MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Zama yayi a falonshi ya cire p cap din dake kansa ya ajiye sannan yafara kunce igiyoyin dake jikin takalmin combos din dake kafarshi daidai lokacin Hanan ta turo kofa ta shigo tana mai yimasa sallama,
Daga kansa yayi ya kalleta sannan ya amsa mata sallamar yana zare takalman daga kafarshi,
“Masha Allah….” Ta fada acikin ranta saboda yanda yayi kyau ya sake ja cikin kayan jikinsa,zama tayi dan can nesa dashi cikin sanyin murya mai cikeda tsantsar ladabi gamida biyayya tace,
“Sannu da zuwa uncle….”
“Yawwa” ya fada atakaice domin zuciyarshi ce ke wani irin hautsinawa tana yimasa kuna,yarasa meyasa aduk lokacin da yaso yin maganar da ta shafi aure yake samun kansa cikin wannan mummunan halin,
Bata yi kasa agwiwa ba ta sake kwantar da murya tace,
“Ga abinci can saman table,ko akawo nan…?”
Girgiza mata kai yayi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanuwansa,shi kadai yasan abinda yake ji kuma yasan abinda yake damunsa shiyasa kadaici kadai yake bukata daidai wannan lokaci,
Ganin yaki kulata yayi shiru baya ko motsi yasata fahimtar cewa yau fa yan miskilancinne akusa wannan dalilinne yasa ta tashi tafita ta nufi sashenta tana zuwa tayi shirin bacci tayi kwanciyarta,sai sake sake take yi a cikin zuciyarta tana ta tambayar kanta to yaushe Khalil suka fita da maamy? Ina sukaje? Tambayoyin da ta rinka jujjuyawa kenan cikin ranta amma bata da amsarsu shiyasa zuciyarta ta cika da kunci da bacin rai,da damuwa aranta ta samu nasarar yin baccin ranar.
Washe gari kamar jiya yauma tunda ta tashi da asubah bata sake komawa bacci ba kitchen ta shiga bayan ta kammala taje ta shirya Aryan shirin makaranta,suna falon kasa tana bashi breakfast yana ci lokacin ba afi 7:30 ba anty maamy tafito zata hau sama, Hanan tasan bazai wuce wurin Khalil ba shiyasa ta gaggauta karasa bashi breakfast din taja hannunsa zuwa sama tana cewa,
“Zo muje kayiwa Papa sallama sai kazo akaika school”
Khalil na zaune afalo sanye da farar t shirt da bakin trouser wanda yawuce gwiwarsa da kadan da laptop gefenshi yana duba wani sako ta email dinsa maamy ta bude kofa ta shiga,
“Ranka yadade har antashi?”
“Ba dole na ba maamy…. Mai girma deputy president da kansa yaturo min sako ai dole intashi”
“Haka kam…. To yakake?” Ta fada tana kokarin zama gefen kujerar dake kusa dashi,
“Alhamdulillah,kefa?”
“Lafiya lau wallahi Khalil”
“Any problem?” Ya bukata idanuwanshi na kan system dinshi,
“Ehh to…. Dan Allah idan zaka fita zaku yi dropping dina wurin saloon ina so zanyi kitso….”
Daidai lokacin su Hanan suka shigo kuma kunnuwan Hanan sun samu nasarar jin kalaman maamy,sam Hanan bata nuna tajiba suka gama abinda zasuyi taja hannun Aryan suka fita,
Bata sake komawa part din Khalil ba sai bayan da tayi wankanta ta shirya ta saka wata pink and blue colour din atamfa riga da skirt sannan ta nufi wurin Khalil tana rike da kayan breakfast dinshi,baya cikin falon lokacin da ta shiga sai dai ga system dinshi nan da wayoyinshi zube saman kujera,fita tayi tai maza taje ta ci nata breakfast din cikin sauri sannan ta dawo tana shigowa yana fitowa sanye cikin farin yadi tissue,bai san ko yaushe Hanan ta koyi wannan abun arzikin ba ko da yake ai kullum mutum girma yake yi hankali na kara shigarshi,
Kan dining din ya karasa ya zauna tana biye dashi abaya,dumamen tuwon daren jiya tayi masa da kunun gyada sai yan soye soyenta da tayi,ga mamakinta sai taga ya wanke hannu ya zuba dumamen tuwon yana ci,wai dan Allah Khalil wanne irin mutum ne shi mai saukin kai haka? A wannan level din nasa da wanine ai ko kallon tuwo bazai yiba bare har yaci,
Shiru ne ya mamaye wurin sai shi dake ta faman cin dumamen sa,dan ajiyar numfashi tayi sannan tace,
“Uncle zan bika…. Ina so zanje gyaran gashi da k’unshi dan Allah sai ku saukeni……”
Shiru yayi bai amsa mata ba dan yi yayi ma kamar bai jita ba,ita maamy tace zata bishi itama wannan yanzu tazo tace wai zata bishi to wa zai dauka acikinsu? Tunda shi dai bazai taba hadasu gaba daya su fita tare ba,kuma idan yatafi da Hanan yabar maamy bai kyauta ba haka idan yatafi da maamy yabar Hanan to yayi ganganci ko kuma yaso kansa dayawa saboda ko babu komai Hanan matarsa ce kuma dole akirata da wannan sunan,
“Kaji uncle……” Muryarta ta katse masa tunaninsa,
“Ba yau ba…” Shine amsar da yabata yana wanke hannunshi cikin sink,bata kai ga kara magana ba anty maamy ta shigo taci wata bubu na wani dan ubansun leshi baki mai adon pink sai kyalli yake ta dan yafa mayafi akanta da alama dai tafi son shiga irin wannan,
“Khalil ka gama ne muje?”
Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace,
“Maamy kiyi hakuri bazai yuyu mu fita tare ba saboda inada urgent meeting yanzun nan,but zan turo miki driver idan hakan yayi miki…..”
“No kabarshi kawai babu matsala bari sai infita da kaina kawai”
“Ok”
Juyawa tayi tafita ita kuma Hanan tafita fuuuu itama alamun wai tayi fushi,bai bi ta kanta ba yawuce yafita shima.
***
Tun bayan dawowar sumayya daga katsina abubuwa suka fara canjawa tsakaninta da mujahid,sai yayita janta yana tsokanarta koda kuwa bata kulashi ba,haka makaranta shine yake kaita ya koma ya daukota,gashi babu dama yaganta da saurayi sai ya koreshi duk wanda yazo wurinta sai ya koreshi,sosai abin yake bata mamaki duk da ta dan fahimci inda yasa gaba amma bata yi saurin bada kai ba,
Yau daga makaranta dan ajinsu ya rage mata hanya domin sun gama lectures daya lecture din ance malamin bazai zo ba,suna zuwa kofar gida tana shirin fitowa mujahid na fitowa daga ciki, parking yayi yaje wurinsu yace tafito, tambayar ta yafara yi wai wanene wannan? Meye hadinta dashi da har zai kawota gida a mota?
“Course mate dinane fa ya mujahid…. Rage min hanya yayi”
Zura kansa yayi cikin motar yace,
“Barka dai…. Dan Allah daga yau karka kara rage mata hanya,koda kuwa itace ta bukaci hakan,kana iya tafiya”
Fuskantarta yayi wacce ke tsaye baki bude saboda tsabar mamaki,
“Daga yau sai yau kar na kara ganinki acikin motar wani da sunan wai yarage miki hanya…. Kina jina?”
“Haba dan Allah ni wai meyasa kake takura minne? Menene dan anrage min hanya? Ni wallahi…..”
“Zaki wuce kishiga ciki ko sai na baki mari….”
Wucewa tayi tana kunkuni sai bubbuga kafa takeyi,har yashiga motarsa zai fita ya kashe yafito yabita cikin gidan can dinma sakata yayi agaba da dokoki wai babu ita babu kula kowanne namiji ta inda yake shiga ba tana yake fita ba da ya isheta da fada mikewa tayi tsaye cikin fada tace,
“Wai menene naka idan na kula wani namiji? Ina ruwanka dani?”
Kallonta yayi idanuwanshi cikin nata sannan ya dan sassauta muryarshi,
“Saboda ke tawace….. Ke tawace ni daya sumayya,bazan iya jure ganinki tare da wani da namiji wanda ba niba”