MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 11 to 20

Bata iya magana ba sai kallon sa da take yi”What happened to bring you here? Where is your father?”

Ya sake jero mata waɗannan tambayoyin

Wannan karon ma bata ba shi amsa ba

Dole ya kalli Me gadin yace da shi, “ya ɗauko mata kayan nata ya shigo da su,” sannan yace mata, “she follow him”.

Shiga suka yi gidan suka wuce Part ɗin Kawu Ali. Sai da yayi Nocking kafin ɗiyar sa Murjana da suke zaune da Umma a parlour’n suna kallo ta zo ta buɗe masa jin muryan Kawu Zubairun

“Lafiya me ke faruwa? Wace ce wannan kuma?” Inji Umma domin itama ta taso ta biyo Murjanan a baya a tunanin ta ko babu lafiya ne

Shi kuma yace mata, “baki gane ta bane? Zulaiha ce ƴar wurin Faruk”.

“Faruk.. Faruk dai ɗan uwan ku na Riyadh?” Ta ambata tana sake ƙare wa MEEMAN kallo

“Eh shi. Kira min Yayan nawa sai ki sanar masa do Allah”.

“To shikenan bari in shiga in Kira sa”.

“Ke kuma ki zo ki zauna kin wani tsaya a tsaye”. Inji kawu Zubairun yana kallon MEEMAN dake tsaye har yanzu a bakin ƙofa. Ganin bata motsa ba sai ya tuna ai ba ta jin Hausa sai ya kuma maimaita mata da turanci

Hakan yasa ta tako a hankali tana bin ko ina da kallo ta zo ta ɗofana mazaunan ta a kujeran

Itama Murjana zama tayi tana ƙare mata kallo kafin kuma ta kalli Kawu Zubairun tace, “wai Kawu wannan ɗin ita ce yarinyan Uncle Faruk ɗin?”

“Eh ita ce mana baki ga sun yi kama da uban nata bane?”

Taɓe baki tayi tana sake ƙare wa MEEMAN kallo don bata taɓa sanin ta ba, a kaf gidan ma babu wanda ya san ta illa labarin ta da suke ji, sai kuma su Kawu Ali da suke zuwa can ɗin shi ne suka santa.

              “Ina Zulaihan take?” Inji Kawu Ali da ya fito da sauri daga ɗaki Umma na take masa baya. Ganin ta yasa yace, “ashe dai ba ƙarya Jamila take min ba itan ce da gaske, ikon Allah”. Yafaɗa yana zama gefen Kawu Zubairu idanuwan sa a kan MEEMAN, kafin kuma ya juya yana tambayar Kawu Zubairu, “a ina ya samo ta?”

“Nima wlh Ina tsaye a bakin ƙofan sashi na na hangi Gali Yana taho wa, shi ne nake tambayar sa lafiya ina zai je? Yake sanar min wai baƙuwa ce ta zo kuma wurin ka ta zo shi ne zai zo ya sanar maka, Ni kuma nace mu je in ganta”.

Kawu Ali yace, “to ke wa ya nuna miki gidan namu? Waye ma ya kawo ki ƙasar? Ina uban naki?”

“Kaima ka san ba ta jin ka tunda ba iya Hausa tayi ba”. Cewar Kawu Zubairun

Shi shaf ya ma manta sai ya juya harshen yana sake tambayar ta

“My Abee is Dead”.

“He died?” Suka faɗa a tare cikin wani irin farin ciki da ya kasa ɓoyuwa a fuskar su

Ita kuwa bata ma fahimci yanayin nasu ba sai gyaɗa kanta da tayi cikin muryan kuka take cewa, “yes he died and left Me”. A nan take sanar musu da komi da mutuwar nasa da kuma wasiyyar da ya bata ta dawo Nigeria ta zauna

“Ka gani ko Zubairu ai Allah ba azzalumin bawan sa bane, tunda Ni na gansa a haka dama na san zai wula nan ba da jima wa ba, muka so mu taimake shi mu tafi da ita amma ya ƙi furr har shegiyar yarinyan nan tana mana rashin kunya, sai ga shi dai mu ne dolen ta ga shi ta dawo wurin mu, to uban wa yace mishi muna da wurin ajiye ta? Ai a daren nan zamu kaɗa shegiya ta tafi..”

Kawu Zubairu yayi saurin taran numfashin sa da cewa, “to gadon mu fa? Haka zata tafi da dukiyan nasa bayan shi muke wa sintiri tun ba yanzu ba?”

“Gaskiya nima abun da na gani kenan?” Inji Umma da ta saka musu baki

Kawu Ali yace, “to ai dole sai mun amsa kason mu kafin ta bar mana gida”. Sai ya juya yana kallon MEEMA da kanta ke saman cinyoyin ta tana ci gaba da kuka yace, “so since he died now where is our inheritance? Where is your father’s property then we will share?”

Ɗago kai tayi tana kallon su, sai kuma tace, “Abee owned everything for me before he died, and now he has returned all his property to my name.”

Wani ashar Kawu Ali ya fesar ya buɗe jajayen idanuwan sa zai yi mata magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi

“Ka ga Yaya bar ta don Allah, na nemo mana mafita, ai maganar ma gado bata taso ba, kaf dukiyar sa ya zama namu wlh kuma dole sai mun amshe sa, amma yanzu idan kace zaka nuna mata halin da muke ciki zata iya tafiya wajen uwar ta ta bar mu, yanzu samun hanyar da zamu yi mu mallaki komi ya zama namu shi ne mafita, in yaso daga baya sai mu kore ta ta tafi, ka san tayi karatu tana da ilmi dole sai mun nuna mata siyasa komi ya dawo hannun mu”.

Shiru Kawu Ali yayi yana tunani

Umma tace, “Abban Sajjad maganar Zubairu fa a kan gaskiya take, yanzu ai ko kace zaka amshi komi bazai yiwu ba, ta yiwu ma babu komi a hannun ta dole zata zauna damu har sai kun mallaki komi ya zama naku kafin ku kore ta”.

Sai da Kawu Alin ya kalli Murjana yace, “ke ja ta ɗakin ki ku tafi ki nuna mata komi don a can zata zauna”.

Tashi tayi tana kallon MEEMAN cikin yatsina tace mata, “she got up and they went”.

Hakan yasa ta kalli su Kawu Alin ta ƙi ta tashi

Shi kuma yace, “she get up and followed her to her room.”

Sannan ne ta tashi ta ja kayan ta tabi bayan ta suka wuce ɗakin Murjanan

“Yauwa to na yarda da shawaran ku hakan za’a yi, yanzu dai dole zamu ja ta a jiki domin mu mayar da duk ƙadarorin ta ya zama namu”.

“Eh Yaya hakan za’a yi”. Inji Kawu Zubairu

“To shikenan mu bar maganar yanzu sai zuwa gobe sai mu ci gaba da tattaunawa ko zamu ɓullo hanyar da ya kamata”.

Da haka suka rufe maganar Kawu Zubairu yayi musu sallama ya tafi. Su kuma suka wuce ɗakin su.

                 *WASHE GARI*

            Sai tara da rabi MEEMA ta farka daga barcin da ya ɗauke ta tun sallan asuba da tayi ta koma. Ta jima a zaune a saman gadon bata iya tashi ba tana ta faman tunanin da ya zame mata jiki, da kuma yadda Rayuwar ta zata koma a nan gaba a inda bata saba ba. Sai daga baya ta miƙe sabida yunwan dake ƙwaƙulan ta don babu wanda ya zo ya tashe ta, daga ita sai farar riga me tsantsi da guntun wandon sa ta shiga bayi tayi brush sannan ta fita parlour’n ko ɗan kwali, sai dai ta kama gashin nata ta tufke shi a tsakiyar kan.

          Babu kowa a parlour’n sai wani kyakykyawar saurayi bafulatani fari sol, don da gani kaf gidan ya fi su kyawu domin shi zak Fulani ne babu silƙi, tamkar dai Mahaifin MEEMA ya haife sa saboda kamanceceniyar da suke yi, don shi ya fi kama dashi a kan su Kawu Ali. Yana zaune ne a kan sofa ya saka ear phone a kunnen sa, daga shi sai gajeren wando ko riga babu, kan nan nasa ya sha askin zamani wanda ƴan iska suke yi, ya bar tulin gashi sosai a tsakiyar kan wanda ko kitso za’a iya yi tsaban tsawon sa, wata macen ma baza ta nuna masa yawan gashi ba. Waƙa yake bi na Turanci duk ya kure parlour’n da muryan sa

MEEMA dake tsaye a bakin ƙofan tunda ta fito ta hange shi sai ta tsaya cak tana bin sa da kallo, tayi five minutes a tsaye a wurin tana faman kallon sa kafin kuma a hankali ta tako ta soma dosan cikin parlour’n zata wuce zuwa kan dainning table da ta hango

Gab ta iso kusa da wajen nasa ne ya ankare da ita, da sauri ya ɗaga idanu yana kallon ta, be san sanda ya miƙe tsaye a kan ƙafafuwan sa ba yana sake ware ido a kanta

Itama idanun ta na a cikin nasa ta kasa ɗauke nata a kanshi, sai dai ko kaɗan fuskar ta babu alamun walwala haka take kallon sa. Sai da ta kusa wuce wa kafin ta janye nata idanun ta nufi saman dainning

Har sai da ta zauna before ya kawar da kansa ya nufi ɗakin Umman sa yana kwaɗa mata kira kamar zai tsaga gidan

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button