Ni da Dr. Sadeeq

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 11&12

BOOK ONE 📖

Story & written by
Mommyn fareesa

wannan shafin nakine halak malak kiyi yadda kikeso dashi
zee hamis wada
Ina yinki over tawan ana tare insha Allah🥰🥰💖💞

🅿️11&12

……….yana shiga cikin toilet d’in” yaganta zaune kan tiles rik’e da k’afarta tana kuka”
yatsina fuska yayi yana kauda kansa yace”.ke lafiya?”dan Allah k’afata!ciwo takeyi dana fad’i”k’aramar yarinya ce ke dazaki fad’i?”amma ai tsotsai baisan yaro ko babba ba”wlh kyankyaso nagani karya koma hawan mun jiki”tafad’a tana k’ara rushewa da kuka”wata doguwar tsuka dr sadeeq yasaki yana hararar ta”

Ahhhhhh!wayyo Allah tafad’a tana k’ok’arin kamo k’afafuwansa”yyi saurin yin baya yana cewa “ke meke damunki?”

zai koma hawamun jiki”sai ki tashi kifita kibani waje”ni bana iya tashi ai”sai Ayi yaya kenan?”

ka kira wata afiddani mana”sbd ga d’an aikenki ko?”dan Allah kayi hak’uri wlh da zafi”karnaje na zama gurguwa”

ai garama ki nakasa kowama ya huta”kuka tasake fashewa dashi”
rasa yamazaiyi da ita yayi”

yanajan tsaki ya nad’e hannun rigarsa ta suit”saidai kawai taji yayi sama da ita”

Atsorace ta bud’e idanuwanta suka had’a ido”yabanko mata harara yanajan tsaki yafito da ita”saman wata kujera dabata wuce 2 seeter ya wurgata akai….yana mamakin rashin nauyinta”

Dole nayi wanka, nakuma wanke hannuna”sbd na tab’a kazamin jikinki”

sannan karki koma zuwa min anan da parsenol dressing”kinji kobaki jiba?”

Idanda zaka taimakeni kadubamun k'afar ka kuma sallameni aiki anan ,ka kaikani wani sashe "dazanfi jin dad'in hakan"

bazaki samu duka ko wane ba”yana fad’in hakan yaja tsaki yazauna”tele phone nasa ya d’auka yakira murtala”

ka kiramun dr amina”dg haka ya ya ajiye tale phone d’in”ya wuce toilet ya wanke hannu yafito”

Aysha na zaune tayi uban tagumi tana kuka”kallo d’aya yamata yad’auke kansa yana tunanin meyasa take yawan kuka.

Ahankali dr amina ta shigo office d’in tanata wani iyayi”(bazawarace kuma sonshi takeyi) had’e rigar sama data k’asa yayi yace”.ga patient nan kuje ki duba k’afarta”kicin kicin da fuska tayi tana wani jifar Aysha da wani irin mugun kallo”

Dr sadeeq na lura da ita”beyi dai mgn ba”tana wani tab’e baki da yatsina tace”.ke taso ki biyoni mana”kinyi wani zaune kinata kuka da wasu idanuwanki can.

Gsky masha Allah”idan bazaki iya dubani saiki barni”basai kinmun ba’a ba”ke kuma naki idanuwan k’ananu ne ko?”

Dr sadeeq beyi mamakin kalaman Aysha ba”sbd azuciyarsa yana kiranta da marar kunya da y’ar rashin kunya”kuma aganinsa dr amina ta zubda girmanta data tsokaneta.

dr wacece wannan k’aramar y’ar iskar?”tafad’a cikin b’acin rai tana kallon dr sadeeq”rushewa da kuka Aysha tayi tace”.kadai gani tana kirana da y’ar iska ko?”bayan nikuma ba ita bace?”be halatta ga musulmi yayi duba ga musulmi d’an uwansaba”dubar dazata cutar dashi”saidai idan fasik’ine!kamasa addu’ar shiriya…yawajjaba ga mutum yakiyaye harshensa daga alfasha”karya wulak’antar da musulmi d’an uwansa”karya ha’incesa”kar yazagesa,kar yabashi tsoro batare da hakk’in shari’a ba!

mena miki dazaki kirani da y’ar iska?”kasa mgn dr Amina tayi sbd rashin abin fad’a”yyinda dr sadeeq keta latsa laptop”azahiri kamar bemasan meye sukeyiba”amma ab’ad’ini mamakin Aysha yakeyi”domin kalamanta na nuni da tanada ilimin addini sosai….

malama kitaso muje nadubaki”bawai ki tsaya kina mana wani iyayiba”tana fad’in hakan ta juya ta fita”sbd tasan dai dr sadeeq ba kulata zaiyiba.

Dan Allah kasaka akira anty tazo da kanta takaini ni bazan iya taka k’afar ba”

banza yamata yana cigaba da abinda yakeyi”dama yagama duba patient”ka’idarsa 11 am yakeshan coffee” gashi time yawuce beshaba”

safa yasaka da hannu beyi mgn ba ya iso gabanta"fuska ad'aure yace".wace k'afarce ke ciwon?"

wannan ce”tafad’a tana nuna k’afar ta haggu”dg inane zuwa inane ke ciwon?”

Janye k’od’addi’yar doguwar rigar ta tayi”y’ar doguwar k’wabrinta fari tas yafito”ta aza hannayenta asama tace”.dg nan zuwa nan”

Hannu yasaka yafisgo k’afar da k’arfi”tasaki k’ara tana yarfe hannu”atake yafahimci targad’ene tayi”

Dallah kiyima mutane shiru targad’ene kikayi”naso ace karayace wlh”

Ikon Allah! gsky ka din….d’ago kansa yyi suka had’a ido”sunkuyar kanta ak’asa tayi tafasa mgn”

Idan ihun zakimun sai abarmiki kekika sani”to amma kaima da mugunta kakeyi ko?”

meye kikace?”dan Allah ka kamamun kawai.bece komaiba yana wani yatsina fuska yafara jan k’afar da k’arfi cike da mugunta.”tasaki ihu tana aza hannunta saman nashi”

d’ago kansa yyi yana jifarta da wani irin kallo”da sauri ta janye hannunta”

Hawaye nata zuba ta rufe idanuwanta hartaji yadena ja mata k’afar”tana bud’e idanuwanta ta ganshi zaune Inda yasaba zama”

Kallon k’afar tayi tana sakkota k’asa ta mik’e tsaye”Alhamdllh nasami sauk’i ta fad’a tana taka wa Ahankali ta juya ta fice”

Tana fitowa anty murja na isowa”wai kuka Kika sakeyi aysha?”fad’uwa fa nayi a toilet anty”

wlh mutumin nan in bacin uk’uba bbu abinda yake ganamun anty”nidai na fito sbd yunwa da k’ishi nakeji”

muje can kitchen nasiya miki abinda kikeso”amma yanaga kinata d’ingishi?”fad’uwa nayi a toilet”ashe targad’e nayi”

Subahanallahi!waye yafidda miki?”yoshimana “da yama saka wata dr Amina ta dubani”naga zatamun rashin mutunci…aysha bakyaji ko? nidai muje nasiya miki”dato ta amsa suka wuce kitchen”

k’at Aysha tayiwa cikinta”sannan ta amshi zainab “tadawo anan area d’in office nasa ta zauna tana hutawa”

Ta lura murtala nason yayi fira da ita”amma tak’i bashi fuska gaba d’aya”

Dr sadeeq kuwa ganin yarinyar tayi kusan awa bata shigo ba yasakashi hassala”

ga lokacin sallah yakusa”k’arfe 1:30 zai shiga theater”

yanason yasha coffee “amma tsabar miskilancinsa bazai iya had’awa da kansa ba ko kiranta ta had’a masa”

Tashi tsaye yyi yafito dg cikin office d’in”Aysha natayiwa zainab wasa suna dariya….ajikinta taji kallonta akeyi”

da sauri takalli k’ofar office nashi”yana tsaye yanata kallonta”suna had’a Ido yabanko mata wata uwar harara”

Laifin menayi kuma?”ka kama hararata akan me??

zaro ido dr sadeeq yayi yana cewa”mekikace?”murtala kuwa k’asa yyi da kansa yana tunanin meyasa yarinyar nan bata shakkar both?”

Idan kika bari nazo nasameki anan zaki sani”yana fad’in hakan ya bud’e k’ofar office nashi yashiga”

gaba d’aya yarinya k’arama naso tasakashi adamuwa”ga kunyatashi datake k’okarin yi agaban na k’asa dashi.

turo k’ofar akayi”azatonsa Aysha ce”yaji muryar hindatu”

yaya sadeeq”malama lafiya?”yafad’a yana d’ago kansa fuska ad’aure”kukan shagwab’a tasaka ta nufesa ta fad’a jikin sa”

waike bakida hankaline?ada kina gida idan kinmun haka nabarki”yanzun kinyi aure ma bazaki dena shagwab’a ba”

To yaya bakai bane kake fushi dani”dole nayi fushi dake baby”tunda kin zab’i soyayya akan kula da ammi”

bafa haka bane yaya ka fahimceni”nidai ki d’agamun jiki”yafad’a yana kallon k’ofar sbd jin motsin za’a shigo.

Kafin hindatu tabar jikinsa Aysha ta shigo office d’in “zainab na a hannunta”

zaro ido Aysha tayi tana kallon dr sadeeq da hindatu take ajikinsa….. innalillahi wa inna ilaihir raju’un!meye zangani haka???cewar Aysha baki bud’e….

wani irin✍️

Mom fareesa🖊️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button