UNCLE DATTI Page 41 to 50

Girgiza mata kai Inna tayi alamar kar tayi kuka amma ina kuka ya kwace mata ta shige jikin Inna tana sheshek’ar kuka”. Ummana Inna, ina so na ganta na san a duk inda take hankalin ta a matuk’ar tashe yake, idan zanyi fushi da kowa bazan iya yi da ita ba”.
Bayan ta Inna ta hau bugawa cikin hikima tana zancen zuci, ita kanta zata so ace an sada yarinyar nan da mahaifan ta amma ganin yanda Ammjntacce ya fice da kuma yanayin Nana ya tabbatar mata da cewa bai ammince da bukatar Nanar ba”.
“Kiyi hakuri kici gaba da zama damu Nana Allah shi yasan nufin hakan, idan da rabo wata rana zaki koma ga iyayen ki”.
Sai da ta ci kuka son ranta kafin ta share hawaye ta dubi inna cikin kuncin zuciya tace” Don Allah a wani gari nake yanzu? “Hmmm Nana ba hurumi na bane na fad’a miki garin da kike, ni dai aikina a nan na baki dukkan kulawan da kike bukata”.
Zata kuma yin wata tambayar Inna ta ja hannun ta da sauri muje ki kwanta dare ya fara nisa”, ba dan ranta ya so ba tabi bayan ta suka shige d’akin ta.
Makeken gadon ta ta hau ta kwanta Inna ta d’auko bargo ta rufa ta dashi kasancewar hunturu ne ana sanyi sosai yasa tayi hakan cuz bata son sanyi ya cutar da lafiyan ta”, ta koma ta zaune a gefen gadon tana mata hira can kuma barci ya fara d’aukan ta tana gyangyad’i
Sai tausayin ta ya kama Nana ta san cewa duk dan tsaron lafiyar ta take yi, cikin hikima ta lumshe idanuwan kamar mai barci komai ne yasa ta hakan ba sai dai dan ta ba ma Inna damar da zata je ta kwanta tayi barci, bayan haka itama kanta Nanar tana bukatar kad’aici”.
Inna dai na nan a haka idan ta gyangyad’a sai ta bud’e ido, da dai taga alamar barci ya d’auke Nanar tayi mata addu’ar barci ta fita tare da rufa mata k’ofa, ta nufi d’akin ta ta kwanta ta hau sharara barci abin ta.
B’angaren Nana tana ganin Inna ta bar d’akin ta mik’e a hankali ta zira k’afarta ta a k’asa ta taso a hankali tana takawa taje jikin tagar d’akin tana lek’awa, dan k’arfin hali duk da tana jin sanyi na ratsa ta, jikin ta na rawar sanyi kattt katttt katttt bata yi yunk’urin kare kanta ba ko tsoron dare bata ji ba balle taji darrrrr a ziciyan ta ta fara tunanin kar tayi gamo……ance tsananin bakin ciki na cire tsoro idan mutum yaji tsoro to bai had’u da bakin ciki bane tabass hakan ya faru ga Nana a wannan lokacin.”
Hawaye ne masu uban dumi suka hau zubowa ta kasa tsaida su zuciyan ta falllll cike take da tunanin……..tayi dana sani mai tarin yawa na ba ma Datti kanta da tayi, duk da dai ta san cewa a lokacin bata da wata cikakkiyar wayo amma duk da hakan sai da taji haushi da zafin kanta na sakin jiki da tayi da tayi da shi sosai, ta bashi damar da zai sarrafa ta ya driving d’inta to his test”.
Tsiraren hawaye suka sake yankoma mata da ta tuna da Auntyn ta Aina, wata k’ila alhakin ta cin amanar da tayi mata ne yake binta gashi nan an killace ta a gida da bata san ko na wanene ba bata da damar fita”. Kaiiiiii ba zai yihu ba ko ta halin yaya sai ta nemo hanyar guduwa baza ta ci gaba da zama a gidan shi ba cuz bata san wani irin buri yake so ya cimma akanta ba”.
Wannan dare ko runtsawa Nana bata yi ba banda aikin kuka babu abunda take yi har sai da taji kanta ya fara yi mata ciwo kafin nan ta hak’ura ta koma ta kwanta.
Da safe bayan ta idar da sallah ta nufi d’akin Inna har kasa ta tsuguna ta gaishe ta ta amsa mata”.
Tana lura da yanda fuskar Nanar yayi luhu-luhu alamar taci kuka sosai daren jira, Inna ta d’an had’e rai tace wato baza ki hakura ki saka wa kan ki salama ba? Yanzu haka kike so ki ta zama kina kuka? Gaskiya idan kina haka baza mu shirya ba tsammm banji dad’in haka ba sai ki saka na fara zargin cewa da wani abu da nake miki wanda bakya so amma kin kasa fad’a”.
“Ganin yanda ranta ya fara baci ta hau fad’a sai ta hau bata hak’uri tare da yi mata alkawarin baza ta sake yin kukan ba”.
B’angaren Datti iya wuya hankali ya gama tashi sai baza ido suke yi a kafafen yad’a labarai amma shiru, Fu’ad ma yayi iya nashi kokarin na bada guduma dan nemo inda sahibar shi take abu amma abu yaci tura, tsakanin shi da d’an uwan shi babu wani kyakkyar alaka da ace baiyi halin b’eran ci ba da babu abunda zai saka su cikin wannan halin”. Kuka iya kuka yake yi a duk sanda tunanin ta ya fad’o mishi a rai sai yaji duk duniya babu wanda ya tsana kamar Datti.
Su Umma da Abba duk sun juya mishi baya, Alhaji ma ya fita harkan shi anyi anyi ya fad’a laifin da ya aikata amma ya ki hakan ya dad’a hasala su”. A b’angaren k’anwar shi ce kadai da Ummi da kuma baba karami yake samun sauki amma duk da halin da yake ciki kowa yayi banza dashi, ai ba yaro bane da har za’a ta tambayar shi yana raina wa mutane wayo”.
Idan ya shigo d’akin tsohuwa cewa yake su neman mishi Nana idan ba haka ba shima guduwa zaiyi ya shiga duniya, ko tausayi baya bata tayi mishi tatasss da zagi”shi yayi sanadiyar gudun shi zai nemo ta ai shi ya san sirrin da ke b’oye wanda ya kasa bayyana wa”.
Itama Aina bata ragar mishi ko kad’an babu kalar habaice-habaicen da bata yi mishi ta mata da cewa a baya dear d’inta ne wanda ta d’auki dukkan yardar ta ta d’ora mishi”.
Duk da irin mugun haushin shi da take ji ko da wasa bata fad’a wa su baba Babba cewa kashe Nana yayi ba…….., ta zuba mishi ido ne har zuwa tsawon lokacin da zai d’auka da kanshi ya fallasa komai.
Wata ranar Alhamis da rana da misalin karfe d’aya Fu’ad ne ya shigo d’akin tsohuwa za shi wajen Aina kasancewar tunda ta koma gidan a b’angaren tsohuwa take zama. Tarar da ita yayi akan kujera ta d’aga ido tana kallon ceiling hankalin ta baya jikin ta bata san ma ya shigo ba har ya nemi wuri ya zauna. Jin motsin mutum a kusa da ita ya sa ta saurin d’agowa ta dube shi tana had’a ido da shi hawayen da take kokarin mak’alewa suka samu daman gangarowa saman cute face d’inta”.
“Yanzu shikenan Fu’ad Nana ta barmu kenan har abada? Ba mu ba sake had’a ido da ita? Shikenan ya kashe mana Nanar mu? Maganar ta dake shi sosai a zuciya sai ji yayi shima hawaye ya hau zubo mishi, a yanda take maganar duk ta karye mishi zuciya”.
Cikin dishashiyar murya yace” Kin ga gawar ta ne? Ko kinji labarin wanda ya samo gawar ta? Tayi saurin girgiza mishi kai”.
“Me yasa kike zargin cewa ta mutu bayan ba ki da wata cikakkiyar shaida akan haka”.
” Share hawayen ta tayi ta ta d’au hanky a gefen kujerar ta fece majina murya na breaking tace” Baka…..ga…. ab……n da na…..ga..ni ba Fu’a….d, da ido……na naga jiki a Jikin Datti, ya shigo shi kad’ai bacin tare suka fita, wan……nan hujjar kad’ai ya tab…….batar min cewa mutu…….wa tayi ku…..ma shi ya kashe ta……..
Shiru yayi shi kad’ai tare da hard’e hannayen shi yana nazartar kalaman ta har ta gama………Tabbass akwai k’amshin gaskiya a maganar Aunty Aina dole d’an uwan shi na da hannu akan b’atan Nana………, dole ne ya zurfafa bincike ya gano gaskiya idan har Datti yana da hannu akan b’atan Nana sai yayi sanadiyar yankewar jin dad’in rayuwar shi”.