UBAYD MALEEK Page 21 to 30

A kasale ta miqe tayi ciki tana duba qaton agogon dake bangon palon ta shige palon ciki ta doshi hanyar bedroom dinsu tashige.
Saidayi sallah kafin tayi wanka ta Sanya doguwar riga Mara nauyi black me dogon hannun Kuma har qasa take komaima Bata sanyo akantaba ta fito ta nufi dakin farhat tana Kiran sunanta.
Zaune take tana homework NURUn ta shigo taqaraso kusa da ita ta zauna farhat din ta haye cinyarta tana cewa”
My Lewa dubamin kigani yayi daidai kuwa?
Murmushi NURU tayi tana karba tafara dubawa tana cewa”
Ni danasan farhat Dina nada kokari Babu homework da bazata iyayi daidai ba Amma dai yanzu kinajiye muje kici abinci tukuna daga baya a qarasa lokacin cin abinci yayi.
Kwantawa tayi jikin NURUn tana cewa”
Ni yau banason cin abinci cupcakes and pancakes nakeso cin zakimin ai ko my Lewa?
Kumatunta taja tana sake gyara Mata kwanciya ajikinta cikin tsananin qaunar farhat din tace”
Yes of course sweetie duk abinda kikeso shi zakici.
Ahankali ta sake lafewa jikin NURUn tana cewa”
I love you my Aunt NURU.
I love you too baby.
Tashi sukai NURU na cewa”
Muje cikin yanzu bada dadewaba chief NURU zatayiwa princess pan and cup cakes dinta duka.
Kicin suka nufa cikin murna farhat ke taya NURU aikin da surutu sbd Babu kowa yanxu acikin gidan Dan dama da angama abincin yamma tun 7 na yamma kowanne me aiki na gidan ke barin shashen sukoma sashen masu aiki musamman idan MALEEK na Nan to ita yau batamasan MALEEK din yadawoba Yana gidan.
Saidata gama hada cake din tasaka a oven tafara gasa pancakes din lokacin tuni tacewa farhat taje dining ta zauna gatanan kawowa yanzu.
Cikin farin ciki takeyin aikin daga can cikin kicin din ta Dan dago muryarta me sanyin dadin sauraro tace”
Sweetie kinajin qamshin cake din Nan kuwa daga Nan inda kike sbd I just added your favorite inib yanzu akai inason kina fara cinsa kunnuwanki suyita tsalle Suna gudu sbd Dadi.
Dariya farhat tasaki tana toshe Baki idanuwanta akan fuskan dad dinta daya Dade da samunta a dining din Dan lokacin dinner dinsa yayi.
Ahankali ya dan kallin hanyar qofan dazaikaika kitchen din saikuma ya dauke Kai tareda saka spoon akan lafiyayyan abincin dake gabansa Wanda yanzu Fana tagama serving dinsa ta fice daga sashen gabaki daya.
Kasa kasa da murya farhat tace”
Daddy ai zakaci pancakes dina sbd cakes din aunt NURU are the best
Idan kaci wannan kullum zakaso ka qara kaji Kuma tasaka inib oh oh daddy na matsu akawo.
Dan kallon farhat din yayi da fararen idanuwansa Yana iya ganin farin ciki me tarin yawa da nutsuwar rayuwa gashinan bayyane ko Ina atareda farhat din Wanda hakan yasa yaji wata nutsuwa tashigesa tabbas yaransa deserve the best life,
Yaran MALEEK guda na delah gizah sun cancanci kowane irin farin ciki na duniya dai sbd sune keda matsayinda kusan yafi na kowa a gizah sbd mahaifinsu shine asalin maleek na kujerar sarautar delah gizah Amma rashin dacen uwa Kamar Laila yabarsu da qarewa tamkar marayu gashi shikuma schedules dinsa na rayuwa sun hanashi lokacin zama tareda yaransa.
Amma koma dai menene tunda sunsamu kulawa daga wannan din hakan yamasa Dan kuwa yaransa na cikin walwala da farin ciki Kamar Basu taba shiga damuwan kewan iyayeba musamman AFIA tasamu ‘yar uwar dataketa yiwa kanta mafarki da fatan asamu hakama farhat tasamu dukkanin soyayya da kulawan datafi buqata daga iyaye sbd qarancin shekarunta.
Dauke da kyakkyawan tray ta fito kitchen din ta nufo dining room tana
Cewa”
Sweetie are you ready??
Yessss “”farhat tafada da Dan qarfi cikin Jin Dadi da qaguwa.
Ok baby I’m coming ki tabbatarda yau kin rufe qofa da windows dinda kunnuwanki zasu gudu Dan kuwa yau hmmm.
Tana shigowa cikin dining room din tace”
Tadaaa…..cak ta dauke wuta ganin dadynsu farhat din a zaune da ‘dan guntun mamakinsu akan fuskanshi sbd su biyun kawai sun cika gidan da hayaniyar datafi ta mutum goma..
Rawa qafafunta suka dauka sbd tsananin tsoro da firgicin data shiga saura kadan tasaki tray din farhat ta karba da sauri tana cewa”
Zaki zubar muyi wahalan banza fa.
Batama San me farhat ke cewa ba gabaki daya ta rude ta tsorota batasan abinyi ba sai kawai ta durqusa cikin rawar murya tace”
Barka da dawowa da fitowa.
Tsit gurin yayi sbd kallo daya yayi Mata ya dauke Kai sbd kayan dake jikinta da kanta dake budeĀ
Itakuma tunda yau ta ritsu Babu damar wucewa batareda izininsa ba Dan hakan ta sauke Kai durqushe agurin.
Farhat ce ganin shiru shiru dad din nacin abincinsa hankali kwance yasata sauka kan dining din tazo gaban NURU ta kamo hannunta tana janta tashi tace”
Lewa Daddy ya amsa gaisuwanki kitaso muci cakes din kibani abaki na matsu nafara ci.
Dan zare hannunta tayi daga na farhat din tana sake saukar da Kai qasa Dan bada tsananin girmamawa ga zaman maleek dake gurin.
Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa cikin nutsuwa da kamewarsa ya bar gurin sbd yagama cin abincin dakuma hayaniyar dazata iya basa ciwon Kai tasu.
Yana barin gurin ta zube zaune gabaki daya tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi tana dagowa ahankali ta dan saci kallon bayansa ta sauke Kai da sauri tana dawo da kallonta kan fuskar farhat dake Jan hannunta,
Kyakkyawan hancin farhat ta zubawa ido Wanda yake tsaf tsaf na dadynta ne ta debo ta gangara da idonta kan idanuwan farhat din take kirjinta ya buga da qarfi ta dauke idonta akai tana miqewa Kamar wadda kwai yafashewa aciki.
Kasa zama tayi sbd sanyin qamshin turaren dadyn daya cika gurin Kamar har lokacin kaman Yana gurin Dan haka saitakejin bazatama iya sakewaba Dan Jin take kaman Yana Nan Dan haka a tsaye tabawa farhat din abaki harta qoshi itama biyu kawai taci suka tattare gurin suka nufi daki sukai brush tareda wanka sukai sallar Isha sukai Shirin bacci suka koma dakin farhat din acan suka kwana.
Washe gari datasan Yana Nan batai gigin ko kallon hanyar dining room ba sbd dama acan ne kawai ake haduwa dashi acikin gidan Dan koyaushe Yana samansa Dan ko acan saman Palo biyune dashi kafin akai Master bedroom dinsa.
A kicin tayi breakfast bayan antafi Kai farhat school Dan haka itama tana gamawa driver ya wuce da ita.
Kwana biyu tana kame Bata wani fitowa sai yaunema da farhat ta tashi da zazzabin sanyi me qarfi na asthman datake dashi Wanda kaman agurin dadynta ta dauka Dan shima yanada asthma Amma ba’a taba ganewa sbd kiyayewa.
Kayan sanyi masu kauri ta Sanya Mata da socks da wulan sanyi tareda dumama dakin yadauki dumi takawo Mata tea me zafi tabata ahankali hartashanye tana gama Sha ta koma kicin ta maida kayan tadawo kenan tun daga bakin qofa take jiyo kukan farhat din da sauri taqaraso cikin rufewa ganin amai farhat din keyi sosai take hankalinta yatashi ta dauketa tayi toilet da ita yarinyar tafara galabaita sosai Dan kuwa ko zama Bata iyayi da kanta sbd galabaita.
Wanka tayi Mata tasake Sanya Mata wasu kayan masu nauyi bayan ta shafe Mata jiki da mai me Dan zafi ta sake gyare dakin tsaf ta sauya bedsheet da duvet ta kunna turaren daki dake fita ahankali ahankali Yana gauraye dakin da qamshi sai dakin yayi Dadi sbd ga dumi ga qamshi me Dadi.