UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 31 to 40

Kallonta AFIA takeyi tana kore duk wani tunanin abinda tagani ta juyarda zancen da cewa”Kije kicire kayan kada sanyi yakamaki tunda juice din nada sanyi ga ac Kuma a bayanki Yana aiki.

Kasa wucewa tayi ta matso kadan tana kallon fuskan AFIA din a Dan daburce tace”

Afia Farhat ta turani da jug na juice a hannuna duka abinda yafaru ma mistake ne sbd Ni bansanma meya meya……

Cikin sauri AFIA ta katsetada cewa”

Relax relax ok,kije kicire kayan ki gyara jikinki wannan abin da kike magana is nothing sbd dad tamkar mahaifinki ne so there’s no way dama wani tunanin zaishigo kanmu mu duka ki manta komai daga Nan gurin ok??

Jin hakan yasa jikinta Kara sanyi ta juya ta wuce daki,

 tana shiga toilet ta nufa acan ta tube tayi wanka ta zuba kayan a washing machine ta fito daure da towel light blue.

Riga da wando na bacci ta Sanya masu kauri tareda hula ash tayi sallar ishai ta kwanta sbd duk Jin ranta take ba Dadi.

Tana kwantawa farhat ta shigo dakin sanye da kayan bacci irin nata ta qaraso gefenta ta kwanta ahankali jikinta tana cewa”

Sorry my Lewa.

Tana Jin farhat din sbd batai bacci ba sai ta gyara musu kwanciya tareda ja musu bargo sukai bacci.

AFIA ma Bata Dade a Palo ba tashigo tayi Shirin kwanciya ta hau gadon ta kwanta tana kallon farhat datake bacci cikin nutsuwa tamkar jaririn dake bacci cikin dumin mahaifiyarsa

Farhat tana yiwa NURU wani irin so da kauna na shaquwar jini Wanda kwata kwata babushi atsakaninta da mum dinsu.

Maida kallonta tayi kan kyakkyawar fuskar NURU dake bacci kamar baby 

Takai hannu ta gyara Mata hular kanta cikin kulawa da kaunar NURUn cikin ranta tana cewa”

Sorry NURU,

Kauna da soyayyar mahaifiyata yaso shiga tunanina,

Naji tsoro matuqa a dazun sbd Babu wani gurbi dazan iya gani na mahaifiyata wani ya cikesa dan haryanzu ban cirewa alaqarta da dad Rai ba kiyi hkr NURU bansan meya shiga kainaba har nabari hakan yaso bani tsoro bayan dad is like a father to you Inshallah bazan taba Bari hakan tasake faruwa duk aikin shedan ne.

Lumshe idanuwanta tayi take bacci ya dauketa tana sakejin kaunar NURU.

Washe gari lafiya kalau suka tashi abinsu cikin kulawa da juna Kamar yanda suke,

Ita tayi breakfast Kuma dukkanin abinda tasan dad din naci shitayi aka jere a dining takoma cikin acan tayi nata breakfast din Takoma daki tayi wanka bayan tafara gama Shirin Farhat itama ta shirya tsaf cikin black palazzo trauser da white ladys long sleeve sai black wedges shoes ta fito daukeda handbag dinta tareda afia da itama take a shirye tsaf suka fito driver na jiransu suka shiga suka wuce.

Tunda suka Isa school takejin hankalinta ba’a kwance ba fargaba da tsoron abinda zai iya faruwa takeji idan har Imran yayiwa MALEEK maganar neman aurenta Wanda takega idan hakan tafaru ta take doka me qarfi tareda tsaurin ido da kawo reni.

Dafe kanta tayi tanajin kanta kaman ze buga ta fiddo wayar daga cikin jaka bayan ta fito daga first class dinta ta saka Kiran Imran din.

Cikin kulawa ya dauka da sanyayyar muryarsa me Dadi yace”

Hello baby how are you doing?

Kasa maganar tayi sbd batasan me zatace Masa ba Kai tsaye sbd Babu ta yanda zata iya fada Masa ita negestati ce ta waya.

Hello sweetie are you there??

Dawowa tayi hankalinta daga Nisan datayi a tunani ta gyara murya cikin sanyi tace”

Dama inason ganinkane we need to talk akan maganan jiya.

Gyara zama yayi daga inda yake Yana cewa”

Akwai matsala ne?

No Inason muyi maganar ne dakyau kafin akaita gaba.

Shiru yayi na tsawon mintuna kafin yace”

Ok karki damu koma menene Ina Nan  zanyi handling komai yatafi smoothly 

Idan kingama ki kirani I will come and pick you up.

Gyada Kai tayi kaman Yana ganinta tareda kashe wayar ta maida jaka ta miqe daga coffee shop din datake zaune takoma.

Sai yamma sosai suka fito kusan lokaci daya da Afia Dan haka Dole tare zasu tafi gidan Dan haka suka bi motar Imran sukace driver yakoma kawai.

Ganin afia na taredasu yasa tafasa Masa magana sai kawai suketa fira su dukansu musamman akan karatunsu da yanzu suka fara nisa sai ‘yar soyayyarsu dasuke jefi jefi ta hanyar kallon juna da kalmomin kulawa Wanda duk yake qara burge afia take ganin ba qaramin dacewa sukai da junaba.

Koda suka iso gida dukkaninsu tare suka fito afia na gaba suna bayanta Imran na Mata magana ahankali Yana kallonta kaman ze hadiyeta da so da kulawa.

Ita Kuma dayake duk a Sanyaye take sai yake ganin kaman yangace take Masa duk yasake sukurkurcewa Wanda ba hakan bane agurinta.

Suna shigowa palon farko itace agaba sbd afia tuni ta shige shikuma Yana gefenta cikin dibbin mamakinta da tsoronta MALEEK suka gani zaune a palon abinda bayayi hannunsa riqeda waya yanayi cikin turanci da yarensa na Amharic Wanda yasa su duka fahimtar da gida yake waya dama mahaifiyarsa sbd Jin yafada sunanta cikin yare.

Dukkaninsu sunsan ko zasu rube agurin bazai dago ya kallesuba musamman ma ita da tana shigowa fararen idanuwansa masu girma acikin nata suka fara sauka tayi saurin sauke Kai zuciyarta na harbawa 

Bata tsaya wata wataba ta wuce ciki sum sum tabar Imran a gurin Wanda shikuma ya gyara zaman jiran MALEEK sbd gabatarda kansa amatsayin me neman auren NURU da neman izinin turowa a nema Masa aurenta.

 Zaman jiran MALEEK ya dasa tsawon lokaci me tsayi Wanda harya fara sarewa sbd ganin kaman lokacin basa ne MALEEK din bayada Amma bazai sareba haka yayita jira har maleek din yagama.

Barka da dare MALEEK.

Kallo daya MALEEK yayi Masa ya maida kansa kan wayarsa dake sake daukan ringing ya gyada Masa Kai alamar amsawa.

Gyara zama da gyaran murya duk yayi lokaci daya Imran din Yana saka nutsuwa a muryarsa yace”

MALEEK Ina neman izini ne na shigowa neman auren NURU idan an…

Dakatawa yayi daga zancen Yana gyara zamansa sbd ganin kaman MALEEK din baiji abinda yafara fada ba.

Sake bude Baki yayi zaiyi magana MALEEK ya dago ya kallesa da kyau a karon farko da yayi Masa kallon tsaf 

Ya bude bakinsa cikin dakakkiyar muryarsa me izza da kamewa yace”

Nayi waya da santiano albeiriteo gobe zasu sauka France jibi zamuyi board meeting na signing contract dinsu 

Get yourself ready Kaine zaka kula da contract din har gamawansa.

Yana fadar hakan ya miqe yabar palon Imran yabisa da kallo da idanuwansa dasukai kaman zasu ciko da hawaye,

Shin MALEEK be jisa bane kokuwa zancen ne bai fahimta ba?

Shafa Dan zufan tashin hankalin da fargaban daya tsatsafo Masa yayi duk sanyin AC daya gama gauraya babban Palon Yana girgiza Kai cikin cire negative thoughts yace”

Baiji Mena fadaba gobe zanzo after breakfast nayi Masa bayani daidai.

Miqewa yayi ya fice Yana maida hankalinsa Kuma gurin contract din santiano albeiriteo da MALEEK din ya basa shugabancin handling Wanda bazai taba samun lokacin kansaba tsawon lokaci sbd contact din nada tarin ayyukanda bazasu barka ko lokacin samun nutsuwan bacci me Dadi kayi.,

Tabbas zaizo gobe yakai qarshen maganarsa da NURU agurin maleek kafin aikin yasa yarasa lokaci duk da hakan zai Kira dad dinsa akan maganar.

##MAMUH#

*Assalamu alaikum warahmatullah,  shin kinaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what’s app kokuma ya ziyarci shafinmu  a instagram *@turare_by_awwaba mungode*

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button