko to kazo parlour ns inason ganinka”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button