YANCIN KI Page 31 to 40

Ahankali me gidansa ya d’ago yana dubansa fuskarsa d’auke da murmushi, sannan yace ” ya kaja ka tsaya kana mamaki,ka k’araso mana ka zauna ….
“Ana so dole ko kuwa dazata zo gurin me gidansa?
“Shifa baya son kayan nacin nan, haka mead ta dinga yi masa naci har daga karshe tasamu nasarar mallakarsa yanzu kuma ga sajida.
Itama tun daya shigo parlour’n idanunta ke kansa tana kare masa kallo tsab ko kifta idanunta batayi,domin sosai kayan dake sanye jikinsa suka masa maseefar kyau ,bayan bayyanar da sumar kirjinsa da sukayi a filli saboda bai rufe maballin rigar har sama ba ,azuciyarta tace “baby kayi masefar kyau tana kada masa kwayar idanunta, wani irin sabon shaukin soyayyarsa ce ke sake taso mata tare da huda kowa wani sashi na gangar jikinta, adduarta daya Allah yasa zuwanta yayi mata amfani yazamo silar yin aurensu..
tsawon minti goma da zamansa, batare da me gidansa ya sake cewa dashi komai ba illa coffee dayaketa kur’ba kad’an kad’an yana karewa yanayinsu kallo had’e da nazarinsu ,sannan ya ajiye cup din akan D’an karamin table din dake ajiye agefensa kana ya numfasa, tare da kiran sunansa “fu’ad kasan kowacece wannan yarinyar dake zaune?
Take Gaban fu’ad yabada wani irin rasssss yashiga duka uku uku sannan yace “sir na santa kawar matatace….
“Ok meye tsakaninka daita saboda tazo min da wata magana..?
“Babu komai atsakanina daita face gaisuwa..
Jin haka yasa gabanta faduwa itama take kuma zuciyarta tashiga rawa “babu komai tsakanina daita face gaisuwa ta sake maimaita abinda ya fada tana kuresa da idanunta, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu.
Naunayen ajiyar zuciya me gidansa yaja ya sauke sannan yace sajida ko ?
Da sauri Ta d’aga masa kai . “Dan bamu guri ki shiga dakin can kijiramu.
ta mike tsam zuciyarta na wani irin dokawa, jikinta na rawa tana jin kar ta kurma ihu ta shiga dakin daya nuna mata wanda ke facing dinta.
“Fu’ad wannan yarinyar tazo min da zance tana sonka da aure, a yadda tabani labari tace sama da shekara goma ta d’auka tana dawainiya da soyayyarka tun kafin ka aure me’ad, giftawar me’ad tsakani, yasa ta dane nata soyayyar, Amman a dan tsakankanin wannan lokacin take jin bazata iya hakura dakai ba ,kodan matsalar dake faruwa agidanka ,tayi alkwarin zama da kai da amana tare da kulawa da nasreen,inda har tace zata ajiye aikinta ta zauna zaman aure da kulawar gidanka,Dan haka me zaka iya cewa yanzu akan wannan lamarin?
Wani irin naunayen ajiyar zuciya da numfashi ya sauke atare, yana duban me gidansa sannan ya bud’e bakinsa da kyar tmkr me koyon mgn “sir duk naji bayaninka, sai dai Dan Allah kabata hakuri saboda banida niyyar k’ara aure ahalin yanzu, ta gidana ma ban gama daita ba balle nayi tunanin kara aure, auren ma da aminiyar matata wace Allah kad’ai ne yasan tsakaninsu ,bana jin iya aurenta ,domin kuwa aurenta shine babban abun kunyar da zan aikata arayuwa yakarasa fadar hk yana me sukuyar da kanshi kasa….
“Babu zance kunya, abinda yakamata kayi kenan… domin musguna matarka bisa ga mummunar halaiyarta, auren sajida kad’ai zai sa tashiga hankalinta ..duk wace zaka aura bazai ta’ba mata ciwo ba kmr auren sajida, bugu da kari yarinyar na sonka da alamun zata maka biyayya tunda har aikinta tace zata ajiye ta kular maka da yarinka abinda matarka ta gida ta gazayi maka kenan .
“ni dai amatsayina ina baka umarnin da shawarar ka aureta kawai kasamu ingancin rayuwa nmj ne kai kana damar kara aure fiyye da daya ,karka sanyawa zuciyarka damuwa feel free kayi abinda yadace…
Fu’ad ya d’ago da sauri yana dubansa gabansa nacigaba da faduwa “kayya meyasa zai yi masa haka ?
“Shi fa bazai iya ba ,shi ko aure zaiyi bazai iya auren irin sajida ba ga tarin mata nan yara masu jini ajika ya tsallakesu ya auri uwar mata ina da sake bazai iya ba yayi mgnr a kasan zuciyarsa …….
“Kamin wannan alfarma nasan zaka iya min fiyye da fu’ad yarinyar tabani tausayi bugu da kari tana sonka gashi ta duba girmana tasan ahalin yanzu babu. Wanda zai iya saka ko hanaka nima din ba dole zan maka ,amman dai banason kullun ina ganinka cikin damuwa ,mata babu abinda suka tsana sama da kishiya kayi amfani da wannan damar ..
Shiru fu’ad yayi yakasa magana gashi dai maganar yake son yi Amman ko bud’e bakinsa bazai iya ba ,gumi ne kawai yashiga tsatsafo masa ta koina ajikinsa “ta faru takare yanzu yaya zaiyi da rayuwarsa….?
“Kace wani abu mana fu’ad kabarni ni kadai sai zuba zance nakeyi ,idan kana ganin bazaka iya min wannan alfarma ba shikenan “karka damu Allah yasa hakan ..”no sir ba..babu komai zan duba lamarin .”ba wai zaka duba lamarin ba, ka fuskanci lamarinta ,sannan ku fahimci juna . “Okay sir I will know what to do ..
“nagode sosai daga yanzu kaje kasoma shirinka ni kuma zan yi kokari nasamu mahaifinta da zance da zarar ya dawo kasar Dan ta sheidamin yaje dubai, “karka sanya wata damuwa aranka balle tunanin halin da matar zata shiga ai duk abinda aka mata ita jawo tunda ta kasa tsaya akan yancinta dan haka kaje waje zan turo maka ita ku fahimci juna.
Jikinsa Sam babu laka ya mike tamkr wanda kwai ya fashewa acikin zuciyarsa na dokawa ya fita daga parlour’n ya bude motarsa yashiga ya zauna yana zurfafa tunaninsa “anya kuwa zai iya auren sajida?
“Aminyar matarsa ce fa ,wannan lamari bazai zama da cin amana ba kuwa ?
” wayyo me’ad wallahi banso kara miki kishiya ba, banso had’aki da kowa ba ,dake kad’ai na shirya rayuwata ,”me yasa kikayi abinda duniya take ganin kara aure kad’ai ne matsalahar damuwarmu..?
Lokacin daya bar parlour’n me gidansa yakira sajida, ta fito da Dan saurinta ta rusuna agabansa kanta sukuye akasa tana wasa da yatsun hannunta “kije waje yana jiranki mungama magana akan komai ,kiyi kokari ki shawo hankalinsa.
“Nagode sosai yallabai Allah saka da alkairi ,Allah kara girma, ya gyara naka kmr yadda ka gyara lamarina “karki damu kije kawai .
Yana zaune cikin motarsa yana kallon saman motar sannan idanunsa aruntse ,yayinda hannusa ke rungume a saman fad’adden kirjinsa ta bud’e motar tashigo ta zauna, tana kallonsa kmr zata cinye shiru ne yacigaba da biyowa kafin daga bisani ta kai hannuta ta shafo gefen fuskarsa dake zagaye da gashi sai sheki suke zubawa tsabar gyaran da suke samu “abban nasreen am really sorry for disturb you na kasa jurewa ne, soyayyarka ce ke neman haukatani ,komai zanyi kaine araina, narasa sukuni ni kaina ina duba lamarin amman ba laifina bane son ne……
ya bud’e idanunsa da kyar ya watsa mata su wanda take numfashinta ya nemi d’aukewa girgiza kansa yayi kawai yana kare mata kallo “a she zaki iya son abinda mead take matsanancin so ?
“A she haka amana da yarda tayi karanci da har kike
kokarin aikata hk ga me’ad,?
“Me mead tayi miki da kika zabi ki so abinda take ?
“zanso ace wata ce ke furta min wad’an nan zantuttuka bake ba ……why why sajida wannan cin amana ne zalla?
“It’s not my fault nima tsintar zuciyata nayi da hakan ina sonka ba kuma zan iya