BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 51 to 60

        *CHAPTER Eleven*________???? A parking lot yayi parking ɗin motan sa sannan yafito saƙale da briafcase ɗin sa a kafaɗa yanufi cikin gidan

Yana shiga parlour’n da sallama a bakin sa

Saleema tafito cikin ɗakin ta riƙe da waya, amsa masa tayi tana kallon sa cike da fara’a a face ɗinta sannan tanufe sa, jakan hannun sa ta’amsa tana mishi sannu da zuwa

Amsa mata yayi yana ɗan guntun murmushi

Har ta juya yariƙo hannun ta suka jera tare cikin ɗakin

A gaban gadon suka tsaya ta’ajiye masa jakan tana shirin janye hannun ta yasake riƙe wa yana kallon ta, don haka bata yi yunƙurin sake janye wa ba tatsaya tana kallon sa cike da so

Murmushi yasakar mata yana zama kan gadon kafin yajanyo ta ya’aza ta kan jinyan sa yana faɗin “yau Halwa taje school kenan tabar min matata ita kaɗai da kewa ko?”

Murmushi Saleema tayi tana ɗan gyaɗa masa kai cike da kunyan sa

Numfashi yaja yana lumshe idanun sa kafin yabuɗe akan ta, yanda yake mata wani irin kallon ƙurilla hakan yasa tayi saurin cewa

“Uhmm abincin ka.. in kawo maka nan?”.

Shiru yayi kamar bazai ce komi ba har alokacin idanun sa na yawo ajikin ta, ahankali yaɗan matso da kansa kusa da fuskarta yaraɗa mata

“Saiiiii nayiii wanka zan ciiiiii…”

Yanda yayi maganar cikin jan kalmomin hakan yasa tsigan jikin ta miƙe wa, tayi saurin ɗaga kanta hakan yasa kansu yahaɗe waje ɗaya

Dasauri yaɗan ja baya da nasa yana yarfe hannu cikin shagwaɓe fuska tare da runtse idanu yace “zaki fasa min kai ne?”

Yanda yayi maganar yasa ta yin dariya itama tana sosa goshin ta tace “ya haƙuri ban kula ba”.

Taɓe baki yayi kafin yace “sai na rama”.

Kafin ma tayi magana ya ɗaura hannun sa akanta yazame ɗankwalin dake kan ta, sannan yamayar da hannayen nasa bayan ta yasoma jan zip ɗin rigan yana faɗin “bari muyi wanka tare ko?”

Murmushi Saleema tayi tana Sad da kanta ƙasa

Sai da yagama zage mata zip ɗin kafin yasake faɗin “zamu je gidan Bro.. Aamir yana fama da zazzaɓi, zuwa yaushe Halwa zata dawo?”

“Zuwa 04:00pm. Tafaɗa min zasu gama lectures”. Tayi maganar ahankali

Shiru yayi kawai yaci gaba da zame mata hannun rigan, sai da yagama yaja sa ƙasa zuwa cikin ta, sannan yaɗaga ta shima yamiƙe, cakk yaɗauke ta suka nufi cikin Toilet ɗin batare da ya cire kayan ba.

       *30minutes*

Khalil zaune kan dainning yana cin abinci, yana shirye cikin farar shadda ɗinkin jamfa wanda yayi matuƙar masa kyau sosai, hulan ƙube yasaka wanda aka saƙa shi da farin zare sai aka sirka da blue colour, don haka yasaka cover shoes ɗin sa da Wrest watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyan hannun sa kalan blue ɗin

Fitowar Saleema cikin ɗaki yasaka sa ɗaga kai yana kallon ta, ƙare mata kallo kawai yake yi yana taunan abincin dake bakin sa

Itama tana sanye da baƙin Material ne da ratsin fari, ɗinkin riga da skert ne wanda yazauna mata daidai, sai tayi ɗaurin ture kaga tsiya, sannan tayafa farin gyale har zuwa kanta wanda yarufe mata tulin gashin ta da yafito ta ƙasan ɗan kwalin, takalmin ƙafan ta Black Colour me ɗan tudu sannan sai jakan ta shima baƙi me matuƙar kyau da tsada, kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsan raman da yake a fuskarta wanda yasa fuskarta yayi fayau sai dogon hancin ta da yaƙara fitowa sosai

Har taƙariso wajen yana bin ta da kallo, sai da tazauna sannan yace mata “kin yi kyau Matata”.

Murmusawa tayi tana kallon sa itama, don ba ƙaramin tafiya da imanin ta yayi ba

“Kayi kyau kaima”.

Murmushi kawai yayi yana ci gaba da cin abincin sa

Itama kuma wayan ta taɗauka tana ƙoƙarin sake kiran Halwa sai ga kiran ta ya shigo, peacking tayi tana karawa a kunne cikin fara’a tace “My dear Ina kika shiga na kira baki ɗauka ba?”

Daga can Halwa tayi magana cikin sanyin muryanta da koda yaushe a haka yake tace “wlh Sister muna lecture ne sai yanzu nafito afwan”.

“Babu komi ai, dama Yayana ne yace in faɗa miki zamu biyo mu ɗauke ki idan mun dawo gaishe da Aamir”.

Halwa tace “be da lafiya ne?”

“Eh yana fama da zazzaɓi”.

“Eyya Allah Sarki Allah yaba sa lafiya”.

“Amin”. Saleema ta’amsa mata

Ɗan guntun dariya Halwa tayi tace “Sister kar ki manta fa ki riƙa yin practical kinsan yanzu kina da shigan ciki fa”.

Saleema kallon Khalil tayi

Shima ɗin idanun sa na kanta tun sanda tasoma wayan, sai dai baya jin abinda Halwan ke ce wa

Kau da kanta tayi tana murmushi tace “sis ai na gane, nariga na ɗau komi tun sanda kike da cikin Husna, so abu me sauƙi ne a wajena nima in yi na masu cikin”.

Sai kuma tasaki dariya tana faɗin “ok sai munzo ɗin ki kula min da Baby”.

Ciro wayan tayi a kunnen ta tana sakawa cikin jaka

Shi dai Khalil kallon ta kawai yake yi batare da yace uffan ba, sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannun sa yana miƙe wa yace

“Tashi muje”.

Miƙe wa tayi tabi bayan sa suka fita, sai da yarufe ƙofan kafin suka nufi wajen motan yabuɗe mata gaban tashiga, sannan shima yazagaya yashiga yaja yanufi Gate yana horn

Me gadi na buɗe masa yacilla motan waje

Ko acikin motan hira suke ɗan taɓa wa, Saleema sai tambayan sa abubuwa take yi idan tagani ahanya, shi kuma yana bata amsa

Suna isa yayi horn a bakin Gate ɗin, sai da me gadi yaleƙo yaduba wanene sannan yakoma yabuɗe masa, shigar da motan yayi yay parcking kafin suka fito, atare suka jera har cikin gidan

Wannan zuwan shine zuwan Saleema na uku kenan

Suna shiga da sallama Hakima dake zaune Aamir na kan cinyan ta ta’amsa musu, sai kuma tafaɗaɗa fara’an ta tana faɗin

“Iyeee maraba da manyan baƙi, sannun ku da zuwa”.

Saleema zama tayi kan kujera tana murmushi

Khalil kuma sai yanufi Hakiman yasaka hannu ya’amshi Aamir yana faɗin “a’a my Daddy Kai da zan zo in ganka akan gado ya naganka anan?”

Yaron na washe haƙora cike da murna cikin tsamin maganar sa yace “Ankul ai na waice”.

“Haba dai?”.

Sai yagyaɗa masa kai yana tsalle a jikin sa kafin yace “wayyayi”.

Dariya gaba ɗayan su suka yi

Zama Khalil yayi yaɗaura sa a jikin sa

A lokacin ne Saleema suka gaisa da Hakima tana tambayan ta jikin Aamir ɗin

“Ai gashi nan yaji sauƙi sai rigima”.

Khalil yace “wai haka Daddy kana rigima?”

Cinno baki yayi gaba yana maƙe kafaɗa yace “kayya ne Ankul”.

Yanzu kam dariya sosai yaba su, har Khalil sai da yadara duk da be cika son yin dariya ba

Hakima tace “iyeee Ni nake maka kayyan?”

Sai yawaigo yana kallon ta yana ƙyafta idanu, kafin kuma yagirgiza mata kai alamun “a’a”.

Murmushi Saleema tayi tace “My son Ni baka ganni bane?”

Sai yamayar da idanun sa kan ta, dasauri kuma yazamo a jikin Khalil ɗin yanufo gaban ta yana faɗin “Auncy..”

“Na’am ɗan Aunty”. Tafaɗa tana ɗaukan sa cike da fara’a

Hakima miƙe wa tayi tana cewa “kunga na barku haka ban kawo muku komi ba kuma”.

Khalil yace “ina Bro ne ban ji motsin sa ba?”

“Wlh ya koma Hospital yana da Patient”. Hakima taba sa amsa tana ciro drinks cikin Fridge

Sai kuma tajuya tana nufan wani ɗan ƙaramin table da aka jera plates da Spoons tare da Cups akai anyi danki dashi

“Caa nake kunyi waya ai?” Tatambaye sa tana zaro plate ɗaya

“No ban Kira sa ba”.

Zubo drinks ɗin tayi saman plate ɗin takawo musu, sannan takoma tazauna

“Saleema tace “Aunty Ina Abida yau ban ji ta ba?”

“Ai kam tana school bata dawo ba”.

“My Daddy zo muje mu yawata”. Khalil yafaɗa yana miƙe wa tsaye

Hakima kallon sa tayi tace “ya haka kuma zaka tafi baka ci komi ba?”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button