Lu’u Lu’u 5

Murmusawa malamin yayi sannan yace _” Rauni, tana da rauni, dan bata iya kare kanta ga duk wani abun cutarwa.”_
Ajiyar zuciya Umad ya sauke ya mik’e daga rusunawar da yayi 脿 ranshi yana fad’in” Ba ita ba ce, wannan ba zata tab’a zama Zafeera da ake fad’a ba.”
Sake kafeta yayi da ido yace “Jiya da dare me ya kaiki d’akina?”
Zaro ido tayi tana kallon shi kamar taga bak’uwar hallita, sororo tayi ta rasa bakin magana, kallonta ya sake yi yace “Cire hular kanki, ki zama daidai da sauran d’aliban.”
Tsura masa ido tayi a ranta tana tunanin watak’ila fa son takura mata yake saboda yanda suka fara had’uwa, to amma ita ma zata ji dashi a haka, a hankali tasa hannu ta cire hular ta kan ta.
D’an zaro ido yayi yace” What?”
Jinjina kai yayi a dak’ile yace” Kin kad’e.”
A sanyaye ta turo baki gaba tace “Sorry sir.”
Juyawa yayi ya kalleta yana rumgume hannaye da mamakin yanda ta gagara mik’ewa tsaye sannan ta masa magana, ita wacece? Sauran d’aliban ya kalla yana sauke hannayenshi daga k’irji yace “D’alibai, sunana Umad Wudar, sabon mai koyar da ku, ina fata zaku bani had’in kai mu k’arasa zangon shekarar nan daku lafiya, ina so ku d’auke ni a matsayin malaminku mai sauk’in kai a aji, amma a wajen aji zamu iya zama abokai, hakan zai k’ara mana fahimtar juna kuma ku ji a ranku daidai na ke daku, kun fahimta.”
A tare cikin d’aga sauti suka ce” E malam.”
Jinjina kai yayi ya nuna d’alibin farko yace” Ku gabatar min da kan ku.”
D’ai bayan d’aya suka dinga mik’ewa suna fad’in sunan su, saida aka kawo kan Ayam ta mik’e ta fara fad’in” Ay…”
Da hannu ya mata alamar zauna tare da fad’in” Me ye abun dad’i a sunan naki da zan ji shi sau biyu? ”
Idonta tar a cikin na shi tace” Sorry sir.”
Girgiza kai yayi tare da jan tsaki ya kalli Deeyam dake bayan ta yace” Uhum!”
Mik’ewa tayi ta fad’i sunanta, har zata zauna yace” Ana koyar daku turanci ne a nan?”
Girgiza kai tayi tace” A’a malam.”
Kallon Ayam yayi ya yatsina fuska a zuciyarshi yace” Gidan uban wa ta iya sorryn?”
Haka aka gama gabatarwa ya shiga darasinshi ba tare da b’ata lokaci ba, awa uku suka d’auka ba hutu ba shan iska, gashi in suka had’a ido da ita sai ya galla mata harara, ita kuma haka kawai taji kamar ta samu abokin wasanta, ta k’i d’auke idonta daga kan shi sai binshi da kallo take.
Saida ya dubi agogon dake tsintsiyar hannunshi sannan yace” D’alibai ina ga anan zamu dakata, shin da mai tambaya a darasinmu? Ko kuma wanda bai gane wani abu ba?”
Girgiza kai sukayi dan magana ta gaskiya sun fahimci darasin shi sala-sala, dan haka da ya ga babu mai tambaya ya juya da niyyar tattara nashi ya nashi.
K’afa d’aya kan d’aya ta d’ora ta rumgume hannaye a k’irji tace” Sir ina da tambaya?”
Wani iska ya feso ba tare daya juyo ba dan yasan ita ce, saida ya sauke nufarfashi ya saita nutsuwarsa ya had’e b’acin ranshi sannan ya juyo a dak’ile yace” Uhum.”
Duk da ba ita yake kallo ba sai yaji gabansa fad’uwa yake kamar mai jin tsoron tambayar da zatayi, cikin siriryar muryarta tace” Sir, indai har dorinar ruwa kakkausan jiki ne da ita ta yanda alburushi baya mata illa, kenan wane irin makami ne zai iya cutar da ita kai tsaye?”
Kallonta yayi wannan karan kallo irin na k’urilla, kamar sub’utar baki yace da ita” Bomb.”
Da mamaki a fuskarta tace” To amma yallab’ai ai mu ba’a yarje mana aiki da bomb ba.”
Wani tsakin ya kuma ja ya juya zai d’auki jakarshi ta sake fad’in” Yallab’ai tambaya ta gaba?”
A hassale ya juyo yace” Ina jinki.”
Cike da son danne dariyarta tace” Ka fad’a mana zakanya tafi zaki iya farauta, me yasa to duk da shi ne namiji kuma sarki?”
Tsurawa fuskarta ido yayi dan ya fahimci ba shashashan tambayoyi take yi ba, cikin d’an saita muryarsa yace” Saboda shi zaki baya son jin rauni a jikinshi, sannan yana da son hutu kamar yanda yake da jin izza ksancewarsa sarki.”
Jinjina kai tayi sannan ta sake fad’in” To amma kuma me yasa zaki baya mu’amula da zakanyar da bata kusa cimmasa a shekaru ba?”
Tarr! Ya kalli k’wayar idonta mai kama data mage a cikin dare, sauran d’aliban ya kalla sannan ya kalleta yace” A nan ajin nasan babu wacce ko wanda bai balaga ba ko?”
Ihu suka saka tare da fad’in” E yallab’ai.”
Jinjina kai yayi fuskarshi ba alamar fara’a sannan ya sake kallonta yace” Zaki ai sarki ne, jarumtarsa da yarda da kanshi yasa baya tarayya da wacce yasan ba zata iya d’aukarsa ba.”
Cike da gadara ya juya ya d’auki jakarsa inda ajin ya kaure da ihu da maganganu, saida ya fita a ajin Ayam ta mik’e tsaye akan teburin tayi wata irin k’ara tare da tintserewa da dariya tace” Yan mata wai kun yarda?”
Duk yan matan ajin suka amsa mata da” A’a.”
Wata ihu ta sake yi tace” Ni ma ban yarda ba, abinda na yarda da shi shine mace rijiya ce, kowace irin guga aka zura mana zamu karb’a kuma mu bada ruwa.”
Caraf a kunnen Umad da bai k’arasa fita ba, juyowa yayi ya kalleta, samun kanshi yayi da sauke idonshi kan ‘yan tsiraun nonuwanta dake cikin rigar kayan makarantar, yan firit da su ta yanda zai iya had’esu duka biyu a tafin hannunshi kuma ba lallai su cika masa hannu ba, a hakan ma dan yana tunanin ta saka bras wacce zata k’ara mata aukinsu, girgiza kai kawai ya sake yi yana jan tsaki yace “Baki san me zaki yake nufi ba.”
Keb’antaccen gurin cin abincin malamai ya nufa, bayan ya gabatar da abinda yake da buk’ata sai kuma ya kasa ci ya tsaya amsa waya, Haman ne ya tambaye shi “To ya sabon aikin na ka?”
Girgza kai yayi yace “Ba dad’i.”
Dariya yayi daga b’angrenshi yace “To amma ka fara abinda ya kai ka ne? Akwai wani abu daka fara samu?”
Shiru yayi tare da sauke ajiyar zuciya, jin bai amsa mishi ba yasa Haman sake fad’in “Lafiya ko Umad?”
Shafa sumar kanshi yayi wacce har yanzu yake takaicin rabashi da ita da akayi sannan yace “Tana jaririya fa ta b’ata, kuma babu wani wanda yasan wani abu a kan ta, ta ina zan ma fara nemanta a Larhjadin? ”
Dogon tsaki ya ja wanda hakan kamar d’abi’arsa ce kafin yace “Ya binciken da na saka ka? Ka samu wani abu ne ?”
Cike dta karsashi yace “E yallab’ai, yanzu haka ma zan je wajen wani ne dan samun wasu bayanai.”
Jinjina kai yayi yana shafa sajenshi yace “Duk yanda ake ciki ka sanar min.”