MEEMA FAROUK Page 31 to 40

“Alhamdulillah.” Ta amsa ta tana kallon ta
Zabba’u tace, “Weldon you slept. Today is a holiday.”
Murmushi tayi mata
“Go to Breakfast there and lie down.” According to Hajiya
Hakan yasa ta tashi ta wuce kan dainning ɗin
Ummee da ke aiki a computer ta ɗago tana kallon Hajiya tace, “Hajiya zamu fita da MEEMA zuwa kasuwa, kiyi mata magana sai mu je tayi shopping abun da take so, and Ina so in je gidan Hajja Salma sai mu je tare su gaisa, dama tayi min complain bata san ta ba.”
“To ke meyasa baza ki faɗa mata ba sai Ni? Ki sanar mata idan zata bi ki sai ku je.”
Ummee tace, “ok.” Sannan ta ci gaba da aikin ta.
Bayan MEEMA ta gama Breakfast ɗin ne ta dawo parlour’n ta zauna
Ummee looked at her and said, “We are going to go shopping. If there is anything you need, we will go and buy it.”
“No I don’t need anything.” Tafaɗa ba tare da ta kalli Ummeen ba
“Why do you say that? I know you need MEEMA, you will follow me to go because I want to go to my friend’s house and greeting”.
Shiru MEEMAN tayi bata ce komi ba
Hakan yasa Ummee tayi tunanin ko ta amince ne, sai ta ci gaba da aikin gaban ta
Hajiya tana ji bata tanka ba hiran su suke yi ita da Zabba’u
While MEEMA tana latsa wayan ta
Can Ummee bayan ta gama abin da take yi ta tashi tana kallon MEEMAN tace, “Go get ready and we’ll go out.”
“I will not go anywhere.” Tafaɗa a wannan lokacin tana kallon ta
Shiru Ummeen tayi kamar zata yi magana kuma sai ta juya ta haye sama
Hajiya kallon MEEMAN tayi tace, “Why are you like that?”
Da ido ta bi ta ba tare da ta fahimce ta ba
“Don’t do that to your mother. She’s your mother. You shouldn’t argue with her. Get up and follow her.”
Girgiza kanta ta soma yi har hawaye sun cika mata ido. “No, I’m not going. I’m not happy if I follow her.” Tafaɗa tana miƙe wa ta wuce ɗaki da sauri
Da kallo suka bi ta har ta ƙule
Zabba’u tace, “wai Ni Hajiya mene ne ya haɗa su ne take yiwa Hajiya ƙarama haka? Kawai fitan da zasu yi ne tare shi ne take cewa baza ta je ba hakan be dace ba.”
“To ai duk yanda kika gani da laifin Zulaiha. Sannan kinga rayuwar su da na nan ba ɗaya bane. Dole sai kin taimaka min wajen mun fahimtar da ita muhimmancin uwa, yanzu tana kallon mahaifiyar ta ce a maƙiyiyar ta kuma kin san hakan be dace ba tunda uwa uwa ce. Ni kaina ba na so ta ci gaba da nuna wa mahaifiyar ta tsana.”
“To Allah ya kyauta Hajiya, ai a sannu zata saba komi zai wuce tunda yanzu suna tare a gida ɗaya”. Cewar Zabba’un tana tashi tsaye zata wuce kichen. Sai kuma suka ji Nocking hakan yasa ta wuce bakin ƙofan ta buɗe. Zaro ido tayi tana kallon Matar da ke tsaye riƙe da hannun ƙaramin yaro da bazai gaza shekaru bakwai ba. Washe baki tayi tana kiran sunan ta. Sai kuma ta juya tana cewa, “Hajiya Jalila ce ita da Habeeb.”
Jalila murmushi tayi ta shigo tana cewa, “ina Hajiyar tawa? Yau na kawo miki Mijin ki.”
Dariya Hajiya tayi da cewa, “maraba lale yau dai muna da babban baƙi kenan?”
“Ai ba mu kaɗai bane har da Abban shi.” Inji Jalilan tana zama
Kafin ma suyi magana sai ga shi ya shigo
Hajiya bata san sanda tayi yunƙurin tashi daga kujeran da take zaune ba. Sai dai kasancewar ta kasa dole ta zauna tana bin ɗan nata da kallo
Shi kuma da sauri ya iso yana kiran sunan ta. Ai rungume ta yayi tsaban murna sai ga hawaye
Itama haka hawayen ta fara bakin ta na rawa tace, “Hashimu ashe zan sake ganin ka? Kai ne dai ka dawo?”
Ɗago kansa yayi yana murmushi da hawaye a tare yace, “Hajiya Allah yayi mun dawo. Yau dai gani ga Hajiyata.” Sai ya sake rungume ta
Zabba’u kuwa baki har kunne, ai sai ta ruga zuwa sama don sanar wa da Ummee. A tare suka dawo Ummee kamar zata kifa tsaban sauri
Shi kuma yana ganin ta sai ya tashi ya nufe ta yana faɗin, “Aunty.”
Hannayen sa ta riƙe cike da tsantsan farin ciki tace, “na kasa yarda da aka ce min kai ne ashe dai kai ɗin ne? Gaba ɗaya ka manta damu?”
“Haba Aunty Kar ki CE haka, kin san aiki. Inda muka je gaba ɗaya babu network muna daji, jiya na sauka muka taho yau.” Yafaɗa yana koma wa ya zauna
Itama zama tayi sannan aka sake gaisa wa
Zabba’u tuni ta cika musu gaba da drinks
Hayaniyan su ne ya fito da MEEMA dake ɗaki
Uncle Hashim shi ya fara hango ta, sai ya waro ido yana faɗin, “wa nake gani kamar MEEMA?” Sai kuma ya kira sunan ta
Hakan yasa ta dawo da idon ta kanshi. Sai kuma ta nufe shi itama tana kiran sunan shi
Cike da farin ciki ya tashi ya rungume ta yana cewa, “When did you come back here? Are you already here?”
Hajiya ce ta ba shi amsa tana faɗa mishi dalilin dawowar ta
Hannun ta ya riƙe suka koma suka zauna. Cike da tausayin ta yayi mata ta’aziyyar mahaifin ta
Kasa magana tayi saboda yanda idanuwan ta suka cika da hawaye
Yace, “Be patient my daughter. Pray for him because he is the only one who needs it. May God forgive us for his loss.”
Duk suka amsa da, “Amin.” Ban da MEEMAN da har yanzu ta kasa magana
Hajiya kallon Habeeb tayi da ya maƙale a jikin mahaifiyar shi tace, “kai kuma baza kazo bane mu gaisa? Ko har ka manta da Ni ne tunda dama ka rabu da zuwa gaishe Ni?”
Tashi yayi ya iso wurin ta
Ta kama shi tana shafa kanshi tace, “Miji na yau dai ga ka a gida, ga kuma Baba ya dawo ko sai murna?”
Murmushi yayi yana gyaɗa mata kai
“Ai yau tunda muka tashi da safe yake murna zai zo wajen Kaka, dayake ya tashi da zazzaɓi a jikin sa amma hakan be hana shi murna ba, zaman mota ne yasa duk yayi yaushi kafin mu zo amma da kuzarin shi muka zo don ya dame Ni har yanzu ba’a kawo ba?” Cewar Jalila tana murmushi
Dariya duk suka yi
Hajiya tace, “ayya ashe mijin nawa babu lafiya ne? Ai ko be kamata a bar shi haka ba. Zabba’u ki samo mishi magani sai a ba shi, amma kafin nan ki dama mishi ko Custard ne sai a ba shi kafin a gama girki.”
“To Hajiya.” Tafaɗa tana yinƙura wa ta tashi
Su kuma hira suka ɗan fara taɓa wa
While Uncle Hashim kallon MEEMA yayi suka sakar wa juna murmushi. Sai ya saka hannu ya riƙe nata hannun yana cewa, “My baby has grown, how did you grow up so much? I miss you so much.”
Dariyan farin ciki ta saki wanda zai tabbatar maka da cewa tabbas tana a cikin farin ciki sosai. Dayake sun saba da shi, a lokacin da tana yarinya kusan ko yaushe yana yawan ziyartan su can Riyadh musamman domin ta, tunda dai aka ƙara mishi matsayi a wurin aiki ne ya dena zuwa amma duk da haka suna waya sosai, sai kuma tafiyan nan da yayi ya jima dole ta dena jin wayan shi, duk da bata yi tunanin ko aiki ne yasa ta dena samun shi a waya ba sai dawowar ta da Hajiya ta sanar mata. Kanta ta ɗaura a saman kafaɗan shi tace, “I miss you so much, Uncle!”
“Now I know you graduated?”
Gyaɗa masa kai tayi
“Now you are getting married. However I thought I would come back and find out you are married and I will see your children walking.” Ya ƙare maganar yana kwatanta wa da hannun sa