JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda ya sauka Benin zuciyarsa kasa nutsuwa tayi hakanan da ya tuno da Meenansa sai ya nemi nutsuwarsa ya rasa zamansa kwanciyarsa tashinsa Meenah ce keyi masa gizo da salon shagwabarta me tsayawa a rai da Hana zuciya sukuni ya rasa irin shaquwar da yayi da ita da bayajinta akan sauran qannensa, da taimakon addu’a ya samu damar ci gaba da aikinsa ya dangana saboda yasan duk nacinsa yanzu bazai samu damar karbarta hanun Mai Martaba ba.
Itama farkon tafiyarsa gabadaya rikice musu tayi suka kasa gane kanta saita zauna tayita kuka idan aka tambayeta meye sai tacce Baffa’am dinta take tunani idan kaga ta saki jiki to Mai Martaba ne ya kirata yasata a gaba yake zolayarta to yanzu zata ware ta kama harkokinta a haka har ta saba da kadaicin rashin Baffanta ta saduda ta saki jiki cikin yan’uwanta Ya’isha da Amrah.
Ya kasance duk safiyar duniya idan su Ya’isha sun tafi makaranta Kareem zaisa a kirata su zauna suyita karatunsu yanajin dadin koya mata saboda nandanan take daukewa a falo suke zama gaban kowa har Mai Martaba suyi karatun indai kaga sun kebe to baqi akayi hayaniya bazatabar karatu ya shiga ba, shiko Muntaz duk sanda zai koya mata saidai yajata Garden su kebe ya rinqa koya mata karatun bokon shima yanajin dadin koya mata Amma dake yasa almundahana a ransa duk yanda zatakai da ganewa sai yace bata gane komai ba haka zatayita qunci ta Hana kanta sakewa saita iya turanci saboda baqin nacinta har tafi mayar da hankali akan bokon fiye da karatun addinin Amma kullum a bata iyaba take.
Hikimarsa shine idan ta matsa da son saita iya to zaiyi amfani da damar wajen cimma burinsa, babban abinda yake damun Muntaz yanda Kareem yake sanyawa duk motsita idanu sau tari idan suna garden din suna darasi shikuma sai yaje can gefe ya kama buga qwallo Sarai Muntaz ya fahimci sabodashi yakeyin hakan wannan dalilin yasa ya tattara koyarwar ya watsar.
Tayi nacin tayi nacin harta hqr gashi jarabawar WAEC din da zasu zana da Baffa’am dinta yasa Mai Martaba ya biya mata takusa dama da lesson din take gane abubuwa. Tanason bawa Baffa’am dinta mamaki musamman da yace indai batamai da hankali taci WAEC ba rugarsu zai mayar da ita wannan abu ya qara tashin hankalinta ta rasa abinda keyi mata dadi.
Yau ma kamar kullum suna zaune a daki Ya’isha na chat Amrah na karatun novel itakuma ta rafsa uban tagumi sai tsiyayar hawaye takeyi batason tayi asarar wannan damar Amma ta lura damar batasonta kufcewa zatayi…….
Dagowa tayi tana sauke numfashi Ya’isha tace “kina damun kanki da karatun nan nifa da Mai Martaba zai yarda Allah inayin candy aure zanyi miqewa Amrah tayi tace “mema kikaji da son aure bakiga kaya ba Nifa ko a yarda ko kar a yarda Allah sai anmin aure na gaji da cin na Allah ya isa” tabe baki Ya’isha tayi tace “waisu tsoffin nan so suke su mayar damu bahuna nifa Allah badon kin takura ba da babu abinda zaisa na zubar da cikina gara susan mun girma munsan dadin maza su auraddamu ko su dauki jikokin soyayya”
Katsesu Juhud tayi da cewa “nikam don Allah kubani mafita Allah nafison karatun da komai ni nasan ma Baffa’am dina bazaimin aure ba” miqewa Ya’isha tayi tace “common baby tashi muje Ni nasan bro gajiya yayi da aikin banza” da jin dadinta ta miqe suka rankaya zuwa dakin Muntaz Yana kwance samsn gadonsa da system a gabansa Yana kallon wani BF suka shigo.
Rufewa yayi ya lumshe idonsa cikin yanayi me ban tausayi Juhud tace “duk da bansan laifina gareka ba Ya Muntaz Ina mai baka hqr don Allah ka taimaka kaci gaba da yimin lesson dinnan wlh Baffa’am dina yace idan na Fadi jarabawa saiya mayar dani rugarmu Kuma idan na koma kasheni zasui……” Murmushin jin dadi yayi dama tazo masa har daka ya tashi zaune yana sake zubawa qaramin bakinta idanu yanda take sarrafashi ya bashi sha’awar ya tsotsa ya lashe lips dinsa ya miqe zaune yana kallonta harta gama yaja numfashi tare da shafa sumarsa yace.
Karatun addini shine akeyinsa kyauta ko sadaka Amma na boko dole sai an kashe kudi masu nauyi Juhud bakida kudin biyana anma kinada kadarar da tafi kudi a gurina idan kin amince zaki mallakamin kanki da lkcnki nikuma na amince zan dauki duk wani lkc na na baki shi domin samun damar cin jarabawar WAEC din da zaku zana amatsayinki na mara background din nunawa saa ba iyakar lesson ba hatta abubuwan da suka shafi kudi zanyi mikishi daga naira daya har zuwa fan taba sama indai kin amince……”
Kallonsa sukayi da rashin fahimta suks kslli juna Ya’isha da alamu suka nuna ta fahimci wani abu tace “Amma ya Muntaz ai ba ita tasaka aikin nan ba Big Cele ne kai kana ganin hakan zai yuwu idan yasani kana ganin zakaksi labari?” Miqewa yayi yana murmushi yace “to saime don ya gane ai yasan baa aikin banza a duniya bayan hakama shidin meye bayayi akwai ma dan bariki irinsa ne da idons nashs kamasa ya dannewa mace kai Yana soka mata wutsiya idan nayi yunqurin tonawa yace zai fasamin kai da Gum balle ma ni bazan taba shigarta ba kawai zan hutane da ita common Ya’isha ki ganar da ita itama zataji dadi rayuwar duniya daga Kano sai Habuja aljanna tamai raboce”……
Bai jira abinda zasuce ba ya fice daga dakin yabarsu zaune da sakakken baki suna kallon kallo ta kalli Ya’isha tace “meye yake nufi da inada kadarar da tafi kudi Ya’isha don Allah Amrah idan kun gane ku ganar dani nikam daqiqiya ce ban gane komai ba” wata iska Ya’isha ta furzar tace “akwai matsala ne Juhud muje rabuda wannan dan iskan ni dama nasan abinda yaketa yiwa raragefe kenan” fita sukayi har zuwa lkcn kanta a kulle yake kalaman nasa sunayi mata yawo a qwanya saidai ta kasa gane inda zatayi musu matsugunni Baffa’am dinta bariki yana taba bariki? Meye ma ma’anar barikin?”
Da wannan tunanin suka shiga gda tun daga nesa suka hango Kareem tsaye jikin mota ya zuba musu ido kamar me nazarinsu har suka qaraso suka giftashi kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa “Aminah” taji an kirata da asalin sunanta turus sukaja suka tsaya dukkansu ya tako cikin takunsa na isa ya iso gabanta ya kalli qannen nasa dukka suka watse ya rage daga ita saishi, hannu yasa ya dago kanta ta lumshe idonta tana shaqar qamshin turarensa me tsayawa a rai yaja numfashi tare da furzar da wata iska me zafi yace “duk da kasancewata abin gudu a gurinki saboda Ina doraki akan tafarkin daidai Aminatuh bazan fasa fada miki ba Babu biyayya gurin abokin halitta wajen sabawa ubangiji zanso Kuma zanyi alfahari idan ya kasance nasihar da nakeyi miki daga ranar da kika tsinci kanki cikin wannan ahli me rangwamen tarbiyyar islama ta zame miki abar tunawa a duk lkcn da wani abokin halitta ya gayyaceki domin aikata sabon Allah.
Nasani cikin watannan da kika samu goyan baya daga Momy kin fara biyewa su Ya’isha kina binsu kuna fita chilling kune har Dikko Club wai abin takaicin hardake a cikin yan shiga rawa bama ki tsaya iyakar kallo ba”
Kallonsa tayi da sauri idanunta ya ciko da qwallar da tun dazu take maqale jikinta ya dauki rawa, murmushi yayi yace meye naki na firgita bayan Baffa’am dinki baisan rayuwar da kika zabawa kanki ba?” Sake firgita tayi bakinta na rawa tanason mgn ya katseta da hannunsa yace “karkicemin komai Aminah kinji dadin zuwa club har kina bada tabbacin gobe ma zaki koma ko?”
Girgiza masa kai tayi haqoranta na rawa tunaninta Ina yasan wannan sirrin da sukayishi iyakar su uku sukayi alqawarin bazasu fadawa kowa ba?” Murmushi yayi ya kama hannunta yace “inasonki da gasken gaske Juhud meye ribarki idan aka tashi mahaifanki aka nuna musu ke matsayin yar rawar Club?”
Girgiza masa kai tayi jikinta duk yayi sanyi tace “Allah Amrah ce tajani tace dole saina shiga Kuma Dana shigama tsayawa nayi ban iya irin rawar da sukeyi ba”