ALKALI NE Page 11 to 20

Mota suka shiga Alhaji yace amma dai ka duba masu aiki yau saboda ance kaya zasu zo. Adebayo yace munyi magana dasu kila cikin dare kayan zasu zo. Alhaji yace da kyau. Shiru sukayi har suka isa ya ajeshi yayi masa sallama.
Sai wajen k’arfe shad’aya Mr. Kallah ya bar Alhaji Mai Wada domin yasan zuwa lokacin bazai iya komawa wajen aiki ba dole ya nufi gida, duk da yawancin firar labarin yanda tsarin aikin yake yake ta fad’a masa, tun Alhaji yana ganewa har ya gaji, sosai yake jin bacci.
Direba Mr. Kallah yasa ya mik’a Alhaji gida, beyi musu ba domin shima baya buk’atar hawan motar haya. Kai tsaye gida yawuce, godiya yayi ma direba hada kud’i ya bashi kafin ya shige ciki.
**** ****
Washe gari da safe Malan Sani ya iso, alokacin har Alhaji ya shirya dan ya k’osa yaje yaga abinda ya faru. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jego. Malan Sani yace lafiya lau ya gajiyar aiki? Alhaji yace akwai ta fa.
Kud’i ya bama Madu kafin sukayi masa sallama suka tafi. Lokacin da suka isa Alhaji yace ya tafi da motar idan ya gama zai kirashi. Malan Sani yace Alhaji da ka barni na zauna anan ai. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in nima zanso zamanka anan, amma saboda hidimar da take gaban ka gara ka tafi, idan akayi suna sai ka fara zama a wajen aiki.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in nagode. Kayansa ya d’auka ya bishi abaya zuwa ofis. Bayan sun gaisa da Malan Bala Alhaji ya gabatar da Malan Sani a wajenshi. Malan Bala yace gaskiya nayi farin ciki da zuwan ka, ya masu jego? Malan Sani yace lafiya lau suke ya aiki? Malan Bala yace gashinan munayi. Malan Sani yace Allah ya taimaka ni zan wuce. Alhaji yace shikenan sai kaji ni.
Bayan da ma’aikata suka gama shigowa suka gaisa da Alhaji sai ga *Peter* wanda shine shugaban masu kula da kayan da ake saukewa. Bayan sun gaisa ya mik’a ma Alhaji takarda yana fad’in jiya wajen k’arfe 2:00 kayan Alhaji Marusa suka iso, na duba abinda ya samu sai muka sallame su kafin kazo ka gama dubawa.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in bara na kammala aiki sai nazo na duba. Risnawa yayi ya juya ya fita. Shiru Alhaji yayi yana nazarin yanda zai b’ulloma Alhaji Marusa idan har ya kamashi da laifi acikin kayansa, domin yasan babban mutum ne, karo dashi bazaiyi kyau ba, amma dole ya tsaya domin ya tabbatar da gaskiya.
Bayan daya gama komai yasa aka kira masa Adebayo, bayan ya iso suka fita tare da wasu ma’aikatan. Tunda suka isa Alhaji yasan an tab’a kayan, haka yasa aka fara bincika kayan, sai dai abun mamaki babu komai na laifi aciki. Adebayo yace ai na fad’a maka Alhaji Marusa baya shigo da kaya masara kyau.
Murmushi Alhaji yayi yana fad’in bazan tabbatar ba sai na gama bincike. Adenayo yace bincike kuma? Na d’auka za agama komai abasu kayan su ai. Alhaji yace ka sani ko akwai haramtattun kaya aciki kafin muzo aka cire? Da sauri ya kalli Alhaji yana had’iyar miyau.
Dafashi Alhaji yayi yana fad’in wasa nake maka, bayan yanzu muka gama dubawa kuma babu komai, amma dai zan sake bincike idan na tabbatar da komai lafiya sai abasu kayansu bayan sun gama biyan komai kamar yanda doka ta tanadar. Adebayo yace ai Alhaji Marusa baya kin biyan kud’in kaya, domin yasan yanda dokar take. Alhaji yace haka akeso ai.
Cikin dabara Alhaji ya ciro abinda yasa kafin ya nufi ofis, mukulli yasa ya kulle ya fad’ama Malan Bala duk wanda yazo yajirashi zai shiga band’aki ne. Malan Bala yace angama Alhaji.
Zaune yayi yana kallon abun mamaki, faskar Adebayo ya gani shida wasu ma’aikata hada Peter da yaran Alhaji Marusa suna ta aikin jidar wasu kwalaye wanda besan meye aciki ba.
Lokaci ya duba yaga k’arfe 3:30 na dare. Mamaki yayi ganin duk saboda su cire wad’an nan kaya ne suke tsaye a cikin dare. Gaskiya duniya ba gaskiya.
Bayan ya gama gani ya kashe dan ya baro (flash) d’insa agida bare ya tura aciki, dirowa ya jawo ya saka kemarar acikin jakarta kafin ya tashi tafiya. Tashi yayi ya bud’e k’ofar yana tambayar Malan Bala ko akwai wad’an da suka zo nemansa? Malan Bala yace Oga Adebayo yazo shida Umar.
Alhaji yace kaje ka kirasu. Bayan sunzo Adebayo yace dama Alhaji Marusa ne yakira waya idan angama duba kayan yana buk’atar su. Alhaji yace bana tunanin bada kayan nan yanzu domin bangama yarda dasu ba. Kallonshi sukayi cike da mamaki.
Alhaji yace akwai fararen kwalaye guda bakwai da akazo dasu wanda nasan da zuwansu sai gashi kuma ban gansu ba, kaga dole mu gano inda suke domin amana Alhaji Marusa ya bamu akan kayansa, yanzu idan yaji acikin kayan babu wasu bayan kuma anzo dasu har nan ai dole yashiga damuwa, kuma tunda naga sun b’ace na tabbatar suna da tsada da muhimmanci shiyasa akayi kokarin sace su, dan haka dole muyi bincike mu gano komai tun kafin Alhaji Marusa yasan da maganar, domin hakan zai iya tab’a aikin mu.
Zufa ce ta fara keto masu jin abinda Alhaji ya fad’a. Adebayo ne yayi kok’arin fad’in gaskiya Sir, babu wasu kaya da suka b’ace, domin Alhaji ya fad’a mani duk abinda yake ciki, kuma na d’auki hoto na tura mashi yace komai haka yake, kila dai ba’a fad’a maka da kyau bane.
Murmushi Alhaji yayi yana fad’in sai da na tabbatar kafin na fad’i haka, dan haka ka fad’ama Alhaji Marusa yayi hak’uri kayansa zasu iso zuwa wani lokaci akwai abinda ba’a gama ba.
Umar yace Alhaji ni ina ganin tunda shi Alhajin yace haka kayansa suke kawai mu bashi, idan ba haka ba zamu jawo ma kan mu wajen son bincike. Alhaji yace tunda nine nace zanyi binciken kawai kuje. Fita sukayi jiki a sanyaye.
Bayan sun koma ofis Adebayo yace ya akayi Sir, yasan da kwalayen da muka cire? Umar yace nima nayi mamaki, kodai wani munafukin ya fad’a masa ko cikin wad’an da mukayi aikin tare akwai wanda ya turo? Adebayo yace bana tunanin haka, dole akwai abinda yayi, domin duk cikin mutanan da mukayi aiki dasu kowa yana da amana, kuma kafin mu fara sai da na tabbatar babu kowa, dole akwai abinda yayi dai.
Umar yace to yanzu ya za’ayi, kada fa ya tona ma Alhaji Marusa asiri ba k’aramun kunya zaiji ba domin kasan kayan da suke cikin kwalin, gashi babban mutum. Adebayo yace Omar bari nashiga tunani dole na gano abinda Sir, yayi, idan yana tunanin zai iya kama mu zamu gani, domin na buga da wanda yafishi.
Dariya Umar yayi yana fad’in dad’ina da kai akwai basira, duk yanda aka k’ulle abu kana iya warwareshi, shikenan bara na barka kayi nazari. Bayan ya fita Adebayo ya kira Alhaji Marusa ya fad’a masa halin da ake ciki.
Sosai hankalinsa ya tashi, nan yace ma Adebayo duk yanda zasuyi kada su bari asirinsa ya tonu, akwai kyauta mai tsoka matuk’ar suka kashe maganar. Adebayo yace angama Alhaji, kasanni akan kud’i bani da wasa, zan iya yin komai.