TUBALI 1-END

TUBALI Page 1 to 10

TUBALI*

                               PAGE 1

                      NA

              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Bismillahi rahmanirahim. Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani rai da lfy da damar fara rubuta wannan littafin nawa mai suna. TUBALI* *Ya Allah ka bani aron rai da lfy da konciyar hankali ka bani ikon rubutashi har ƙarshe bisa, lfy al’farmar Annabi da al’ƙur’ani. Allah kayi min tsari da abin hani, ka tsare min hannuna, tunanina, idanuna, al’ƙalamina, yatsuna, da rubuta wani abu da zai zamewa al’ummar Annabi sharri ko ya zama cutarwa ga tarbiyarmu.*

GEMBU MEMBILA Taraba State.

Wani irin hadari mai masifar ƙarfi da duhu ne, ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila ƙawanya tako wani sashi, gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami.

Yayinda Ya haɗe da duhun dare mai gauraye da duhun damina.

Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu ƙaƙƙautawa, kana kuma wata iriyar iska mai ɗan karen ƙarfi da sanyi ne ke ci gaba da  kaɗawa da ƙarfi.

A dai-dai ya irin wannan lokacin  kuma gaba ɗaya bani Adam mazauna cikin gidaje, sunyi nisan bacci kasan cewar ƙarfe ɗaya na dare ta gota.

Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske, wanda take nuni da mamalakinta wani  ne ko wane,  ta faso kai.

Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama. 

Ma’ana gudu irin na ceton rai, shiyasa shi kansa bai san irin tuƙin da yakeyi ba.

Gaba ɗaya jikinsa kyarma yakeyi, duk da azabebben sanyin yanayin wurin, da kuma sanyin A/C’n dake cikin motar, amma hakan bai hanashi haɗa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da rayuwar duniya ba.

Tuƙi yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya, haikan-ƙadaran. 

Da nufin bi ta kanshi ya takeshi, ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi.

Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa, kana yasa hannunshi ɗaya ya ruggume yaron dake bisa cinyarsa, yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi.

Dai-dai lokacin kuma suka iso, kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaɓan kogin Gembu wanda yake haɗe da kogin. Numan Adamawa. Dadin Kowa Gombe. kana da binuye.

Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya ziz-za.

Wayarshi ya zaro a cikin kiɗima ya fara magana da wanda ya kira ɗin, yana maganar muryarshi na rawa, magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana.

Sun zo gab da Rugar Rumo dake ƙasan hanyar can gefen kwazazzaɓan.

Dai-dai lokacin kuma, tirelar nan ta cim mishi.

Cikin tsananin mugunta ya danna motar da ƙarfi, ya ingizata, cikin ramin dake haɗe da manyan Koguna wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato.

Ji kakeyi k’uuuuuuhhhh, motar ta bada wani irin gigitaccen sauti.

Sai kuma ta ɗan tsaya daga gangarawar sabida karon da tayi da wata bishiya hakan yasa bata faɗa ciki kai tsaye ba.

Da ƙarfi ya kuma matsowa ganin  bishiyar ta ƙare ƙaramar motar.

Ingizata yayi ta tafi cikin ramin.

Ji kakeyi fuuuuuuhhh zinɗim! Ta faɗa cikin ruwa.

Wanda sautin faɗawan yasa mafi akasarin mutanen Rugar Rumo farkawa.

Suna al’hini da tausayin sanin duk wanda ya faɗa ciki ya faɗa ƙabarinsa kenan…

Shi kuwa mai tirelar wani irin masifeffen dariya mara daɗin amo, yayi kana ya wuce cikin garin dan babu damar yin kwana a wannan wurin.

 Tuƙin yakeyi wayarshi saƙale a kunne shi yana cewa.

“Sir na gama dashi, babushi a duniya.

Yayi ban kwana da duniya yanzu zan wuce cikin Gembu kuma zamuje mu kashe matarsa da yaranshi kab”.

Ɗan jim yayi jin yadda Sir ɗin ke dariyar cin nasara tare da cewa.

“kuna kashesu.

Sauran cikon 2 million din ku zai shigo hannunku.”

Cikin zaƙuwa matuk’in tirelan yace.

“Yanzu kuwa”.

Kana ya katse kiran, ya nufi cikin Gembu a cikin daren da wannan duhun damunar.

            ***************

Bayan wasu shekaru A kamar Ashirin da biyu 22.

             Kano state.

Shiru hall ɗin taron ma’aikatan tashar Arewa 24 TV dake birnin Kanon Dabo yake, yayinda ma’aikatan ke zaune bisa kyawawan kujerun dake zagaye da babban table mai kujeru sama da hamsin.

Yayinda gaban kowa goran ruwan Faro mai sanyi ne da kuma Nutrimilk sai maltina da chii exotic, baya ga haka kuma glass cheers cups ne a gefe-gefe.

Kana sai abun sautin magana dake gaban kowa, mai ɗan tsawo.

Gefen dama duk manyan ma’aikata ne.

Kana gefen hagu mabiyansa.

Can baya kuma ƙananun ma’aikata.

Babban ogansu ne ke musu bayanin canje-canje tsarin aikin da suke shirin kafawa na forkon shekarar.

Gyara zamanshi yayi tare da kallon gefen damanshi.

Murya ya ɗan gyara tare da cewa.

“Ina mai Shirin baƙon mako?.”

Cikin nutsuwa Jannart Idris Saleh Dakata. Ta ɗago kanta cikin tattausan muryarta mai cike da nitsuwa tace.

“I’m here Sir”.

Sautin daddad’an muryarta ne kuma yasa, mafi akasarin mutanen dake wajen suka juyo suna kallonta.

Tabbas Nitsuwarta na daya daga cikin dalilan da suka sa aka bata ragamar wannan shirin.

Kasan cewar manyan mutane masu kamala da shahara ake gayyatowa, so ana buƙatar mai nitsuwar da zata martaba musu manyan baƙin su.

Cikin kula. Uban gidan nasu yaci gaba da cewa.

“Shirin baƙon mako, yana da manufa mai girma, ta samo manyan mutane ta tattauna dasu, su sanarwa duniya nasarorin su da kuma irin ƙalubalen da suka fuskanta domin.

Su kasan cewa matasanmu masu tasowa, Maduban gina TUBALIn rayuwarsu ta yadda zata inganta su, tsare kansu da lalatacciyar tarbiya suyi karatun da sana’a domin watan-wata rana su zama abun koyi abun so wa yan baya.”

Shiru ya ɗanyi tare da kurɓar ruwan Lemun exotic din dake gabansa.

Ita kuwa Jannart na’urar maganar dake gabanta take ɗan sa fararen yatsunta wanda sukaji red henna tana sama tana ƙasa dasu a hankali.

Yayinda duk saura kuma sukayi shiru.

A nitse yaci gaba da cewa.

“But now I’m sorry to say Jannart, shirin ya raunata sosai. Yananin tsaron da kike ciki yasa bakya sakewa ki samu ki gayyato mana manyan mutane, shahararrun masu nagartan da zasu burge mutane.

 Shiyasa shirin yayi rauni mafi akasarin ranaku sai dai aita maimaita program ɗin daya gabata.

Wannan dalilin yasa muka samu umarni daga sama.

Aka bamu zaɓi biyu.”

Da sauri Jannart ta lumshe idanunta kana tayi ƙasa da kanta, saboda fahimtar inda kalamanshi suka dosa.

In ta gane ana gab da  sallamarta daga aikin. Wanda nanne kaɗai duniyar farin cikin ta, in ta shiga cikine kadai take samun ta sake, tayi raha tajita mai eanci babu Escort, ba Yah Junaidu a kusa.

A hankali tasa yatsarta ta ɗan ƙara saƙala na’urar dake saƙale a kunnenta wanda shike ƙarawa jinta ƙarfi, yadda take ɗan taune lips ɗin ta na ƙasane ya bawa kyakkyawan Dimple ɗin ta damar lotsawa, yayinda jajayen lips din nata suke sheƙi dan lasarsu da ta ɗanyi.

A hankali A’isha Lawal dake gefenta tasa hannunta ta kama nata tana ɗan murzawa alamun bada ƙarfin guiwa.

Salman kuwa dake fuskantar ta, idonshi ya rumtse.

Da sauri ta buɗe idonta jin shugaban nasu yaci gaba da cewa.

“Umarni na forko wannan karon an bamu sunan mutumin da ake son mu gayyato, yazo ayi hira dashi.

Domin shi kadai ne zai ɗaga darajar shiri.

Sai kuma  cewa in har bazaki iya samun dama da lokacin sakewa ki nemishi ba, to dole a sauƙeki kan shirin. 

A nemo wata ko wani da zasu iya.”

Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi kana a hankali cikin tsoron rasa aikinta tace.

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Back to top button