JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Zama tayi tana hada masa tea din tana cewa “mom tace idan na gama naje mu gaisa da baqin Mali sunzo tun jiya sunata buga sashin nan ka Hana a budensu” yasan da hakan shiyasa baice komai ba ya rinqa janta da hira Saida ya gama yayi wanka sannan suka fito tare sunsha kyau na ban mamaki suna fitowa da ango Kareem suka fara kicibis sukayi musabaha ya tambayesa aiki shikuma ya tambayesa jiki itadai gaba tayi saboda zuwa lkcn wani haushin Kareem din takeji yanda yake nacin kallonta.
Ta rigashi shiga tana shiga parlourn Hajiya Bilki da su Nana da sauran mutanen suka fara watsewa ta tsaya sake da baki kawai sai tajiyo a bayanta wata mata na cewa “ai wannan kina ganinta kyaun dan maciji baqar annoba kenan yanzu kina cika wargi zaki tsinci kanki a Ramin kabari ta tsotse bargo ta lashe kurwa”
Juyawa tayi ta zubawa me mgnr ido hawaye wani nabin wani shiyasa jiya taqi fitowa saboda gudun abinda zatayi gamo dashi a wannan taron bikin, ji tayi an saqalo qugunta taja ajiyar zuciya tare da share hawayenta da gefen mayafinta ya zagayo gabanta yace “dame Kuma kika gamu daga fitowarki” murmushi tayi tayi gaba ya riqo hannunta yace “wlh bazaki shigaba saikin fadamin uban waye ya tabaki?” Tana Shirin mgn Ya’isha tace “wato Ya Rasheed yau zaayi kutmar uba a gidannan…..” Fuuuuuu tayi gaba tana zuwa ta dauke Hajiya Bilki da Mari ta kama qunduma mata ashar abinka da bakatsina yau jini ya motsa bala’i takeyi tana dara nandanan gurin ya kacame taron biki ya koma taron fada shidai Rasheed baisan meye yake faruwa ba Saida yaji tana cewa “aikin banza aikin wofi har wasu kune zaku dubi Meenah ku rinqa jifanta da miyagun kalamai dama ai na dade Ina jiran damar cin bura uban kowannen shege a gdannan idan kuna taqamar ance muku itan mayya ce to ai gara ita ansan wacece ita ku waye yasan asalinku yayan bayi kawai Wanda tsiya da munafurci ta Haifa ta goya ta shayar Bilki kibi a sannu halwa ce dake gaba da baya Kuma mata ba maza ba aure Big Cele yace bayaso bazai auro irin masifa irin jaraba ba wlh dadai auren halwarki gara auren mayyah so million indai msita irinta Meenah ce Kuma Meenah ta zame muku ciwon ido a gdannan kowanne dan iska saidai yaganta yabarta idan da meja Kuma yaja shima ya wullah barzahu kamar yanda Zulaihat data dage saita shiga tsakanin rabo ta fece, yan iskan banza munafukan wofi”

Tunda yaji dalilin rikicin jikinsa ke tsuma ran maza ya baci idanunsa suka kada sukayi jawur ya dubi Juhud data durqushe a qasa taketa aikin kuka me cin zuciya ya juya ya dubi mutanen kowa jikinsa ya hau karkari baice komai ba baiwa kowa mgn ba ya figi hannunta da qarfi suka fice daga falon gurin Mom din da baajeba kenan ya mayar da ita sashinsu ya kulle ya zauna yanata huci ya miqe ya zauna yafi sau ashirin sannan Kiran Mai Martaba ya shigo yayi jifa da wayar ta tarwatse ya tashi ya shiga dakinsa batasan me yayi ba ya fito dauke da jakankuna manya guda biyu ya fice ya jefa a mota daidai lkcn da yake Sanya kayan a mota Mai Martaba ya iso gurin yace “ya subhanallah meye Kuma hakan Ina zaka?” Juyowa yayi idanunsa sun kada sunyi jawur ya dubeshi ya kawar dakai Alh Aminu ne ya matso shima lkcn Rasheed din ya koma cikin gdan ya figo hannun Meenah ko dankwali Babu akanta Mai Martaba daya fahimci barin gidan yake niyyar yi yace “wai ba mgn nakeyi maka bane” a fusace ya juyo yace “banaji Mai Martaba banji abinda kaceba ka kauce kabani guri yau kam ko baku koreni ba na gama zaman gdan sarautar nan akan matata zan iya hqr da komai…..”
Muryarsa ce ta sarqe ya jefata a mota ya kulle har yanzu kuka takeyi yama kasa rarrashinta ya sake kallon Alh Aminu ya nunasa da yatsa yace “ka sanar da munafukar matarka ni Abdulrasheed nafi qarfin yayanta a aure kun bani Zulaihat banaso na karba Allah ya dubeni ya kasheta kun bani Hidaya na sakar muku kayarku shine yanzu zaku liqamin bazawara kwancen wasu saboda kun Mai dani jani talau waima ni kadaine da namiji ne a gidannan Ina Salman Ina Arman Ina Kareem Ina Muntaz hatta Urwat kukayiwa aure zama zaiyi da matarsa saini akanme zaku sanyawa rayuwata idanu ne banaso na fada muku banaso wlh tallahi zanci mutumcin duk ubanda ya qara tunkarata da mgnr aure auren banza auren wofi da har zaku sanyawa matata tsura akansa aiba ita ta hanani ba nine naga batada tamka bare mahadi, Abu na qarshe ka fadawa Bilki ta kiyayi dawowata gdannan Kuma ta shirya Amsa Kira kotu saita fadamin uban wa matata ta kashe da take fadawa duniya cewa in mutum ya cika rabar Meenah saidai yajishi a Ramin kabari?…..”

Sosai Mai Martaba ya girgiza da yanayin Rasheed din yasan tabbas yau yakai qarshe akwai gagarumar matsala idan yabarshi yabar gidan dama Meenah ce zatake kawoshi tunda shi dama asalinsa bayada ra’ayin zaman gdan sarautar to ya dauke abarsa meye Kuma zaisa suganshi? Mai martaba na Shirin mgn Mom ta iso gurin ita da wasu mata su uku dole tasashi yin shiru ta kama hannun Rasheed tajashi gefe sun jima suna bugawa kafin ta shawo kan kayanta Yana kuka kamar wani yaron goye daqyar ta lallabashi ya yarda zaibar Meenah a gidan sarautar Amma da angama biki da ita zai tafi.
Zuwa tayi ta fito da ita a mota ta janye mata sumar data rufe mata fuska tana ganin Mom din ta fada jikinta ta sake rushewa da kuka itama hawaye ta share tana tausayawa rayuwar Meenah Babu uwa Babu uba babu shaqiqin dan’uwan da zata zanta dashi taji dadi ga rayuwar taqi mata dadi wata murya taji ta bayansu tace “kiyi hqr Aminatuh komai yayi tsanani sauqi na zuwa hakanan Allah yake jarabta bayinsa zababbu domin ya gwada imaninsu ba sonki ne bayayi ba qaunace ta kawo miki hakan bantaba ganin Wanda akayiwa irin wannan qazafin ya qare rayuwa a wulaqance ba ko baizama wani ba zai samu yardar Allah”
Juyawa tayi ta zubawa matar idanu gabanta ya yanke yabada wani rass ta janye jikin Mom da sauri tana qara kallon matar tare da langwabar dakai a rayuwarta nata taba ganin kamar tsagin Kara irin wannan ba kama haske da jiki inda kasan innatun ta a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace “mom wannan fah?”

Dadine ya cika mom ganin ta fara warewa tace “Wannan Kharimatu kenan qanwata ce babanmu daya daga Mali suke ita da Mamanta Hamida kinganta can” juyawa tayi ta kalli dattijuwar matar da tayi tsufan jin dadi fatar nan kamar a matsa a tatsi jini tana sanye ds farin tabarau tayi mata murmushi ta bude mata hannu ta fada jikin matar hakanan takejin wata nutsuwa na ratsata da kwanciya a jikin Kumbo Hami Kumbo Hami ta shafa kanta tace “kiyi hqr jikata zakiga ribatai a gaba munci wannan baqin cikin nida babbar yata Aysho tana jaririya a tsumman goyo aka koremu daga gdan babansu Aishatu surukarki……” Kuka ne ya qwacewa Kumbo Hami ta share qwallarta tace “saboda qin jini da yanayin qabila wannan abu yake bibiyarmu kamar garin Bodde wani babban garine da yake cikin Qasar Mali So garin yazamo kamar Biddah a Nigeria sunyi qaurin sunan asiri da maita Wanda ba dukkan garinne suke da wannan hali ba su masu yinma sune kaso mafi qanqanta.
Baffana attajiri ne a garinmu a zahiri bama maita bama tsafi Amma saboda dukiyarsa yasa ake cewa shine shugaban mayun garinmu Baffa Garbu wato babansu Aishatu surukarki yaron babana ne hakan yasa yabashi aurena tunda nazo garin lkcn baa auro uwayen su Aishatu ba matan gidan suka tsangwamin Kuma Allah dabawa mugu dama haka akayita rashe rashe a gabar tun baa yarda har suka amince da gaske ni mayyace hakanan na haifi Aysho ranar dana haifeta Garbu bayanan uwarsa tasa aka daukemu akaje bayan gari aka yasar damu daqyar na iya komawa Mali daga Senegal naci gaba da rainon Aysho Garbu nasona Amma bashida ikon dawo dani domin babana ya fusata hakan yasa Aysho nada shekara goma ya karbeta a gurina sai labari naji ya auradda ita ga dan qanwarsa ya taho da ita Nigeria tun daga wannan Rana nakebi akaini inganta nakasa samun dama dakaina nazo Nigeria neman Ayshatu na ban dace ba a qarshe dai nama hqr domin jikina na bani Ayshatu bata raye don da tana raye inni ban nemeta ba ita zata nemeni, bayan na rasa Ayshatu ne qulafucina da son naganta yasa na komawa Alh Garbu shine har na sake haihuwar Kharimatu, Aminatuh yanzun komai ya wucce bayan ansha wuya kema idan kikayi hqr watarana zai wucce”………..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button