Ni da Dr. Sadeeq

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 13&14

BOOK ONE 📖

Story & written by
Mommyn fareesa

wannan shafin na y’an team d’in honorable ne….lolx”😅😂

🅿️13&14

…….wani irin mugun had’e fuska yyi yana kallon Aysha da alamar tambaya?”hindatu kuwa bbu wata damuwa tace”.wacece wannan yaya?”she is my cleaner”okay dama nazone akan managar Abba(honorable lawal)gimtse fuska yayi ya saci kallon Aysha dake tsaye tanata kallon su”dukda ta fahimci cewa hindatu jininsa ce”ga kammanni da kuma kiransa yaya datayi”

aiki kikazo yimun ko raino kikazo kiyiwa wata??" Ah ah aiki nazo nayi"maza kije ki mayar musu da yarinya nabaki 10 minit"

Tab’e baki Aysha tayi batace komaiba ta juya ta fita”amma yaya kacika yimata tsau….. d’agamun jiki kifad’amun meke faruwa ba kimun zancen dabai shafekiba”

hindatu bata wani ji haushiba sbd tasaba da halin dr sadeeq”

Janye jikinta dg nasa tayi taja kujera ta zauna”tana kallonsa tace”.gsky yaya abinda mutumin nan keyi yayi yawa wlh”

Kaga jiya yatursasa ammi tamaka mgn katura mishi million 5″ka kuma tura”bayan mun tambayeta meye zaiyi?” dasu tak’i sanar mana”

To yanzun sabuwar motata(kud’in motar million 4 )naduba bata gidan nan”tun shekaran jiya dana dawo dg gidana”na ajiyeta bansake waiwaiyaba”sai yau zanje nayo cefane ,kawai nasamu bbu mota bbu alamarta”natambayi me gadi da securities sunce”. Abba suka gani da motar”namasa mgn yakama mun fad’a da k’ananun maganganu”wai nida kai bama k’aunarsa”shine zamuyi masa sharri ya d’auki mota…..bamuga rufin asirin daya mana ba”ya zauna da mahaifiyarmu bayan ta nakasa……

Amugun fusace dr sadeeq yabuga table d’in gabansa yamik’e tsaye yana huci”cikin fushi yace”.anzo Inda bazan iya jurewaba”dole yabawa ammi takardarta”besan yadda natsaneshi bane shiyasa”ko anfad’a masa muna son auren ne?

yafad’a yana d’aukar key d’in motarsa”tashi muje yana ina?”yana gidan fa yaya”kuma ammi tamun alama karna sanar maka fa”

hannunta dr sadeeq yafisga sukayi bakin k’ofar”hakan yyi daidai da karasowar Aysha”

Ke kije gida sai gobe”ajiyar zuciya tasaki”aranta tace”. aljarabatu sai akoma gida Ayi masifar da kyau”

rufe k’ofar yayi bebi takan murtala da Aysha ba”suka yi waje shida hindatu.

Tafiyar minti 15 ta iso dasu anguwar su”bayan yyi parking a bakin get suka fito”

ammi na kwance kan 3 seeter amain parlour” anjingina mata jikinta da pillow tana kallon me shigowa”

Kallo tabi y’ay’an nata dashi…atake ta fahimci hindatu taje tasanar masa meke faruwa akan motarta.

Honorable lawal na zaune a dining area” yanata cin abinci da uban nama asaman abincin….

sosai gabansa yadinga bugawa”sbd yana mugun shakkar dr sadeeq”yasan kuma tabbas hindatu tasanar masa abinda yafaru”

 saurin d'auke kansa yayi sbd ganin dr sadeeq na nufosa"

Mlm inaso yanzun basai anjima ba karubutawa mahaifiyata sakinta 3 kabata”tunda kanada bakin mana gorin ka rufa mana asiri ka zauna da ita tana nakashashshiya!sannan dole ka fito mun da motar hindatu” kokuwa nayi mugun baka mamaki…. yafad’a yana dg tsaye fuskarsa bbu rahama”

sadeeq ni kake gayama mgn haka??karka manta matsayin uba nake gareka”

Tab’e baki dr sadeeq yayi yace”.mahaifina yamutu”kai ba mahaifina bane”aurenka da ammina ka d’aukesa amatsayin k’addara”amma matuk’ar ina numfashi adoran duniya saina rabaka da ammi na”idan kuwa hakan be faruba to bancika ABUBAKAR SADEEQ ba! yafad’a yana huci”

yanzun sbd baku k'aunata shine zakumin sharrin nasace motar hindatu?"

Tarin da ammi keyi yasaka dr sadeeq juyawa da sauri”yahango tana k’okarin fad’owa dg kan kujera,hindatu na rik’e da ita tana kuka”

Atake yaji damuwarsa tayi yawa”bebi takan honorable lawal ba yanufi gun ammin”

Ruwan dake kan center table ya d’auka yana d’ago kanta zai bata….amma tak’i yarda”dafe kansa yyi”domin hakan na nufin amminsa na fushi dashi”kuma yasan fushin nata kan mijinta ne”wato honorable lawal..

Hindatu ta amshi ruwan ta bata tana share hawayenta”itama k’in amsa tayi”yah salam!ammi dan Allah kiyi hak’uri”kada damuwa tamana yawa” dr sadeeq yafad’a yana k’ok’arin aza kansa asaman cinyarta”yakama hannun ta guda ya aza saman kansa”dan Allah ammi kidena fushi damu”kullum daddy namiki nasihar ko bayan ransa ki kula damu….meyasa sbd wannan mutumin zakiyi fushi damu”bakisan waye shiba?bakisan halinsaba?haba ammi!nine fa sadeeq da autanki hindatu”yanzun kin rik’e nasihar daddy kenan?

Ajiyar zuciya ammi tasaki tana bud’e idanuwanta”ya d’ago kansa yakalleta”da ido tamasa alamar yadena yiwa honorable haka “ammi motar baby fa tana gunsa”rufe idanuwanta tayi”shikenan nadena ki bud’e idon to”

babu musu ta bud’e idanuwanta”yaya jikin naki ammi?”da ina da ina ke miki ciwo??juya idanuwanta tayi alamar bbu ko ina”tanata kallon su shida hindatu”tanajin kamar zatayi mgn saidai bata iya mgn balle motsi ,sai yadda akayi da ita”kuma normal takejinta batajin ciwon komai ajikinta….

Yaya time d’in sallah fa yayi”kaje kayi sallah kadawo kayi lunch pls”

Korata kikeyi baby?”ah ah yayana”nasan baka wasa da sallah”kaine ka koyamun yinta atime”

Kama dawo pls muyi zancen farida dan Allah”harara yagallah mata”ban hanaki yimun zancentaba?”da ciwon ammin zanji koda wani zance?”kayi hak’uri dan Allah”

Ammi dai nata kallonsu aranta tana addu’ar Allah yakawo mata sauk’i”ta tashi taga time d’in da sadeeq zaiso wata mace haryayi aure.

K’arar rufe k’ofar da honorable lawal yayi yafita”yasaka dr sadeeq kallon k’ofar”

ammi kinada alwalah?”da ido tace”. Eh”bara nakaita saitin alkiblah tayi sallar a bed room d’in ta”yana fad’in hakan yad’auki ammin ,hindatu tabishi abaya”

bayan yakaita ciki yafito ya wuce sashensa”cire takalminsa sawu ciki yyi da suit na jikinsa ya wuce toilet.

bayan yagama alwalah yafito yasaka jallabiya milk yafito zuwa masjeed”

A compound d’in gidan yahango honorable na waya”d’auke kansa dr sadeeq yayi yanufi bakin k’ofar get d’in”yana wani irin girgiza kansa”sbd shiyasan tarkon daya azawa honorable lawal….


washe gari tun k'arfe 6:am Aysha ta gama shirinta"cikin yunifoam na cleaners da anty murja ta amso mata "

tana fitowa tsakar gidan baffa na shigowa gidan”sosai Aysha ke mamakin meyasa beson kwana gida yanzun?”

Ina kwana baffa?”ke ina zakije da yunifoam ko makaranta zakijene?”

Ah ah gun aiki zanje”wane aikin kenan?bayan rainon dakikeyi ana biyanki wata shegiyar dubu 10 “wani aikin kuma kika canza??

goge goge ne nakeyi yanzun ai”nawane kud’in watan?”dubu 25 ne(tak’i fadar 30k ne sbd idan anbayar duka zai amshe)

Tab’e baki yayi yace”.garadai wannan d’in na dubu 25 d’in”amma akwai lokaci kad’an da dole ki barsa” kidinga yin abinda zaki taran dukiya”adinga baki dubu dari biyu ko dari biyar arana d’aya bama wataba…

gaba d’aya Aysha bata gane Inda zancensa yadosaba”tasaka takalmin ta ta fice” sbd tasan halin wannan mugun idan ta makara zai azabaceta.

gashi bbu kud’in transport”gudun kada tayi latti kawai ta tsayar da adaidaita ta hau” da nufin idan sunje asibitin dr sadeeq yabiyashi kud’in sa….lolx🤣

Suna isowa asibitin✍️

Mom fareesa🖊️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button