JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL
Juyowar da zatayi suka hada ido da Rasheed dake tsaye jikin swimming pool kallon da yake mata ne yasata kama in…inar qarfi da yaji tace “am…in….” Ji tayi ya warce wayar ya duba yaga number qanin nasa yana mgn Yana cewa “hello….. Luv…..” Qit ya kashe wayar ya jefa a aljihunsa ya juya yabar gurin daga Ya’isha dake qarasowa ta dafata tace “wai me kikeyi ne anata nemanki” juyowa tayi idanunta ya ciko da qwallah tace “ya qwace wayar Amrah….” Binsa sukayi da kallo Ya’isha tace “hmmm wannan mutumin dan rainin hankalin mutumin wlh bashi da mutumci yanzu duk hotunan da mukayi sun tashi a banza kenan?”
Qwafa Amrah tayi tace “kuma duk baqin cikinsa bazamu fass shagalinmu ba Allah yasa ba layina bane akai daya cuceni” janta sukayi suka shiga filin itadai yaqe kawai takeyiwa mutane har takwas taron ya tashi suka shiga gda ta shige daki ta kwanta tana mayar da numfashi.
Da wayar Ya’isha Kareem ya sake kiranta yake tambayarta Ina wayarta ne yanata Kira a kashe taja fasali tace “Baffa’am ya qwace tawa ta Amrah ce nakesa layin itanma dazun ya qwaceta” wata iska ya furzar yace “ina Gsky abin nasa ya fara yawa fah banason shigarmin hanci da qudundunen nan da yakeyi Ina ganin girmansa kada azo ayi babu dadi zan fadawa Mai Martaba ya dakatar dashi gsky na gaji duk yabi ya takuraki to ko hsihuwarki yayi kikakai yanzu ai ya qyaleki balle a sama yaganki” itadai batace komai ba saboda itanma duk kawaicinta da kararta Baffa’am din nata ya fara duba juriyarta.
Satinsu biyu da Candy samarin Ya’isha da Amrah suka aiko neman aurensu da farko Mai Martaba yaqi amsar batun a cewarsa karatu zasuyi Alh Ibrahim wani amininsa shine ya sameshi ya bashi shawarar tunda sun nuna auren sukeso yayi musu ba lallai sai mace a gdan iyaye zatayi karatu ba a gdan mijinta ma zata iya karatunta da farko bai dauki mgnr ba saida Addah Abulle ta sake samunsa da mgnr Kareem fah ya matsa akan mgnr aure da Momy da ita da Ya Arman sune suka sameshi suka rinqa nuna masa abin hakan suna nuna masa Kareem namiji ne Kuma yanada kawaici tunda har ya fito da maitarsa ayi masa kada azo a samu matsala.
Badon yaso ba ya amshi shawarar tasu dake dama an gama shirya komai na baikon Rasheed da Zulaihat hakanan ya Kuma bada maqudan kudade aka shiga kasuwa aka sake yo siyayyar baikon Kareem da Meenah Meenah batasan meye akeyi ba ranar baikon korasu akayi Katsina gdansu Addah Abulle acan suka yini suna tantalbadedensu akatsai da ranar aure Rasheed da Zulaihat wata biyu masu zuwa ya kama bayan azumi da sati uku dake azumin ya rage saura kwanaki bakwai ne sukuna akasa wata shidda saboda an qiyasta abinne da yanda zaizo daidai da hutun shekarar Kareem din ayi bikin ysnana ya dauki matarsa su tafi.
Ranar farin ciki gurin Juhud da Kareem kamar su hadiye juna ta waya inda Rasheed yayi yinin qunci da baqin ciki a qarshe ma daki ya shiga ya kulle kansa yini sur har dare har safiya bai fito ba Mom ce ta kirata tace taje ta duba Baffa’am dinta tun jiya bai fito ba, bataso ba batason haduwa dashi tsoronsa takeji batasan da wacce irin fuska zai kalleta ba, hijjab dinta ta dauka ta Sanya ta fita ta nufi part din nasa tun daga falo ta fahimci akwai matsala kaca² ta tarar dashi gabanta ya fadi ganin kwalaben wine da wasu qananun kwalabe ta matsa ta dauki daya ta duba tare da dafe qirji da sauri tace “A’uzubillahi Baffa’am Alcohol kakesha?” Tsorone ya sarqeta takai hannunta qofar tana bugawa kusan 20 minutes bataji motsi ba murdawa tayi tajita a kulle ta rinqa bugawa da dukkan qarfinta Amma shiru dube dube ta farayi a falon can ta hango mukullaye a hade ta dauka da sauri ta fara gwadawa cikin saa na qarshen da tasa ya bude qofar ta tura da sauri, toshe hancinta tayi saboda warin daya daki hancinta takai dubanta inda ta hangeshi kwance a qasa cikin amai ta saki qara tana cewa “innanillahi meye hakan meye ya sameshi?” Matsawa tayi ta shiga jijjigashi Amma kamar tana jijjiga dutse daidai lkcn Momy da taji shirun tayi yawa ta shigo ganinsa a wannan yanayin yasata sakin ihu tace “Abdulrasheed meye hakan bakada lfy ka kulle kanka a daki zaka kashe kanka…..”
Oum Hairan
[7/22, 6:51 PM] Oum Hairan: JH016 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki
Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566
Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde
Gabadaya gidan ya rude Big Cele babu lfy Mai Martaba dakansa yazo suka daukeshi da likitan gdan suks nufi asibiti dashi suka fara bashi kulawa sosai likitan ya kadu dayin hoton zuciyarsa da yaga ta kumbura jininsa ya hau fiye da misali tashin hankalinsa ya nunku ya fito Yana sharce gumi iyakar saninsa Abdulrasheed ba mutum ne me shiga sabgar mutane ba balle su Dora masa damuwa to meye yaja asalin damuwar tasa?
Da wannan tunanin ya fito ya sami su Mom a zaune suna ganinsa suka miqe ya sake share gumi ya dubi Mom yace “dama Rasheed yanada heart issue ne?” Da sauri suka kalleshi Mai Martaba yace “aa bashida ita” iska likitan ya furzar yace “to mgn ta gsky akwai abinda yasa a ransa da yakecin zuciyarsa har yayi mata Ramin da ciwo ya shigeta hoton da nayi masa ya nuna cewa zuciyarsa ce ta kumbura jininsa yayi mugun hawa fiye da misali nikam lamarin ya firgitani meye damuwarsa meye yasa a ransa da yake neman salwantar da rayuwarsa akansa?”
Goge gumi Mai Martaba yayi ya dubi likitan yace damuwa Kuma a Rasheed din to wacce irin damuwa ce wannan nikam bansan irin yaron nan ba zurfin cikinsa yayi yawa” Mom ce tace “kuma ba akan yarinyar nan bane da yace bayaso kasanshi fah da baqar gaba idan yaqi abu zai iya komai akansa Mai Martaba ka duba lamarin Rasheed fah da Zulai……” Daganta hannu yayi yace “dakata Ayshatu indai akan wannan ne to zan tanadi likkafanin suturarsa don wlh bazan watsawa zuminci baqar toka ba ko zai mutu saina daura aurensa da Zulaihat…….”
Kwanansa goma a asibitin duk sanda zasuje dubashi daya ganta saiya lumshe idonsa bazai bude ba harsai ta fita a dakin maganar duniya bazai kulata ba tun abin na damunta har ya daina damunta da zugar qannensa da suketa famfata akan kada ta kuskura ta bashi qofar da zai gane tanajin tausayinsa zai kaita ya baro ne qila ma ba aurenta zaiyi ba Kuma ma yaushe zata saki saurayi ta kama tuzuru tuzurun ma me Shirin auren wata a fari ba itaba, quruciya da wauta da rashin mafadi ya hanata gane kuskuren da take qoqarin tafkawa Wanda ita kadai takeda ikon canzashi hakanan akaci gaba da tafiya har yaji sauqi aka sallamoshi kwanansa Tara da sallama ya tattara nasa ya nasa yabar gdan batare da kowa yasan da tafiyar tasa ba koda ala fada mata ya tafi Saida yaji babu dadi a ranta Amma zugar su Ya’isha ta hanata saukar da kanta a gefe Kuma da sabon haukanta na dokar da Kareem ya kafa mata cewa indai namiji ba muharraminta bane to ya haramta mata mu’amala dashi wannan dalilin yasa tanason taje ga Baffa’am din nata Amma babu dama gani take kamar Allah ma fushi zaiyi da ita ta karya dokar mijinta.